CINIKIN RAI....11
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
A yadda yake maganar ya masifar bata haushi, don haka bata san da ta daki table ɗinshi ba, sai da ya razana. Takowa tayi gabanshi ta riko necktie ɗinshi ta shiga gyara mishi a hankali tana me kara zuge mishi sai da ta shake wuyarshi. Bude baki ya fara. "lalacewar bata kai wanda zaka min barazana ba, baka isa ka min barazana ba wallahi. Kasuwanci muke da kai da kai ba bauta nake maka ba, banza irinka zaka shigo da al'umma charity House!" Ta kuma tamke wuyar. D'aga hannu sama yayi yana faɗin. "Ya isa haka, kyale ni zan gaya miki yadda zaki yi, da tausassawa. " Kara matse wuyar tayi ainun har sai da ya fara kakari ta ce mishi. "Koda wasa kada ka tab'a martabar al'umma charity House, yadda na matse wuyarka haka zan tsinke ta." Daga haka ta wuce waje. "kayi kokarin niman wacce zata maka aikin ba dai ni ba." Ware idanu yayi yana tari, ina ba zata sabu ba, Ita ce ta dace da aikinshi. Sosai abin ya d'aga mishi hankali, don haka ya nufi hanyar waje. Ko da ya fito ya samu har ta fito daga dakin sauya kaya. Zubewa yayi a kan gwiwarshi. "Allah ya ya huci zuciyarki, na tuba nabi Allah na bi ki." Ganin yadda a gaban ma'aikanta kamfanin ya iya sauke girmansa ita wace ce da ba zata hakura ba?
"Shi kenan kome ya wuce." Ta fada tana, me dauke kanta. Abin sai ya zama Gulma sosai a cikin kamfanin Chairman ya durkusa yana bawa ma'aikaciyarshi hakuri kafin kace kwabo al'amarin ya zaga ko ina har ya fada manhajar social media. Sake wasu sun yi video din abin. Haka yasa shi Mr Amjad ya dakatar da ita, kuma daman haka yana cikin shirinsu.Kwana biyu a tsakanin, Salim ya zo ya dauke ta, suka je aka mata international passport. Saboda fitarta USA.
<<<|=|>>>
Waterfall island.
Tsibiri ne da yake kan dutse, inda ruwa yake sauka izuwa babban tekun Keivroto sabuwa. Tsuni ce da babu wanda yake da ikon ya isa wurin sai ka isa ka kai, ka kuma gawurta. Yanki ne me dauke da manyan manyan jami'an tsaro ko ta kwana. Wadanda suke aiki na tsawon awa ashirin da hudu a sati. Sannan kullum sauya su ake babu wanda zai kuma dawowa, sannan wani abin da zai kuma daure kai, shi ne masu aiki a ilahirin tsibirin maza ne va mata ba, asalima babu mace ko daya.Fili ne fallau a saman dutse aka fasa shi, sannan aka mishi wani irin stone house, aka yi wani ƙasaitacciyar Mansion a tsakiyar dutsen, aka zagaye shi da wasu irin duwatsu wanda aka yi katangar da ya zagaye gidan, na musamman ne domin ba daga asalin duwatsun aka yi su ba, wasu irin duwatsu ne aka zo da shi, idan aka ce za ayi bayanin yadda gidan yake bata lokaci ne.
Malik Menk Jordan, Mansion kenan me dauke da abubuwan ban al'ajabi da mamaki. Gidan da babu wata mace da ta tab'a zama cikinsa, sannan ko a cikin gidan shirye yake da kayan alatu da more rayuwa, domin kome da yake cikin expensive ne daga ƙasashen waje. Babu abin da babu a gidan, daga masu kula da Flowers, bangaren abinci da sauransu babu wani ma'aikaci da yake permined dukkan su temperary ne, kullum sauya su ake.
Cikin gidan me dauke da dakuna shiga, kasa uku dama uku. Sai wani katon zanen hoto irin na da can, domin zana shi aka yi. Ba hoton aka dauka ba, wasu dattijai ne guda biyu. Mace da namiji sai wani yaro a tsakiyarsu. Gefe wani zane ne me Black and white. Bayansu babu wani abu na azo a gani, sai domin duk wani abin da yake cikin gidan ba bakon me karatu ba ne.A saman can harabar gidan, fili ne na tashin helicopter na daidai mutane biyu zuwa uku. Sai dan gefen can da aka ajiye expensive cars, irin wanda ake yayinsu. A ilahirin mansion akwai yar karamar drum da yake tashi irin na wasan Yara, sai dai wannan an sake shi ne, saboda tsaro da kwantar da tarzoma. Sannan akwai wasu irin tsuntsaye Eagle manya da suke shawagi a gidan, dauke da Camera a cikin gidan.
Akwai wasu manyan lion dogs da aka kewaye su, sai zuwa dare aka sake su, duk da a cikin gidan inda ake kwana akwai wani daki da aka ajiye tiger, wanda girmansa yafi na irin raguna udawa, a batun gaskiya masu kula da tsaron gidan kawai, abin tsoro ne domin tun daga tsibirin har zuwa inda aka saka iyaka da tsuburin. Domin sai an ketare ruwa kafin a iso, idan ta jirgin ruwa ne. Koda yake mutum daya ne yake amfani da jirgin Elbashir Jamal Arab, saboda kusancin shi da Malik.a bakin gabbar tsibirin akwai masu kula da ruwan suma 24/7 a cikin sati. Motoci kusan guda bakwai suka iso bakin ruwan, masu ɗauke da Shatima01 har zuwa 6, a tsakiyar motoci shida nan ya fito daga cikin wata phantom. Wacce ake bude ta ta gefe daya, rike yake da wata irin sanda, yana dogarawa sanye yake da normal shigar hausawa, kanshi dauke da zanna bukar. Wacce ta kara fito da dattijuwar fuskarshi. Amma hutu da jin dadin rayuwa yasa baka iya hango dattijantaka da take tattare da shi. Lalla Salmah ta tawo a cikin motarta a tsakiya itama, sai masu tsaron lafiyarta kasancewar ta Assamblywoman. Bude mata motar aka yi, ta fito rike da yar karamar jakar Charles Keith , sanye take da turkiyya plan gown minti colour. Hade da hularsa, sai ya tafi da jakarta da takalminshi. Murmushi yayi mata sannan ya ce mata. "Yar majalisa ya kwana biyu?" Kallonshi tayi kamar ba zata yi magana ba, kafin ta ce mishi. "Lau!" Da wani irin yake, ta dauke kanta, sannan suka nufi inda jirgin da yake jiransu, shiga cikin jirgin suka yi kowa yana jin wani abu na daban akan dan uwansa, ko da jirgin ya fara tafiya, mika musu wani karamin akwati wani jami'in tsaro yayi, suka zazzage kayansu baki daya, ya ja ya rufe suka cigaba da tafiya, koda suka tsallaka ruwan. Jami'an tsaron suka karbe su, takowa suka yi aka fara screening dinsu, bakiɗaya a duk lokacin da zasu tafi ganawa da Malik sai ayi musu screening kamar masu zuwa lahira, sun san da Elbashir ne babu me mishi wannan binciken kwafkwaf din. Babu abin da ba karbe ba, domin kuwa babu yarda a cikin lamarin Malik. Karban kome da aka yi yayiwa Lalla Salmah ciwo. Haka yayi fuska sannan suma da mitarsu ba sabon abu ba ne a wurinsu. Domin ba yau aka fara bincikar su ba, shi kan Shatima bai wani ki dar ba, ai dama ba sabon abu bane a wurinshi.
Daga nan baki ruwan mota suka shiga da zai kai su, cikin Mansion ɗin. Lokacin da suka isa kamar waɗanda suka fito sansanin cutar coronavirus, domin sai da aka musu feshi da magani sannan suka wuce shingen farko. Tsaki Lalla Salmah tayi tana dauke kanta, kafin suka isa wurin aka saka su, suka cire takalmarsu. Aka basu wasu, karshe sai da aka kai su wani daki na musamman suka sauya kayansu, sannan aka mika musu wani kati.
![](https://img.wattpad.com/cover/348879669-288-k328280.jpg)
YOU ARE READING
CINIKIN RAI..... beauty meet the beast
FanfictionMutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin sa ba a dawowa.... Silar su mutane dayawa su...