Chapter:18

171 10 0
                                    

CINIKIN RAI....18
      Beauty and the beast.
  Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Kamar ya sake zawo a wandonshi ya ce mata. "Zeenobia ayi haka a hakura da shi kawai." "Bata lokacinka kake kawai, amma tabbas sai na ga Malik duk abin da zai faru sai ya faru!"
        Tabbas yaso haka, amma bai tab'a zata haka abin yake ba, domin ta ga Malik duk ta haukace, fisabilillahi sai kace akanta aka fara samun matsala, kome sai taci da karfi, sai kace jikar iliya dan mai karfi, gaskiya ba zai yarda da wannan zancen ba.
           "Chairman kayi hakuri, amma na yanke kuma haka zan aiwatar da abin da nayi niyya." Daga haka ta kashe wayar tana me kallon wardrobe dinta, tabbas dole ta kure a daka domin zata gamu da Malik, domin bata son ta isa wurin shi yayi mata kallon bata kai wacce ta dace da ya hadu da ita ba. Kallon madubin mirror dinta tayi
      Ta juya tana kallon bayanta, d'aga pillown kwanciyarta tayi tare da kwashe atm dinta, ta dauko abaya ta daura, sannan ta fita shiga motarta tayi tana faɗin. "Dole yau na gyara kaina da jikina." Ta fada tana bawa motarta wuta.
           Ita kanta tana jin wani irin d'auki na son ganin gawurtaccen zakin da ya hana kowa sakat, so take ta ga yadda ya samu damar yake bugawa kowa mulki kamar masarauta. BINTUN BATUL SALOON WORLD AND SPAN.
          Gyaran jikin da saloon ake a shagon, kamarsu dilke, lalle, da Makeup. Ba karamin wuri ba ne, domin yaran masu kumbar susa ne, da matan manyan suke zuwa wurin. A hanyar titin da zai kaita wurin suka hadu da ASP Zulfa. Bin motar tayi da idanu, a hankali ta bude file din gabanta. "Sajan Barau yarinyar nan, me yasa bata da kamun kai?" "Madam bata da laifi fa, haka iyayenta suka watsar da ita, kuma ta daura rayuwarta a kan haka!"

    "Allah ya kyauta" "Amin" ya fada.

★★★
Demark
Zaune suke a dinning room, kowacce da abinda take bukata. Kallon juna Wahida suka yi da Nadrah. Suka dauke kai, "Wahiba ina Maidah?" D'aga kafad'arta tayi tana faɗin. "Tana can dakinta!" "Atikah ajiye abincin ki je ki kirata" domin yau ta lura Wahiba bata jin yan surutun. 
Lokacin da Atikah ta isa dakin, ta samu tana shiryawa ne, cikin girmamawa ta ce mata.
"Jaddah tana kiranki!" "Tow gani nan" ta fada tana gyara zaman yan kunnenta. "Tow!" Atikah ta ce mata, a hankali ta juya ta cigaba da abinda take, sai da ta gama sannan ta shiru tana tuna maganar da Lalla Salmah ta gaya mata jiya.
   _Ni ban aiko ki, ki zama yar kallo ba ne, na aiko ki ne domin ki rabe Malik, Jalilah zata miki kome, domin itama tana da fushin Malik bana son ki gaya mata gaskiya. Kada ki sake Nadrah ta rena ki domin zan mugun sab'a miki._
      Ta rasa yadda zata yi da ranta, yau kwana biyu da zuwanta, idan ta cire Wahiba da take kulata, sauran babu me kulata kowa ta kansa yake, a hankali ta fito a dakinta jikinta a sanyayye. Koda ta isa dakin cin abincin, baki daya hankalinsu na kan abincinsu. Zama tayi ta fara kokarin zuba abincin. "Ki sake jikinki, nan ma kamar gida ne. Ki daina zaman a daki kamar wata bakuwa." "Hmm! Kin san bakon da yazo birni daga kauye dole ya koma dodon kanshi." Juyawa Nadrah tayi tana kallonta, domin itama yau da safe Babanta ya kara mata magana, akan lallai ta samu shiga ga Malik. Domin an turo Maidah ce, domin ta samu Malik. Yadda ya tsara mata kome, da yadda zata na dragging din Maidah har ta ji ta gaji ba zata iya shiga rayuwar Malik ba.

       Wahiba da Wahida, basu kai su shekaru ba. Amma kuma suna sane da cewa Dad ɗinsu anyi maganar aurenshi da Nadrah aka fasa. Amma kuma dawowarta wurinsu yasa baki daya suke shiri da ita musamman Wahida domin tafi Wahiba kirki da saukin kai, amma kuma idan ka gansu su uku, zaka dauka cewa halinsu daya ne.
"Jaddah kin gayawa Dad saura kwana biyu, Birthday dinmu?" "Kici abincin zamu yi magana idan na gama!" "Na koshi!" "Kin san dai ba zai saurare ki ba, idan baki ci abinci ba."  "Jaddah don Allah ki saka baki ni na gaji da Demark mu koma Keivroto kinji.!" Inji Wahiba.  Kallonta yan matan suka yi, ta saka fuska kamar ba ita tayi magana ba, dama ba gwanar magana ba..
 
     "Ya ce zaku koma, har da ni amma sai yayi aure domin yadda zaku ji dadin zaman gidan da mace a cikin gidan idan babu mace ai babu magana."  Cikin karambani Nadrah. "Jaddah wani auren zai yi?" Take Sayyadah Qudussiyah ta d'ago inda Nadrah ta dosa, gyada mata kai tayi, ajiyar zuciya ta sauke, tana faɗin. "Akwai wani abu ne Nadrah!" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Babu kome " ta fada tana mikewa. "Har kin koshi?" "Eh" ta wuce dakinta, ta dauka jakar makarantarta, ta fita daga gidan baki daya, domin tana bukatar shaƙar iska me sanyi don Allah kadai yadda take konewa ta cikinta, Malik yayi rejected ɗin aurenta. Ba tare da wani dalilin ba, kawai yayi dumping ɗinta, ba tare da tasan dalili ba, da farkon da Babanta yace zata auri Malik da kwana biyu su shigar da shi kotu, karshe a raba dukiyarshi a basu, tayi farinciki ko babu kome zata shiga sawun matan da suka shahara, amma once lokacin da aka gama kome suka yi magana da Malik sau biyu akan ta amince zata aure shi, sai da magana tayi ƙamari kowa ya sani, duniya ta dauki al'amarin bawan Allah nan ya kira Babanta ya gaya mishi ya fasa aurenta.
         Kuma tsabar girman kai, mutumin naj bai gaya musu dalilin da yasa ya fasa auren ba,sai dai kawai ya ce ya fasa kuma har yau tunda ya ce ya fasa ko da wasa bai kuma nimanta ba, wani bin tana jin zai kira Yaranshi su yi ta waya, amma ba zai tab'a cewa a bata ba,  wani abin tashin hankalin tun daga ranar Allah ya daura mata sonshi da kaunarshi.
         Kai ko waya yake kamar ta gigice haka take ji, amma shi ko ta kanta baya bi. Wani abin burgewa ita ubanta yake kokarin shigar da ita, amma ita ta tsaya a ina nan bata son cusa kanta tunda dai baya yi da ita no way da zata ce sai yayi da ita, number wayarshi hotonshi da Yaranshi suna wayarta amma ko sau daya bata tab'a gwada kiranshi ba. Tana tsoron kada ta kira ya sake mata gwiwa.

CINIKIN RAI.....  beauty meet the beastWhere stories live. Discover now