CINIKIN RAI....!
Beauty and the Beast♡
007
_Wace ce Xno?🌚 Da za a wani dame mu da ita, yar daba da ita😏🚶🏽♀️ sai mun bindige yar tusa kanwarka tutu, yan comments section aji tsoron Allah 🙄🙄😏 ku daina abin da kuke._
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>
_Past_
"Ni Malik!" Ya nuna kanshi, yana me kallon ilahirin mutanen da suke wurin. Sannan ya nuna su da yatsa. "Bani da had'i da ku, sannan shi bai da haɗi da ku, don haka kowa ya kama gabansa, idan ba haka ba tow kuwa zan mai da hankali wurin girbe rayuwarku." Ganin yadda ya iya kashe dabobbin da Dulma yaƙe takama da su, babu tausayi balle imani, yasa suka fara ajiye makamansu, suna barin wurin domin kuwa suna son kansu. "kai Malik waye kai? Kana abu kamar wani mutum, bayan kowa yasan cewa uwarka ma karuwa ce."Wani irin b'acin rai yake ji, idan ya tuna abin da ya faru, idanunshi a rufe suke, a hankali ya buɗe su, sunyi wani irin jajjur tare da ƙwanciyar jini a cikin ƙwayar idanun. Ya juya tankar juda. Cillar da sigarin yayi ya juya kofar kegin zakunan ya ballo wani murtakakken karfe, ya nufi dulma da zazzababen gudu, yana isa wurin kafin Dulma ya ankara tuni ya zuba mishi karfen a tsakiyar kansa, zubewa yayi jini na fita ta hancinshi da baki da kunne, sannan ya juya wurin motar da ya zo da shi, ya ciro igiya, ya daure kafar Dulma ya daura da boddy motar, ya shiga jan shi. Kafin ya shiga cikin ma'aikatan, ya ciro mutanen da aka kama su, tare da sake mutanen da suke aikin bauta, sai da ya tabbatar da ya sake su, sannan ya rufe ma'aikatan ya zuba nakiya ya saka mishi lokaci, ya tattara dukiyar da ya gani, kudi da wasu abubuwan matasa da maigidanta da suke wurin ya mikawa. "Kuje da shi, duk wanda ya iya tuka mota, ya tabbatar ya ja sauran mutanen" daga haka ya shiga motarshi, sauran mutanen suka shiga motar da mutanen Dulma suke amfani da shi. Sai da yaga fitarsu, sannan ya take musu baya, yana jan Dulma. Har suka fitar daga Hill and Tim town, sannan ma'aikatan Ma'adinan ya fara fashewa da rushewa. Kome na wurin kamawa yake da wuta. Bakidaya ma'aikatan ya lalace ya kone, ya kuma rubta cikin ramin da suke hako kuzan. Yana hango rubtawan. Wani smirk yayi irin na tsantsanar mugunta da zalinci. Haka ya cigaba da gudun ganganci da Dulma, har ga shiga cikin garin Fiston ya tsaya a daidai kofar birnin. Ya sauka a motar, ya kunce dulma ya daura a kofar birnin. Sannan ya wuce zauna a saman motar. Yana kallon gawar Dulma har yau wutar da yake ci a ransa bai mutum ba, baya ji zai mutu. Kome zai yiwa mutanen ba zai tab'a wucewa ba. Domin bai ji ya huce ba.
Wasu daga cikin mutanen Shu'iba sun kai mishi labarin abinda ya faru, kamar zai yi hauka haka yake ihu, kamar ya fito daga maboyansa ya fuskanci Malik amma sun hana shi, domin babu Allah ya cikin al'amarin Malik. Yana ji yana gani Malik ya kashe mishi dan uwa, sannan ya rubuta a gefen fuskar gasar Dulma.
*Dan daudu idan ka gama gudunka, namiji yana jiranka* wannan abin da ya faru, ya sakawa Alhaji Nasr Hadejia, shakkar shigar Malik cikin lamarin, domin dai har ga Allah babu yadda za ayi su nemi taimakon dan daba, kuma makashi mara imani. Ko da yake a wani bangaren sun kammala aikin bude wurin shakatawar.A lokacin bikin buɗewa ne, Iyalan Alhaji Nasr Hadejia suka tawo, daga nigeria. Aka yi bikin buɗewa cikin farin ciki da murna, har aka bude, dukkanin farinciki ya wanzu a fuskarsu. A lokacin ba laifi sun samu masu shigowa daga wasu ƙasashen yawon bude idanu, sai dai wasu abubuwan da suka faru kafin buɗewa wurin shakatawa. Kudin hannunsu yayi mugun sauka. Babu wanda zasu dauki ma'aikata da wasu abubuwan. Daga shi kansa Hadejian har Yamini, suna cikin wani irin matsi, sai suka yi decided amsar bashi daga banki inda suka nemi Mayor Fahad ya shiga cikin lamarin, shi kuwa ya ce musu. "Ai kuwa ba sai kun nemi na banki ba, shi mutumin da ya taimaka muku, yana badawa, kuma zai baku da Amana" duk da Nasr Hadejia bai so ba, amma haka ya amsa domin ya lura Yamini ya amince. Don haka ya saka a ransa, zai amsa amma matuƙar akwai ruwa a cikin zasu hakura. Don haka suka tsayar da lokacin da zasu je amsa,
**
*Present*
Sakarwa kanta, ruwa tayi tana tsaye a gaban shawa, baki daya kanta sarawa yake. Idan idanunta ba karya suke mata ba, tabbas taga wani abun da ya tsaya mata a kai, a lokacin da suka bar wurin yar sanda, akwai wani abu da ta san shi tsawon shekarun rayuwarta, daga baya kuma ta daina. Wani irin sarawa kanta yayi, tare da zubar da jini daga hancinta, tun shekarun baya take fama da wannan zubar jini. Sake ruwan tayi da karfi, tana me rike hancin, sai da ta d'ago kai sama, wani irin kara kamar na Harbin bindiga. Toshe kunnanta tayi, tare da zubewa akan gwiwarta. Hawaye ke zuba mata kamar an bude famfo domin dama idan ta fara irin wannan ciwon, ko a kaita asibiti. Ihu ta ta fara da karfi, wanda ya janyo hankalin mutanen gidan, har rige-rige suke na zuwa ɗakinta. Dakyar aka balle kofar ban daki, daura mata towel Ammyn Abbas tayi, suka fito da ita aka saka mata kaya, suka nufi asibiti da ita, a hanyar tafiyar ne Ammyn Abbas ta kira wata mata. "Dr Saddikah, gamu nan a hanya jikin Zeeno ya tashi fa " "Ok ku kaita zan zo yanzu." "Tow gamu a hanya." Ko da suka isa, an karɓe ta. Aka shiga bata kulawa. Kafin wani lokaci har an mata alluran da ya saka ta, barci. Lallai dan adam ba a baki kome yake ba, yanzu kake takama an jima zaka zama ba kome ba. Abin da ya faru kenan.
YOU ARE READING
CINIKIN RAI..... beauty meet the beast
FanfictionMutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin sa ba a dawowa.... Silar su mutane dayawa su...