https://chat.whatsapp.com/KZbdBOduk2c2nLpNQp7Qh3
CINIKIN RAI....!
Beauty and the Beast♡
006
_Past_
A lokacin da suka zo ganin wurin dayawan su, sun yi fatan da sune suka kawata wurin domin ai sune yan kasa ba Nasr Hadejia da Aswad Yamini ba. Taya baƙin haure zasu zo su fi yan gari kawo cigaba har haka, wani abin ya tsaya a ransu. Matukar tsaya musu. Kuma ba iya shi ba, asalin su mutane ne masu matukar Kyashi da Hassada da wannan dalilin yasa suka buɗe iyakokin duk wani tubalin bakincikinsu, inda aka fara turo musu yan jagaliya suna yiwa mutanensu daukar amarya. Koda Alhaji Nasr Hadejia ya ga haka sai ya shigar da bukatar jami'an tsaro su shiga cikin al'amarin amma abin haushi sai aka yi rashin dace. Domin yan sanda bakinsu daya. Haka yasa jikinsu yayi wani zai ce me yasa suka nace da son suyi wurin shakatawa? Abin da mutum be gane ba, shi ne fisto yana cikin garuruwan da suke buƙatar a inganta su. Na farko zai samawa birnin cigaba, na biyu matasan garin da suke sana'ar daba da jagaliyanci zasu samu aikin yi, dattawan da suke sana'ar kamun kifi, zasu samu damar baje kolin sayar sa kifinsu. Sannan gari ne masu al'adar gargajiya. Wannan dalilin yasa baki daya mutane biyun nan saka zuciyarsu, akan lallai su kawo cigaba da garin.
A hankali kome ya fara kwace musu, domin a zahirin gaskiya yan daban sun dame su. Abubuwa biyu ya dame su, ga asarar dukiyarsu ga wasu daga cikin mutanensu a hannun yan garkuwa. Akwai wata rana da Alhaji Nasr Hadejia da Aswad Yamini suka hadu a gabbar tsibirin. Kowanen su, yana da damuwa amma dan samu kwarin gwiwa a tsakaninsu yasa suka sauke ajiyar zuciya a lokaci guda. “Hadejia ina ga ya kamata mu sake budar wurin Mayor Fahad Albagwi da wannan al'amarin, idan har muka yi haka tow ba makawa zamu samu adalci, kaf garin nan kansu a haɗe yake ba zasu sake mana mutanen mu ba.” kallon shi yayi sannan ya ce mishi. “Ni ma nayi tunanin haka, amma nasan Allah yana sane da al'amarin mu, Allah zai tsaya mana.”
“Ka saka mana lokaci mu tafi wurinsa, idan yaso sai mu shirya ba.” murmushi Alhaji Nasr Hadejia yayi ya ce mishi.
“Idan Allah ya kai mu gobe, sai mu tafi. Ina son na kira iyalina ne su zo da Yarana.”
Dariya suka saka ya ce mishi.
“ai ku yan Nigeria kuna da hakuri da juriya, ina zan iya wannan hakurin? Kawai malam ja sa Madam ta dawo nan, kafin nan karatunsu da kome nasu zai dai-daita.”“Hmmmmm! Tow ya zamu yi? Kasan idan baka yi hakuri ba, ya zaka yi da hakkin Allah, shi Allah ya sauke hakkin mu da yake kansa, saura mu mu sauke wanda yake kanmu. Ina da Yara mata biyu, ina jin kunyar na bude idanu na kalle su bayan na sabawa Allah, sannan Allah ba zai kare mu ba. Sannan ba zai kare bayan mu ba, amma idan muka ƙare kanmu da iyalinmu Allah zai kare bayanmu bayan mutuwar mu.” jinjina kai Yamini yayi yana faɗin. “Na gamsu da bayaninka. Allah ya kare zuriarmu bayan mutuwarmu” “Allahumma Amin” da wannan suka ajiye zancen zasu tafi wurin Mayor Fahad Albagwi.
Washi gari kuwa Yamini shi da kansa ya taso ya dauki Alhaji Nasr Hadejia, izuwa farfajiyar gidan gwamnati. Sun taras da mutane, musamman manyan baƙi don haka suka tsaya su jira. Bayan kamar minti Talatin sai ga sakataren Fahad ya fito dake an isar mishi da yayi baƙin. Duk da kasancewar sun same mutane a wurin bai hana sakataren isowa wurinsu ba, ya ce musu.
“Ku iso ana kiranku.” mikewa suka yi, tare da bin bayanshi, a cikin ofishin Mayor. Cikin girmamawa da mutuntawa Mayor ya mike tare da tarbansu yana faɗin.
“Malik sune mutanen da suka zo da nufin raya garin Fiston, amma Shu'iba da Dulma sun hana su, har nan suka zo suka min kashedi. Malik na kira ka ne, domin ka taimakawa bayin Allah nan, suna san cigaban jahar nan ta fuskar Kasuwancinmu.” duk da basu ga fuskarshi ba, amma baki daya basu wani gamsu da shi ba, domin kuwa ba a niman taimakon dan daba akan yan daba yan uwanshi. Hadin kai ne dasu, d'ago hannunshi me dauke da zobban ya yi musu wani alama.
“Wai ku gabatar da sunanku?”
"Aswad Yamini, wannan abokina Alhaji Muhammad Nasr Hadejia.” a hankali ya juyar da kujeran ya zuba musu idanu, mutum ne mai tsannanin kwarjini da cikar halitta. Mutane da matukar ka kalle shi sau daya sai ka sunkuyar da kanka ƙasa. Domin yanayin zubinsa kamar zubin zaki ne, rintsa idanun Yamini yayi yana jin wani irin yanayi. Domin kallo daya yayiwa Malik ya hautsina mishi tunani, banbancin shi da Nasr Hadejia da ya kuma kallonsa ido ciki ido har sau biyu. Duk da wannan yanayin bai hana shi jin kamar ya zuru da gudu ba.
![](https://img.wattpad.com/cover/348879669-288-k328280.jpg)
YOU ARE READING
CINIKIN RAI..... beauty meet the beast
FanficMutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin sa ba a dawowa.... Silar su mutane dayawa su...