Chapter:3

221 22 1
                                    

BOOK ONE
003
"Mr Amjad!" “ Kiyi abin da na saka ki, babu ruwanki da Malik Menk Jordan, idan da kin ga abin da ya faru, ba zaki fara shiga wannan lamari ba. Kowani mutum yana da iyakarsa don haka ki tsaya iyakarki” kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta ficce daga office ɗin, lallai tana son sanin waye shi? Me ya taka har haka da kowa yake jin shakkarsa haka. Tana fita Mr Amjad ya kalli MD da Salim. “a firgice nake, ina ga zan zauna a kamfani na tsawon kwanaki, domin Malik ya manta da ni, idan ba haka ina fita qur'ani kashe ni zai yi."

        Shiru sukayi kowannen su, da abin da yake yawo a ransa, kafin Salim ya ce masa. “Yallabai me yasa ka razana haka ne? Ni fa bana tunanin Malik ya kai yadda kuke fada, kawai kashe prime minister yayi haka ne domin ya cusa muku tsoro da firgici. Kuma yayi nasarar haka"  juyar da kai Mr Amjad yayi yana kallon window waje. Kafin ya mike kana ganin yadda fuskarsa ta nuna zaka fahimci yana cikin damuwa soka hannunsa yayi cikin aljuhun wandon ya ce.
       “Tabbas rayuwar tana tafiya da yadda mutane suka tsarawa kansu, amma rayuwar da Malik ya tsarawa kansa, yafi kowacce rayuwa bala'i.” Kallon juna MD da Salim suka yi kafin suka mai da hankali kan Mr Amjad.
           Kuma aka rasa waye zai magana, wayar Amjad ne yayi gunji. Kamar ba zai dauka ba, ya dauka.“Amjad Lamid ne?” kamar wanda aka watsa mishi ruwa haka ya amsa da cewa. “Eh ni ne, waye” “Na kira ne, na baka shawara kada ka sake shiga abin da babu ruwanka tsakanin Malik Menk Jordan da Mr Khuldu Jahid Khan”
  
    “Amma waye kai?” Mr Amjad ya tambaye shi, murmushi me sauti na wayan yayi sannan ya ce mishi. “Sani na bai da wani amfani, amma zan baka shawara ka nisanta kanka, daga wannan hatsaniyar Malik ya fi ku hauka, a duk lokacin da ya fahimci kana cikin masu niman shi sabga shi.” ya fada mishi yana kashe wayar.

         Wani azzababen tsoro ne ya mamaye zuciyar Mr Amjad, ilahirin jikinsa rawa yake, yadda zaka fahimci, yana cikin tashin hankali. "Sir akwai matsala ne?"  Kallon MD yayi da ya tambaye shi, sannan ya ce mishi.

     “Na jima ina Kasuwancina, ban tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, amma qaddara sai da ta haɗa ni hanya da Malik Menk Jordan, a da wai-wai nake shi a yau da na gani da idanuna na tabbatar shi din ba kanwar lasa ba ne.”

        “Sir wai mene ne matsalar ne?” MD da shima yake razane, domin daga yadda Mr Amjad yake firgice zai tabbatar maka da cewa yana razane. “Ban san kaddaran da ta hada ni da Malik ba? Amma nasan mutuwa ta ce ta kusa bayan haka” kura mishi idanu suka yi. Sannan ya cigaba da cewa. “Idan har kuka ji labarin na mutu don Allah ku saka idanu akan iyalina.”
   Su kansu a rude suke, domin kuwa labarin mutuwar Prime minister ya ratsa lungu da saƙo na cikin garin Keivroto city.

       ^^^^
A lokacin da Zeenobia ta bar S..... Digital art, ta nufi hanyar gida da mutanenta, a nan ne ta fahimci garin ba lafiya domin duk inda suka wuce zanga-zanga ake wanda zai nuna maka, alamar kowa a fusace yake, ko da yake ai ba kowa bane domin wannan rigimar ba don talaka aka yi ba, suna yi ne domin kare muradunsu da aljuhunsu. Duk wanda zaka gani tow ba yana yi don talaka ba ne, yanayi ne domin cikawa aljuhunsa yan canji.

      Ajiyar zuciya Zeenobia tayi tana kallon yadda ake fashe-fashe, babban burinta su isa Al'umma charity House, domin kare wannan gidan hakkine da ya rataya akanta, ba iya ita ba, ga duk wanda yake numfashi a cikin gidan.  Domin ganin yadda yan zanga-zanga suke barnan dukiyar gwamnati, yasa ta kalli black ta ce mishi.
     “Ka taka motar, mu isa akan lokaci domin za a iya saka curfew nan da wani lokaci.”
        “An gama Yar kunama!” Ya kuwa karawa mutanen gudu, cikin ikon Allah suka isa gidan cincirindon jama'ar gidan a bakin get din gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya.  "Yar kunama!" Sauka tayi daga motar tana kallonsu. “lafiya kuka yi cirko-cirko?” ta tambaye su, tana cire glass din idanunta. “ina zamu iya nutsuwa mun ji labarin gari babu lafiya, ke kuma da su Dundurosu kuna waje.” murmushi tayi ta wuce bakin get ta ja kofar tare da rufe kofar gidan bakidaya. “ina son nayi magana da murya daya, kowani lokaci za a iya saka dokar tab'aci, ban lamunci wani ya ketare gidan nan ba, idan na fahimci haka ya faru hmm.”  ta fada tana haurawa sama.

CINIKIN RAI.....  beauty meet the beastWhere stories live. Discover now