10

117 11 0
                                    

*KISHIYAR ƘABILAH...10*

BY SURAYYAHMS.

Saida Adiaha tay nisa sann ta tsaya da gudun datakeyi ajikin jejin tanayi tana dan juyawa baya tana sauke haki.

Mannuwa tay da jikin wani katoton mahagony tree mai wani irin tsayi da duhu idanuwanta a lumshe hannunta dafe da kirjinta tanamai sakin wani irin zazzafan huci..

Wani abu takeji ajikinta na mata yawo zurrrrrrrr tare da sunan Ahmed dake mata amo mai ruri acikin kololuwar zcyarta da kwakwalwar kanta tanajin wani iri irin sassakewar jiki tamkar wanda sihirin soyayya mai karfi ke fuxgarta akanshi wanda bata san daga ina yake fitowa ba.

"Ji take kamar bazata ma iya rayuwa a duniyan nan in batare da Doctor Ahmed bello jimada ba"..

Wani irin bugawa zucyrta yakeyi akansa, kirjinta na sama da kasa cikin hucin tsoron mai tafe da tashin hankli na rashin sanin me zatayi da rayuwarta aynxu.

Kara lumshe idanunwanta tayi tabi tay tsamm ajikin bishiyar jin har an biyota ana kwala mata kira acikin jejin acikin tashin hankli da alaman kowa yafito ne anata nemanta.

ADIAHA...ADIAHA..ADI?
Muryan kawunanta mr akpan da mr udo da na kawayenta duk ya cika koina ajejin,jin muryan
sun a kusa kusa yasa ta sake ballewa aguje ta kara shigewa can cikin jejin taje ta buya akan wani boyayyen tsaunin ciyawa inda tasan ba lallaine suyi tsammanin ta awajen ba.

Banda kuka mai sanyi babu abunda takeyi, ahankli tay ta rakube harta haura can saman tsaunin ta zauna ata inda ba wanda zaiji motsinta koya san tana cikin jejin gabaki daya.

Haka har aka karace nemanta aka dawo gida ba aganta ba. Wani tashin hanklin da ba'a saka masa lokci shiya shiga wanzuwa tsakanin kawunanta, mahaifyarta da kuma bakin da sukazo neman aurenta.

A Daren ranan saida ran kowa ya bala'in baci akan abunda tayi.

Mutane dayawa sunyi Allah wadarar da ita snn babu kalar tsinuwa da ba'a yi akan rashin isashen tarbiya da dattakon gidan nasu da ake cemasa gidan mr bassey ba.

Guduwan da Adiaha tayi saida yazamo wani babban taɓo agare su, harga shi kansa yaron da ake son ahadata dashi, iyakan abunda tay masa ayau kadai ya isa ya zamo masa abun gulma, snn duk inda ya shiga neman aure za'a nunashi ace shine wanda budurwa takishi snn ta gudu masa awajen consent taking dinsu.

Sum ppl now will start seeing him as a cursed ko wanda yake da bakin jini acikin al'umma...

Taruwar dangi elders din yankin sukayi akan familynsu adiaha kowa na fadar albarkaciin bakinsa Musammn ma dayake bayau aka fara samun babban abun kunya acikin wann familyn nasu ba.

Bayan kura ya dan lafa kowa ya watse bakin ciki mai tsanani shine ya rufe fuskokin mrs grace tare da uncles din adiaha wato uncle akpan da uncle udo.

Uncle akpan shine yake bin mahaifinta,shikuma uncle udo twin brother mahaifinta ne sune manyan yaƴa acikin mahafiyarsu mrs chidara
Wanda ahalin yanzu bata tare da su sabida musuluntar dataje tay aure a garin adamawa.

Har wajajen karfe 9 na dare adiaha na zaune ajeji tanamai tunanin rayuwarta wanda yake da yawan rikici da rudani mai yawa aciki.

kokri take ta raba gardama tsakanin soyayyar datakeyi wa familynta da kuma wanda takeyi ma rayuwarta ayanzu.

Dan tabbas idan ta zabi tay rayuwarta yadda take so toh komi zai lalace musu tsakaninta da familynta dan tasan babu abunda zai iya hanata musulunta domin ta aure babban muradin zuciyarta wato dr Ahmed.


Idan kuma ta zaɓi ta hakura da soyayyr Ahmed dan familynta tasan hakan zai kawo martaba wa iyayenta da familynta nata saidai ahalin yanzu batajin aranta kmr zata iyayin rayuwa agidan wani da namiji inba doc Ahmed ba.

KISHIYAR ƘABILA...Where stories live. Discover now