CINIKIN RAI....20
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
*Wannan shafin na ku ne, Aunty Halima da Habibay ku more!*
<<<<<<<|=|>>>>>>>>>
Wato dukkan hankalinta ta daura akan shi, har ya fito falon baki ɗaya. *Wheelchair!* Ta furta a kasar zuciyarta. Dauke kai tayi tana dariya ƙasa ƙasa, d'ago idanu yayi ya zuba mata. Sake kallonshi tayi ta kunshe dariyarta, baki daya sai yaji ya muzanta. Jikinshi ya wani irin sanyi. "Ke meye haka?" Dake bata iya boye abin da yake ranta ba ta ce mishi.
"Malik Menk Jordan! Ya kare akan keken guragu. Wai dama wannan shi ne dalilin da yasa shi nisanta kanshi da Al'umma?" Ta kuma kwashewa da dariya, sannan ta dan durkusa akan gwiwarta kamshin turaren Imperial Majesty ya daki hancinta. Sau daya ta tab'a jin kamshin nan, a rayuwarta sai yaui. "Ko a yaya nake bana kunyar haduwa da mutane, sannan maganar pmutane bata gabana. Ni mutum ce me ra'ayin kaina. Ban zo nan domin Kasuwancinmu ba, nazo na ga waye ya firgita mutane da Gwamnatin kasa baƙi daya.
Ka ji da kyau, bana tsoron tunkarar kowacce matsala, amma a karon farko na rayuwata da na ga makirkirin matsala ya koma gefe yana gudun matsala, shi yasa na mishi dariya. Da nasan cewa Malik Menk Jordan ya gudu daga cikin al'umma saboda nakasarshi da ban tako nan ba!"
A karon farko da yaga macen da ta saka shi ya ji ashe, shi in matsoraci h ne. Ashe tsoro ne ya saka shi boye kanshi. Kasa magana yayi ya kalli Elbashir. "Coffee take bukata ko Tea?" Wani dariyar takaici ne ya kamata, wato shi a haka har wani izza ce da shi. Haka kawai zuciya ta ingizata ta kai mishi naushi. Kafin ta idda nufinta, ya ja kekenshi. Sai da ta fadi can.
"Ke baki da hankali ne?" Elbashir ya fisgota zai kifa mata mari.
"Kyaleta mana, bakuwar mu ce tana buƙatar karramawa ko wacce iri ne!" Gyada kai yayi. Fita yayi kallon Malik tayi yana tafiya a keken shi har gaban wani table. Zaman shi ya gyara yana kallonta. Nuna mata kujeran da yake facing ɗinshi yayi.
Hadiye yawu tayi tana me zama dakyau ta ce mishi. "Da gurgunta kake niman maza?" D'ago kai yayi ya kalleta, kasa tayi da kanta tana wasa da file din hannunta. Kwarjini ya mata lokaci guda, yadda ya kura mata idanu, tana jin ba dadi domin tsakani da Allah idanunshi na da kaifi. "Me kake so?" Ta tambaye shi muryanta a shake. Murmushi yayi yana me juya kekenshi. Shigowa aka yi da tiren tea. Elbashir yana biye dasu, duk maza ne kuma matasa.
Ajiye a gabanta suka yi, Elbashir ya koma gefenshi ya tsaya a gefenshi. "Sha!" Ya fada a sassanyayye. "Ba na shan ruwa ko wani abu a inda ban yarda dasu ba!" Murmushi yayi ya ce mata. " "Sugar nawa kike so.?" "Guda bakwai!" "Bakya tsoron ciwon sugar ne?"
"Waye ya damu idan na mutu? Don haka zanji dadina kafin na mutu." Duk da tarin yarintar da ya hango a tattare da ita, amma kuma ya fahimci tana fadar duk abin da ya fito daga zuciyarta ne. Sai da ya zuba mata sugar hudu, ya juya kafin ya d'an diba a cokali ya sha kaɗan, ya tura mata. Da wutsiyar ido ta kalle shi ta ce mishi. "Duk da haka ba zai saka na sha ba ""Ok" ya kai spoon zai diba Elbashir ya ce mishi. "Malik ka manta baka shan sugar!". Juyawa yayi ya kalli Elbashir ya ce mishi. "Kai haba dole mu karrama bakuwar mu"
Sai da ya sha sau uku kafin ya tura mata har da cookie ɗin. A hankali ta dauka tana kallon coffee ɗin. Kurba tayi a hankali, "Idan kuma da mun saka, guba fa?" "Tunda ya sha ai zamu mutu tare ne!"Murmushi Malik yayi yana kallon ɗan bakinta yayi, yana girmama maganar da yake fitowa sam babu mara ma'ana sai dai rashin da'a. Ajiye kofin tayi tana faɗin. "Ya ishe ni" "Muje ji ga gidan!" "Tab! Ba ji ya kawo ni ba." Ta mika shi file ɗin. "Da dai kin tashi kunje!" A fusace ta kalli Elbashir.
"Ban zuwa wani abu ne?" Ta tambaye shi, "ko daya"
"Ok Ina file ɗin!" Mika mishi tayi ya dauki medical glass ya saka sannan ta ce mata. "Su mutanen da suka baki aikin me yasa basu, bawa Yaransu ko su kansu ba?"Shiru tayi tana kallon shi, sam bai yi kama da wanda yake dogon magana ba, amma yadda yake magana. Yana kara saka mata mamakinshi.
"A Kasuwancinmu, cinikin rai yafi kome armashi da me zaki biya asarar da aka min?"
Kallon shi tayi, sannan ta ce mishi, "Na sani rayuwa ita ce fansar, tsinannen dukiyarka"
"Ke ki iya kalamanki!" D'aga hannu yayi alamar Elbashir yayi shiru. "Hmm! Ina jinki." Ganin babu ɓacin rai ko muzanci a kan fuskarshi yasa ta sake wani lalacin murmushi ta ce. "Ba fa ni ce ba fada ba, abin da naji mutane na fada ne, me yasa ba acin dukiyarka?"
"Saboda gumina ne, babu gumin kowa a cikinshi."
"Kana cire hakkin Allah kuwa a cikin gumin naka?" Rintsa idanu yayi ya ce mata. "Bana cirewa ko zaki cire min ne?". Kallon shi tayi sannan ta ce mishi. "me yasa kake jin haushi?" Nuna kanshi yayi sannan ya ce mata. "Bana jin haushin!" "Kana jin haushi mana, kokarin boye fushin zuciyarka kake, amma kafi wancan sikagon fusata!" Ta kalli Elbashir.
Matse hannunshi yayi sannan ya ce mata. "bana jin haushi, baki gani ba ne!"
"Kana jin haushi tunda gashi kamar zaka karya kashin hannunka, Malik" ta kira sunanshi a hankali, ta fuskance shi. "Kasan me? Nayi abubuwa dayawa a rayuwata, kama manyan laifuka zuwa kananu. Amma na iya saita kaina, kai kuma tunda nazo naga fushi da ɓacin rai a kan idanunka, idan baka manta ba kasan dalilin da yasa na kai maka duka? Domin na kara yarda da cewa kana cikin fushi ne, and saka hannu zan tafi"
Ya kai tsawon shekaru sha uku a wurin zaune, amma babu me zarrar gaya mishi magana ko wacce iri sai an sunkuyar da kai amma yarinyar da yasan da yayi aure da wuri da ya haifi wadanda suka haife ta , take gaya mishi magana son ranta.
"Saka min hannu?" Shiru yayi yana nazarin abun da ta fada, a fusace yake? Yes a fusace yake na tsawon shekaru arba'in yana cikin fushi da fushin wani. Amma kuma me yasa yarinyar ta zo har niman shi? Shin Ishara ce tazo ta mishi ko kuma tazo ganin sirrin shi ne ta gaywa duniya.
YOU ARE READING
CINIKIN RAI..... beauty meet the beast
FanficMutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin sa ba a dawowa.... Silar su mutane dayawa su...