Ta juyo da sauri ta kalli Ummi hawaye na sauko mata da bibiyu.
“Ban aikata komai ba, ban yi komai ba Abiey ka yarda da ni”
Ta sake juyawa ga mahaifinta.
“Ina motarki take?”
Mahmood ya tambaya sai ta kasa furta komai, ta sani idan ta fada laifinta kara girma zai yi, kuma bata son iyayenta su sake kallon Ameer da wani laifin, bata kiyayyarsa ta girmama a zuciyarsu. Ummi ta kalli mijinta.
“Bari na yi magana da ita private”
A take Abiey ya daka mata tsawa.
“No a nan zata amsa mana, ba sai anje wani gurin ba domin police za su su tafi da ita, su ai dole ta fada musu gaskiya idan mu ta boye mana, dole ta fada mana abun da ya kai motarta Kt tare da wasu tarduna nata da suke motar da duk wasu bayananta, tun daga kt aka turowa CP na garin nan abun da ya faru, shi ya turo min komai kuma ya tabbatar min za su zo su tafi dake saboda an ga gawa a cikin motarki”
Ummi ta zaro ido tare da dukan kirji, sai a yanzu ta yarda lamarin babba ne. Gaba daya sai idon kowa ya dawo kanta, not just her body har muryarta da idonta rawa yake duk sanyin falon sai da gumi ya kwankwasa mata kofa, tashin hankali yace baki ga komai ba sai a yanzu, gaba daya sai ta manta da tsoron fadin wanda ta bawa motar, furucin mahaifinta cewa an ga gawa ya fi komai daga mata hankali.
“Ameer na bawa motar Abiey gawar wa aka gani?”
“Wane Ameer din?”
Sai a wannan karon Maleek ya saka bakinsa with confused.
“Ameer abokinka”
Ta amsa kai tsaye, a take Abiey ya sauke mata lafiyayyen mari sai da ta fadi kasa.
“Ta ina kika alakantu da shi? Miye hadinki da shi? Ina kika san shi har zaki dauki motarki ki bawa makiyin ďana? Kin kyauta gashi yanzu an yi miki sakamako kuma zaki girbi abun da kika shuka”
Ummi ta yi saurin shiga tsakiyarsu hawaye na cika idonta, kafafuwanta suka fara juyawa kamar ba za su dauke ta.
“Ga.. Ga.. Ga...ga... ”
So take ta tambaya gawar waye a motar amman ta kasa, saboda tsoro irin amsar da za a bata gashi maganar ma ta gagara fitowa. Mamaki ya hana Mahmood da Maleek cewa komai sai kallonta suke bama kamar Maleek. Abiey ya juya ya fice daga falon cikin wani irin fushi da bacin rai da ya dauki shekaru be ziyarce shi ba. Yana fita Ummi ta duka ta kama Nimra dake kuka.
“Ummi ban yi da wata manufa ba, ya fada min mahaifinshi ya koreshi kuma be san inda zai je ba, na bashi motata da kudi da ATM, amman ban san inda yaje ba, kuma ban aikata hakan da sanin cewar shi ne wanda suka yi fada da Ya Maleek ba, Allah ne shaidata ban sani ba Ummi”
Ummi ta rumgume ta tana kuka. Ummi ta amsa mata ta hayar daga mata kai alamar ta gamsu, sai dai zuciyarta ya samu rauni na rashin jin halin da Ameer yake ciki. Nimra ta dago ta kalli Maleek da ya kasa motsawa daga inda yake tsaye.
“Gawar waye a motar Ya Maleek? Kashe kansa yayi? Ko hadari yayi? Ina Ameer din yake?”
Sanin halin da Ameer yake shi yafi tsaya mata a rai sama da abun da aka zarginta da aikata, ji take idan aka samu gawar wani wanda ba shi ba abun zai zo mata da sauki, amman idan gawarsa shi ta wanne zata ji? Mutuwarsa ko zargin da ake mata?
“Gawar wata yarinya ce”
Maleek ya amsa mata, ita aka amsawa amman Ummi ce ta fi jin sanyi a ranta a take ta lumshe ido ta sauke ajiyar zuciya, kamin ta mike tsaye da sauri ta fice zuwa bangaren Abiey, ko da ta shiga ta same shi yana aikin saka sabon tufafi.
YOU ARE READING
WANI GARI
General FictionA wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta ball...