*KISHIYAR ƘABILAH 15.*
BY SURAYYAHMS.
Yola:
Wajajen karfe 4pm na yamma su Ahmed suka kammala shiryawansu izuwa gidan Alhaj Aliyu mijin kakar adiaha.
Already brother kazim Aremu daga can u.s haryay magana da wani Abokinshi mai kudi dan siyasa ne honourable sabo, nan da nan aka musu arranging motoci guda uku na kece raini da zasu je gaisuwar dashi, black colour lexus guda biyu da DBX jeep, dukan su suna zuba kyalli aka dire musu agaban hotels din snn aka hadasu da official drivers.
Dukan su manyan kaya suka saka, dan uwan mahaifinsu mai suna uncle bakre da brother hamzat sun sako shadda ubansu mai gare da hulunansu masu shegen tsada wanda daga ganin su za kasan cewa shigar tasu ta barazana ce kawai da suka shirya musu dan suja girma wa familynsu sosai, brother hamzat dimeji yasaka golden colour shikuma uncle bakre ya saka wata royal blue getzner, Banji ya saka black half jumfa bugun kamfani, Ahmed kuma ya saka full fitted jumparsa sky blue colour mai wani irin kyau da sheqi dukansu sun sako hulunan da sukai matukar dacewa da kayansun sosai.
Fadin irin kyan da sukayi dukansu acikin shigar tasu bazai iya misaltuwa ba,banda qamshin turare masu dadi babu abunda yake bibiyarsu dan a kallo daya kamasu zaka iya sanin cewa tabbas suna dashi snn sun kece raini.
Already sun siyo duk wata tsarabar gaisuwar su ta aure na alfarma wanda zasu kai gidan alhaj aliyun domin Adiaha,brother kazim ya riga ya gaya musu cewa yana son ayi komine a lokaci guda batare da bata lokaci ba,yace idan har mutanen Adiaha basuda wata matsala har kudin sadaki ya tanadar su bayar sabida baison ayita memeta jeka ka dawo tsakanin Abuja da yola.
Tun safe Adiaha take cikin zullumin abunda zatayi kafin su Ahmed suxo danko kayan da zata sakanma ya zama mata damuwa dan data gudu agarinsu batazo da kayanta ba sai wanda yake jikinta. Tay girki kala kala ta aje dan al'adarsu ne su bada abinci awajen neman aure. Komi tay ta shirya snn tay wanka tay kwalliya Karshe wani tsohon Abaya mai kyau hjy hajarat ta dauko ta bata akanda tasaka kafin suje sumata siyayya washe gari. Shekarun su yaja sosai yanzu ba wani neman kudin sukeyi sosai ba, iya dan abunda suka tarar ne suketa lallabawa ahankli sai temakon da yayan alhaj aliyun suke kawo musu.
Wajajen karfe biyar saura motocinsu Ahmed suka bayyana acikin harabar gidan alhaj Aliyu inda aka musu iso izuwa cikin babban falonsa ta alfarma.
sallama sukayi daga waje sai akazo aka shigo dasu ciki, nan suka tarda shi a falonsa tare da manyan yayansa maza su biyu, da kuma limamin da ya musuluntar da Adiaha da wani dan uwansa malam shehu.
Tunda su Ahmed suka shigo ciki Sai satar kallonsu awajen akeyi sabida yanayin shigarsu ta kece raini da wayewa.
Cike da girmamawa
Da karrawa akayi yar gaishe gaishe snn aka fara tattauna dalilin daya tarasu.Tunda manya suka shiga tattauna zancen auren Ahmed baice uffan ba dan tunda ya rusuna kanshi ƙasa babu abunda yake tunani sai komawarsa gidan dan sosai ya gaji da batun auren nan. Iya abunda yaji awajen shine da akace musu ai Adiaha ta riga ta musulunta snn harma ta amshi sabuwar sunanta na musulunci wato REEMA BASSEY
Sunan REEMA suna ne mai kyau na larabci,duk dama wasu yararruka suna amfani dashi da wata ma'ana daban,a harshen larabci sunan REEMA yana nufin "white gazelle" or "a Good and polite at heart person"...
Sosai sunan ya dace da Adiaha dan ita yarinyace mai kyawun hali da saukakken zuciya mai taushi.
Saida akayi kabbara snn Ahmed ya daga kai shima yay dan murmushi jin kowa na mata murna, yanajin su uncle hamzat da uncle bakre suka karkare maganan nasu acikin mutuntawa.
An yarje an amince za'a bawa Ahmed auren Adiaha,saidai ko da aka kawo zancen saka rana sai dukansu suka fara yin baya baya da zancen hidiman biki musmmn ma da aka ga kamar su Ahmed din suna da shi sosai
YOU ARE READING
KISHIYAR ƘABILA...
Historical FictionBansan meye Soyayya ba kace? Soyayya fa kace Ahmed? Kasan ma'anar kalman soyayya ma kuwa? Toh barikaji, Soyayya shine wanda na maka Ahmed, sabida Soyayyar ka shine ya rabani da Addini na, kabilata, da iyayena...tayaya ne xan Amince da wann juyin mul...