CINIKIN RAI....17
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>Wani juya idanu tayi, ta ce mishi.
"Sai na saka shi yayi dan danasani, sai na tabbatar ya biya zunubi da ya fara dibarwa kanshi dole ma ya kira ni."
Ta fada tana mikewa, karkad'a key din motarta tayi tana wani irin murmushin gefen baki ta ce mishi.
"Bari mu gani, zai sauke girman kai ne ya nime ni, ko sai na fitar da abin da zai saka shi nima na da kafar shi."Ware idanu yayi yana faɗin. "Me kike nufi? Akwai wani abu ne?" Murmusa mishi tayi tana faɗin. "Dan luwaɗi!" A firgice ya ce mata "Ke!" Ya daka mata tsawa, yana faɗin. "Kina hauka ne? Da zaki janyo mana masifa, wallahi ki rufa mana asiri!"
Dariya ta saka tana faɗin. "Cabdijan, aikin gama ya gama sai dai kuma kada a kuma !" Ta fada tare da mike zata bar Office din,
------
A can office din Elbashir kuwa, zufa me yake karyo mishi, asalima wani azazzben tsoro ne ya kama shi, muryanshi yana rawa d kira Malik. Zubewa yayi akan gwiwarshi. "Malik don Allah ka bani izini na saka a mata yankar rago." "Hmmm!" Ya faɗa ta wayar. "Malik ka bani izini na kashe ta. Ko na saka a batar da ita, Malik ka bani izini a aikata mata kome!" "Me take bukata?" Ya tambaye shi a sanyayye, wata irin kamilalliyar murya, mara amo da hayaniya. "Wai." Inji Elbashir. "Baka tabbatar da abin da take bukata ba kenan? Bashir?" Ya tambaye shi, sake zubewa yayi akan gwiwarshi. "A'a Malik so take ta gana da kai!" Ya fada kamar ya rushe da kuka. "Shekarunta nawa?" "Yarinya ce, bata wuce 19 zuwa 20 ba" kashe wayar yayi, sai a lokacin Elbashir ya sauke ajiyar zuciya. Sako ne ya shigo wayar Elbashir. *Ka jaraba hakurinta?* Da sauri ya tura mishi. _Kusan wata guda tana bibiyar kamfanin domin ta samu gani na_
Bai kuma turo mishi da sako ba, sai dai zuwa can ya turo mishi, *a kawo ta Waterfall island sau uku muga yadda zata yi idan bata samu gani na ba, kafin nan kasa a mata barazana sau uku muga yadda karfinta yake!*_Done* ya tura mishi. Mikewa yayi yana share zufa da guntun hawayenshi da suka cika mishi idanu. "Shegiyar yarinya sai na saka an zakulo min ita" kiran wani number yayi ya ce mishi. "Maza ka zo kamfani akwai hoton wata yarinya, ku ci min Ubanta " "Yes sir!"
Bayan kamar awa biyu, wasu kartin yan maza suka tawo, "Yes gamu mun ga hotonta, sannan a bisa binciken da nayi yarinyar yar hannu ce, tasan darajar kwanji!" Cike da takaici ya ce. "Ku razana min ita!" Gyada kai yayi yana faɗin. "a gaban jama'a zamu bata tsoro! Ku muje!"
Barin kamfanin suka yi, ya turawa Malik sakon. *Na bawa su Boddi aikin firgitatta.* Yana ajiye wayar ana turo mishi sakon. _Ayi min recording din kome, idan da hali a saka musu bididdigi tracking!_ gyada kai yayi kamar yana gaban Malik.
______
Da la'asar sakaliya, ita da Yara sun fita cikin kasuwa, abaya ne a saman 3qrt din jikin. Sai riga armless kanta mayafi ta yane kanta da shi, tun da ta nufi cikin kasuwan Yara nata nuna mata abin da suke so, tana cewa. "Ku ɗauka Yarana!" Suna cikin tafiya daya daga cikin Yaran Elbashir ya bangajeta, bata wani damu ba ta ce mishi. "Sannu ko" zata wuce ya janyo ta, tare da dawo da ita gabanshi. Kallon hannunshi tayi a kafad'arta. A hankali ta juya tare da cewa.
"Kayi hakuri!" Sake dukar kafad'arta yayi, yana faɗin. "Karamar karuwa, waye Ubanki?" Fashewa da dariya Yaran suka yi, suna faɗin. "Didi koya mishi yadda ake ladbatarwa." "A'a Amir kaga Chu-chu tana jin tsoro muje na saka ku a mota!" Ta riko hannun Yaran suka juya wurin motarta, ta bude musu suka shiga, sannan ta juya tare da shiga mazauninta. Kafin su ce sun dakatar da ita ta bawa motat wani Mahaukacin wuta, a guje ta bar wurin, haka suka biyo bayanta, har zuwa Al'umma Charity House. Kafin ta isa dama ta kira Black, tana parking yana budewa Yaran kofa, suka fita da sauri. Shi kuma ya watsa mata wasu karafuna a mazaunin pasinja, da gudu ta taka motar, suka rufa mata, har zuwa filin sai da naka ko aci Ubanka.Murmushi tayi tana kallon filin babu kowa, sannan ta sauka bayan ta dauki karafunan ta saka a hannunta. A hankali ta bude motar bayan ta cire abayar jikinta, kama gashin kanta tayi ta daure shi a baya, tare da yin gammo da shi ya zauna damar, sannan ta saka ƙafarta me dauke da canvas white and pink, kalar wandonta.
![](https://img.wattpad.com/cover/348879669-288-k328280.jpg)
YOU ARE READING
CINIKIN RAI..... beauty meet the beast
Hayran KurguMutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin sa ba a dawowa.... Silar su mutane dayawa su...