“Ko wace dakika da mintuna idan suka wuce basa dawowa, rashin dawowar yana nufin rasa abubuwa da dama ciki har da lokaci idan baka yi amfani da shi a lokacin da ya dace ba, kyaunku ba zai tabbatar har a bada ba, ku yi aure a lokacin da maza suke ganinku suna yaba surarku har suna sha'awar aurenku, idan lokaci ya wuce za ku neme su ku rasa a lokacin ido zai rufe wata kila ku fadawa wanda be dace da aurenku ba, ba ni da buri a yanzu kamar ganin aurenku”
Ta sauke hannunta daga fuskar Nimra tana murmushi.
“Zamu yi aure Ummi, ni kin riga da kin san inda da wanda nake so kuma da zarar ya dawo daga Umra zan masa magana ya turo, sai dai ki yi ma Namra wa'azi ta rika sauraren masu zuwa gurinta, domin ita ce mai girman kai”
Namra dake ta danne danne da complete ta dago a fusace tana kallon kanwarta, wato Husainarta.
“Okay haka kike zama gurin Ummi kina min munafurci ko? Kina ruwanki da rayuwata? Maybe I'm not ready now ko kuma dukan masu zuwan basu min ba”
Ummi ta lankwasa kai tana kallon yarta.
“Na fa san halinki Namra, taya za a ce duk samarin dake nuna suna sonki babu wanda yayi miki?”
“Ummi I'm serious gaba dayansu ni ba su min ba”
“Ba ki sake jiki da su taya za'ayi ki san wadanda suka miki? Da wandanda basa miki?”
Cewar Nimra, domin ita ce mai far'a da saurin sabo ga son mutane, yadda take friendly da kowa sai ka dauka tana kaunar duk namijin da ta yi arba da shi ne.
“Nimra this is my life, can you please mind your own business? Ni fa ba irinki ba ce kowa far'a kowa dariya har wanda be kamata ace yana sonka ba ya zo yana maka maganar soyayya”
“Ummi See? Kin ga abun da nake fada miki ko? Fadin rai ba zai bar ta ta kula samari ba”
Namra ta dauki fillon kujera ta jefawa Nimra, Hajiya Zahra ta yi saurin saka hannunta ta tare.
“Gaskiyar da ba ki so, dole mu fada miki, kuma karki yarda na sake jin bakinki ya furta cewar baya son kowa?”
Miyewa ta yi sauye bayan fadar haka ta nufi wata karamar kofa dake falon ta bude ta fita tsakar gidan da ko'ina yake tsab, matsawa ta yi kusa da flowers ta mika hannunta tana taba su a hankali, babu ranar da bata tunanin ďanta, babu ranar da zata zauna ta yi hira da yaranta akan rayuwarsu bata tuna da ďanta, damuwarshi ta haifar mata da damuwa da yawa, ta haifar masa da rashin kuzarin iya rike kanta a duk lokacin da ta tuna kamar yadda hawaye suka fara wanke fuskarta, ta kasa cire kanta a damuwa ta kasa daina tunaninsa duk da kasancewar likita ya gargadeta da ta cire damuwa a ranta saboda hawan jinin da take fama da shi. A tsorace ta juyo jin muryar Mahmood yana kiranta. Kamar hoto ya tsaya yana kallonta ganin hawaye a idonta.
“Ummi lafiya?”
Ta taba fuskarta sai ta ji hawayen sa bata san lokacin da suka sauko mata ba, murmushi ta yi ta share hawayen.
“Lafiya kalau, yanzu ka dawo?”
“Eh ni ma dauko Abiey, amman Ummi ba lafiya ba kalli fa kuka kike yi”
“Tunani kawai nake yi, makomar yayana idan bana raye that's...”
Ta karasa wasu hawayen na sauko mata.
“Haba Ummi ki daina kawo wannan abun a ranki please, ba zai taba faruwa ba tare zamu rayuwa In Shaa Allah”
Ya rumgume yana jin wani emotional, he can't imagine his life without her, ta ya za su iya rayuwa.
“Ummi ba zamu iya rayuwa ba idan babu ke, babu wanda zai rayu babu uwa a kusa da shi kuma ya more rayuwa, there's no love like a mother love for her child”
YOU ARE READING
WANI GARI
General FictionA wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta ball...