Chapter:2 Fabrication

342 27 0
                                    

BOOK ONE
002
Tsam tayi da ranta tana kallonsu, kafin ta mike tana faɗin. "Zanje nayi nazari amma yanzu kan ba zan yanke hukunci kai tsaye ba." Kallon juna suka yi, ai ba haka Mr Amjad ya gaya musu ba, ya gaya musu rauninta ne al'umma da Abbas, amma bai gaya musu cewa tana da kafiya da ra'ayinkanta ba.

Har ta fita a cikin office ɗin, babu wanda ya samu arzikin ce mata cikanki domin baki daya yanayinta ya sauya. Tana fita daga office ɗin, kiran Mr Amjad MD na kamfanin yayi ya ce masa. "Yarinyar nan bata yarda da matsayin da muka bata ba, asalima taki amsa fa, sannan nayi amfani da rauninta na gaya mata amma yarinyar taki amincewa sai tayi tunani." Ajiyar zuciya ya sauke na cikin wayar ya ce. _Ka da ka damu, haka take zan ji da kome!_ gyara zama MD yayi ya ce mishi. "Kuma dole sai ita ne? Babu wasu yan matan ne?" _Itace kawai zata mana yadda muke so, ita ce zata iya daukar wasu abubuwan, kasan me?  Ita din zamu yi amfani domin cimma manufar a yanzu gani muna tattaunawa da wasu kamfanoni amma babu alamar zasu amince, don haka ka lallabata domin zata mana amfani!

_ "ok Sir!" Ya kashe wayar da sauri ya dauki wayar landline na kamfanin yayi kirà da shi. "ku kira min yarinyar nan!"  A lokacin da kiransa ya isa office din Mss Mary da sauri ta fito ta fara niman Zeenobia.

Kiran dakin tsaro tayi ta ce musu. "Ku duba min Zeenobia ta fita ne?"  "Ok ma" kamar minti uku suka ce mata, "tana cikin elevator nan minti goma zata iso" "okay" ta nufi kofar elevator ɗin ta tsaya, sai kallon agogon hannunta take, tana jin kamar har lokacin zai wuce Zeenobia bata iso ba. Minti goma ciccib kofar yana budewa. Ajiyar zuciya ta sauke. "Zeenobia inji yallabai wai ki koma, tuntuni nake jiranki." "Amma ai mun gama magana da shi me kuma yake bukata?" "Please muje." Haka ta koma cikin elevator ɗin.
***
Daga cikin yan majalisu da suke karkashin jam'iyyar PKO, power Keivroto Own, tare da yan jam'iyyar CDL, civilian democrats labor, sai wasu manyan masu ɗauke da kamfanonin ƙasar musamman yankin Keivroto, gefe guda kuma wasu dattijai ne na musamman da suke zaune cikin shigar alfarma. Tare da wani dattijo da ya haura shekaru hamsin da wani abu a duniya. Shiru dakin ya dauka, sai kallon juna ake cikin fushi da fusata.

"Dake an mai damu sakarkaru, babu wani labari daga ɓangarensu fisabilillahi a haka za a zauna lafiya? Tuntuni Khuldu Jahid Khan yake nan zaune, a ƙalla a girmama shekarunsa taron bunkasa tattalin arzikin Keivroto zai tafi amma aka dakwafar da shi a nan, anya akwai adalci cikin lamarin ku? Nace akwai adalci? Gaskiya duk wanda ya shirya wannan taron, ya shirya taron shan shayi ne domin Malik..."

Bude kofar da aka yi yasa bakiɗaya suka mai da hankalinsu kan kofar, haka yasa shi kansa azagwaigwaidu  da yake magana yayi shiru, ajiyar zuciya wasu daga cikin mutanen da suke wurin suka dauke, cikin girmamawa suka mike. Hatta masu hayaniyar da jami'iyyar adawa ta CDL su kansu  mikewa suka yi, ban da Khuldu Jahid Khan da yake zaune fuskarsa bata yi na'am da zuwan mutumin ba, dauke kai yayi yana rike da sandar dogarawa. Dauke kai yayi yana kallon gefe har mutumin da ya shigo ya samu wuri ya zauna, sannan ya ce. "Ayi min afwa kusan dukkan mu, babu wanda zai so b'atawa wani lokaci. On be half of Khalquz Zaman muna bada hakuri."  "Yallabai Elbashir Jamal Arab mun yi hakuri, me yafi haka a gayawa Mayor muna jiransa an shirya mishi shagali na musamman." Murmusawa yayi ya ce. "Ayi hakuri Mayor ba zai samu halatta ba...." "Taya zai samu halartar taron da kowa da kafarsa zai zo? Shi kuma a keken guragu?"  Inji mutumin ɗazun da yake ta b'ab'atu. Murmushi Elbashir Jamal Arab yayi sannan ya ce. "Da alamu ba karamin shan kaye kuka yi ba, da har yau baka manta rad'd'in da ya same ku ba,  al'ummar Keivroto sun tsaya ka'in da na'in sun zabi abin da zai gina su ne, ta fuskar Kasuwancinmu, don haka abin da ya kawo mu nan shi ne, a tattauna a wuce wurin ina da trip to China!"

Zuciyar Khuldu Jahid Khan ya buga, 'ba dai wani abu Malik Menk Jordan zai kuma kullawa da gwamnatin kasar China?' wannan wani irin mutum ne? Wani irin sa'a gare shi? Dole na ga karshen Malik Menk Jordan.
"Prime minister, ka saka baki Malik Menk Jordan ya barwa wasu daga cikin yan kasuwa damar yin kayayyakinsu a kasar nan, Malik Menk Jordan bafa dan kasa ba ne; kowa yasan cewa bakon haure ne, sannan Shugabana Khuldu Jahid Khan yana da shaidun gani da idanun da suka tabbatar Malik Menk Jordan dan ta'adda ne da yake, amfani da dukiyarsa yana kashe mutane, tare da tilasta musu karban bashin da zasu kasa biya." Mutumin da aka kira da prime minister ya zubawa Elbashir Jamal Arab idanu ya ce. "Elbashir Jamal Arab ya haka? Abin da yake faruwa kenan?" Murmusawa mishi yayi sannan ya ce. "Mr prime minister dayawansu a nan, sun san Malik Menk Jordan, shima kuma yasan su, wasu kuma sun yarda da shi. Shima ya yarda da su. Malik yana da goyon bayan yan majalisu kusan 108, yana da sahalewan yan jam'iyyar PKO, sannan yana da hadin gwiwa da kwamishinonnin jahar nan, uwa Uba ta fuskar Kasuwancinmu muna da kyakkyawan alaka da wasu ƙasashen za ayi dubi da yadda garin Keivroto city yake gabbatar ruwa. Mr prime idan har aka ce za a fito da abin da suke bukata, ai Malik bai yiwa mutanen da suka yi nominations dinsa izuwa matakin Mayor ba, taya zai yarda da muradunsu bayan shima yana da tasa muradun?" Mikewa Azagwaigwaidu yayi cikin fushi ya ce. "Prime minister a sake kidayan kuri'a Yallabai Khuldu Jahid Khan ya ci ba Malik Menk Jordan ba, mutumin banza kawai, dan luwadi waye bai sani ba, kaf gidansa babu Y'a Mace, wanda kowa yasan cewa Yallabai Khuldu Jahid Khan gidansa mata uku ne, Yara mata babu wanda yasan adadinsu, ka gayawa maigidanka kar yayi asarar kwayayyensa a ta baya, ya nimo ko karuwa ce, ta haifa mishi hana gori." Gyara zaman tie dinsa Elbashir yayi ya zuba masa idanu, kafin ya ce mishi. "Na maka uzuri ni tarbiyyar Malik Menk Jordan ne, ya haramta min cin zarafin kowa."  Jin haka mutumin ya buɗe baki zai magana, Mr Khuldu Jahid Khan ya ce mishi. "kul!" Shiru yayi sannan ya cigaba da cewa. "Me yasa Malik ba zai yi show up ba?" Gyara zama Elbashir yayi ya ce mishi. "Meye matsalarka da show up dinsa, kome yana tafiya yadda yake bukata. Kasuwancinmu da siyasarmu, tow kai me kake bukata anan?"

CINIKIN RAI.....  beauty meet the beastWhere stories live. Discover now