*KISHIYAR ƘABILAH 7...*
BY SURAYYAHMS.
Tunda Ahmed ya kama hanya zuwa Airpot bai sake ya bar wayarsa a kunne ba acikin gaggawa kawai yake tuki dan already lokacin tafyr tasa baifi saura minti goma ba.
Daga ta cikin gidan kuwa Ko ina yy fess fess kowa yaji kyau andau qamshi kowa ya saka hadadden kayansa mai tsari duk anyi kyau musamn ma kafayat buraimo data sako backless red flowing gown dinta mai tsada.
Kowani lungu na cikin gidan anyi decorating dinsa ne da heart shape ballons da katoton red flyr an rubuta will u marry me ajiki mai ja da fari ana jiran shigowarsu Ahmad da mamansa ayi suprising dinsu.
8.40 am dot hajya khadijatu ta doka sassanyar sallama acikin gidan snn ta shigo ciki fuskarta dauke da fara'a tanamai furta wow wow masha Allahu ganin inda waje yy mugum kyau dn anka kashe kudine akayi romantic decorations da abubuwa masu ban sha'awa da burgewa sosai.
Dukan tara tara sau goma kirjin kafayat yy dataji sallaman hajya khadijatu,rashin jin muryan Ahmed bai dameta ba ,dan a tunaninta lokacin cikar babban burin xuciyarta ne yaxo.
She was soo nervous and excited to the wings tana jin kanta acan sama kamar wacce zata tashi sama dan murna.
Nan Kowa yaja ya tsaya in position aka rage hasken wajen ya dawo dim ana jiran Ahmed ya shigo sai ayi suprising dinsa. After some min saiga haj khadijatu ta bullo ita kadai ,tun kafin su fara gaisawa anty ramotou tajata gefe murya kasa kasa, tace iya dami shushhh, pls dont talk loudly u will ruin the suprise for the kids.
Tooh ina shi damilare din yake,ya baki shigo ciki tare da shi ba kuma?
tun kafin hjy khadijatu ta amsata caraf kafayat ta juyo ta tsareta da ido da alaman tanajiran jin amsar itama
Hajiya khadijatu tay murmushi snn tace ku kwantar da hanklinku Ahmed yana waje dan tare dashi mukaxo shiya jawoni ni ma a motarsa.
Anty ramotou tay yake tana duban kafayat data sunkuyar dakanta kasa tana dan murmushi tace Alahamdulillahi rabboul Alameenà
"Why is he not here yet."
Anty moju ta katsesuAcikin girmamawa hjy khadijatu tace "ohhh He said he wll be parking his car outside, Nasan ma hala harya kammala parking din. Wani irin sihirtacyar ajiyar zcya kafayat ta sauƙe snn ta dauke idanunta akansu jin ta samu wani nitsuwa ta cikin ranta.
Anty ramouto tace its okay, kowa yy shiru..any moment Ahmed will be in and in sha ALLAH he wll love this .
Nan kowa yay shiru sunata murmushin jin dadi,after some few mins wajen kimanin 25mins ya tafi abanza anata jiran ganin Bullowar Ahmed sai shiru abun nashi har ya soma sakasu cikin suspense duk wani motsi ata bakin kofar sai sun leka amma sai shiru..
after like 20 more min Anty moju tafara mita kadan kadan da yaren su tana cewa wnn wani irin parking mota ne aiko kera sabuwar mota yakeyi albarka..anty ramatou ne ta dan fara calming dinta dan karta fara daga musu hnkli.
Sosai kirjin kafayat yake bugawa taciki sai tafara jin tsananin bugun zuciya da fargaba mai karfi na neman hadiyeta amma bata san na menene ba.
Da shirun yafarayin yawa Haka nan kawai sai ta soma tunanin ko Ahmed ya fasa zuwa ne dan tasan zai iya aikatawa, thinking of that make her soo weak tafarajin kmr ana suyar masa ne akan kaskon kirjinta.
Gashi ta gama cika baki wa kawayenta na business cewarta ayau duk wani gulma da akeyi akan maganan jinkirin aurenta da Ahmed zai zamo tarihi, and she wll update them live dan suga engagement dinta da Ahmed.
So One of her close business partners mrs Zikirat fasihu da gulma ya mata yawa, ta kasa hakuri tanajin labarin partyn already harta kira mahaifyar kafayat din awaya ta watsa mata labarin dan tasan me ake ciki,babu abunda zikirat bata sani akan rayuwar kafayat ba sabida yawanci idan kafayat tasha giya hakanan take zama ta juye mata dukkan wasu sirrinkan dake cikin cikinta.
YOU ARE READING
KISHIYAR ƘABILA...
Historical FictionBansan meye Soyayya ba kace? Soyayya fa kace Ahmed? Kasan ma'anar kalman soyayya ma kuwa? Toh barikaji, Soyayya shine wanda na maka Ahmed, sabida Soyayyar ka shine ya rabani da Addini na, kabilata, da iyayena...tayaya ne xan Amince da wann juyin mul...