Momy ta yi dariya tana kallon kawarta.“Hajiya Saude kina ba ni mamaki, ai a tunanin saboda bana neman maganin sai na zauna a haka? Akwai wani karin magana da hausawa ke cewa ko kana da kyau ka kara da wanka”
“Hajiya a taimaka mana da lanin muma mu samu kan mazanje na mu”
Momy ta dauke kai daga barin kallon wayarta ta kalli Hajiya Saude.
“Samun kan maza yana da wahala Hajiya Saude, idan kana son samun kan miji to dole ne ka masa biyaya ka bishi sau da kafa kuma ka so abun da yake so ka guji bacin ransa, kamar kin ga mijina be hada ďansa Ameer da kowa ba, a gabana zai nunawa yayana banbanci ya nuna min ya fi son ďansa da su, amman na kan daurewa zuciyata kuma su ma na nuna musu ba komai ba ne gudun kar su ďarsawa zuciyarsu kiyayyar dan'uwansu, nuna masa da nake ina kaunar ďansa ya kara masa so na a zuciyarsa, da ace tsana nake nunawa ďansa da yanzu mun rabu, domin Alhaji yana matukar son Ameer irin son da ke bani tsoro wani lokacin, ina masa biyayya sosai, kuma ina karawa da nawa dabarun da na sani”
Hajiya Saude ta gyara zama kallon kawarta dake kokarin zayyano mata sirrinka.
“Ki samu madubinki mai kyau ki rubuta idan kin iya ki rubuta ko kuma ki saka a rubuta miki Wa Alqaitu Alaika Mahabbatan Minni kafa 71 gurin ko wane min ki bude shi ki saka sunan mijinki, sai ki samu zuma farar saka duk inda kika rubuta sunan mijinki ki diga zumar akai, idan kuma ba ki da zuma ki dora madubin bayan rufin daki ki dora shi a kai, ki bar shi ya kwana a gurin, zaki iya samun wani kyalle ki rufe shi akai gudun kar wani abu ya taba, da safe zaki duba ki dauko ki wanke sai ki saka girishi kadan, shi saka gishiri da a ciki rubutu yana da karfi sosai, wasu malaman man suka ce har ya fi zuma, duk wani sirri da ake da madubi ko ake saka zuma farar saka ko gishiri yana da kyau sosai gaskiya”
Hajiya Saude taja dogon numfashi ta sauke yana jinjina lamarin yadda kawarta ta san sirrin da ita bata sani ba.
“Lallai Hajiya yanzu duk kin san wannan amman kika bar ni ina zaune haka nan”
“To ai baki bukata ba ne, ni Wallahi ba boka ba Malam amman mijina sai abun da na ce, amman fa ina hada masa da biyayya sosai da kuma balmar baka, kin san mata sai da salon zancen da kisisina. Bari na kara miki da wani sirrin mai karfi gaske shi wannan ma mijinki ba zai taba iya boye miki sirrinsa ba, idan kina da koshiya ki saka sunanta ita ma zata biki sau da kafa ku zamu zaman lafiya, wannan tawada mai kyau zaki samu ki sai ki dauki Kur'anenki ki bude suratul Yusufa, ita wannan ayar ana sarrafa ta kala kala ko da yarki ce ta rasa mijinki aure zaki iya sakawa ayi mata sai dai kowane sirri da yadda ake hada shi...”
Shigowar da Ameer yayi a falon cikin tsananin fushi babu riga a jikinsa ya saka ta yanke maganar da take da Hajiya Saude ta juyo tana kallon ďan mijin nata, ba abun mamaki ba ne ta ganshi rai a bace domin abu kadan ya bata masa rai ko da be taka kara ya karya ba, sai dai na yau kamar ya dara na kullum, domin ya shigo falon kamar an korashi a waje.
“Ameer lafiya?”
A maimakon ya amsa mata sai ya aika mata da tambaya cikin zafin rai.
“Balarabe ya shigo nan?”
“Be shigo ba, Allah yasa ba shi yayi maka laifi ba”
Momy na aje numfashi, Baba Balaraben ya kwankwasa kofar falon, sannan ya turo ya shigo a hankali, jiki na rawa ya karaso kusa da Ameer yana fadin.
“Ranka ya dade Wallahi ban gane abun da kake magana kai ba, ka ga abubuwan da na samu”
Ya bude bakar ledar dake hannunsa ya ciro wasu kanan gel na wanke fuska yana nuna masa, kamar kibtawa da bismillah haka Ameer ya dauke tsohon da zai kai shekara sittin da uku mari, a take ledar dake hannun Baba Labarabe ta subuce ta fadi, ya dafe kuncinsa yana kallon Ameer, Momy da Hajiya Saude suka mike tsaye.
YOU ARE READING
WANI GARI
General FictionA wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta ball...