*3&4*
K'aramar hukumar Toro tana cikin k'ananun hukumomin jahar Bauchi. Duk wani mai nazari yasan yadda Ubangiji ya wadata Toro da girman k'asa.
Ita ce k'aramar hukuma mafi girma a dukkan fa'din tarayyar Nigeria dama Africa ta yamma gaba'daya.
Garin Toro an kasa shi zuwa Gundumomi uku.
Gundumar Toro, gundumar Jama'a da gundumar Lame.
Sannan akwai kabilu daban daban bayan Hausawa da Fulani.
A karkashin jahar Bauchi ta ke amma tafi makwbataka da jihar Filato.
Shi yasa garin kewaye yake da ni'imomin kayan itatuwa da rashin zafin rana sosai.
Ba dan ina y'ar garin ba, Ubangiji ya dabaibaye garin Toro da tarin faloli Alhamdulillah.
Dare ne amma ba ainun ba, mafi yawa mun ha'du a kofar Kakarmu Dada ana ta hira da tatsuniya. Kannenmu kuma sai wasan d'an dunmi suke yi.
Dukkanmu y'anmata mu bakwai da muke kai d'aya muna zaune akan tabarma, idan aka dauke shalele Nasiba da take kishingi'de a jikin Dada.
Sannu a hankali Dada take taunar goron bakinta tana mulmulawa.
Kyakkawar dattijuwa mai kyakkawan jiki. Asalin Bafulatanar Lame ce, kowa kuma yasan asalin mutanan wannan garin fulanin Mali ne da kiwo ya saka suka tsallako Nigeria suka yi sansani a yankin na Lame.
Wani ikon Allah mafi yawa na ahalinta sun samu kyawun halittar fulanin Lame.
Haka muke y'an gidanmu son kowa k'in wanda ya rasa.
Wani irin kallo take mana na kurillah.
Ta kasa ha'kuri ta ce "Na fa'da muku dukkanku ku zauna cikin shirin ko ta kwana.
Domin kuwa ba zaku fi haka gandare wa a gabanmu ba.
Dukkanku abubuwa sun cika muku k'irji. Ko wacce a cikin ku wanki take yi a gabanmu, ina kallon zamani ni Binta! Muna cikin alhini. Allah yasa intingifarin da muke nacin yi mun samu rabauta ana karban sallarmu".
Dariya ta kama mafi yawanmu.
Ni da nake da kaud'i na ce "Dada Ashe ba'a karban sallarku ne?"
Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Ai matu'kar kana da yarinyar da ka yi saken da ta fa'di a gabanka, to kuwa babu makawa sallarka bata isa gaban zati, daga bakin k'ofa ake dakatar da ita!"
Nasiba ta ce "Allah ya kawo mafita. Yanzu biya mana karatun na yau".
Nan da nan ta furzar da goron bakinta dan girmama karatun da zata d'ora mana.
Ta tsume ta ce "Mu karanto na jiya".
Muka ha'da baki wurin rera karatu cikin sigar wake muka ce "Idan attishawa ta sauko mana, idan wani bawa a kusa da mu ya ce mana "Rai ya hadu da Gafarar Allah!"
Sai mai attishawa ya ce "Ya-hadi kumalle.
Idan kuwa zamu ci adda'ami.
Zamu fara da ambaton Allah. Idan koshi ya zo mana sai mu ce "Sawaba ta sauka akan me nemo wa da mai dafa wa".
Dada ta murmusa tabbacin ta gamsu mun ri'ke karatun nata da kyau.
Ta ce "Madallah!". Cikin alfaharin muna da fikirar fahimtar karatun da take yi mana.
Ta muskuta ta ce "yau karatun yiwa kai rigakafi daga shaidanu da makarai zan dora muku".
Muka ha'da baki wajen fa'din "Mun gode Dadarmu, Allah ya kara miki nasibi.
Annabi yasan da ke".
Ta numfasa ta ce "Ameen, a kuma tsananta yi mini rokon dacewa da shiga cikin masoyan SHEHU".
Na kasa jure wa na ce "Ashe Dada ba zaki bar zancen Shehu ba?
Kowa ya bar Allah da ma'aiki ai ya bar hanyar tsira."
Nan da Nan ta fusata ta ce "kaico da Yabi! Yabi ba zaki tsira ba, waya yake inkari da jikan Manzo? Tabbas sai gafalalle".
Na ci je na sake ce wa, Annabi dai aka ce mu ri'ke ba waninsa ba Dada, iyalan gidansa suna da girma da hakkin mu so su mu kare mutuncinsu.
Amma ba'a ce a kai su wani bigire da zai iya zama halaka ba.
Da kansa ya ce "Zan bar muku kura'ani da sunnata wato (Hadisansa) idan kuka bisu kun tsira.
Amma ku kun shure komai, kun dauko shehu kuna neman mayar da shi abin bauta?".
Ai kuwa ta sake harzuka ta ce "Wahalar rayuwa akan ki Yabi! Mai gadon taurin rai da kafiya, kaicon ki, kaicon ki! Da yi mini izgilanci Asiya".
Jikina ya sabe da rawa a dalilin ba irin jan kunnena da Gwaggo bata yi mini ba, akan kada na sake na janyo abin da Dada zata dinga yi mini mugun fata. Ga shi ban ji ba, na yi sanadin da take fatan na dauwama cikin wahalar rayuwa.
Kafin na ce komai sai ga Tijjani wanda mafi yawa an fi k'iransa da sunan garinsu Bulkachuwa.
Wani irin zabgegen saurayi.
Dogon gaske har d'an rankwafa wa ya yi ka'dan.
Fari ne tas, irin fulanin Bulkachuwa, a murde yake, shi ba siriri ba, kuma ko ka'dan baya cikin masu kiba.
Ga dogon hanci da ya k'awata doguwar fuskarsa.
Baya ga hakan manyan idanuwansa ka'dai sun isa abin burge wa.
Ban ta'ba ganin namiji mai jajayen lebe ba sai Tijjani kyakkawan gaske.
Wani irin mutum mai saurin fishi, da k'arfin zuciya.
Amma mai saurin saukowa da mantuwa.
Illarsa d'aya manemin mata ne, a yadda a ke fa'da. Na shaida kuma duk wata budurwa ballagaza a Toro to kuwa budurwarsa ce ko kuma suna d'asa wa, shiyasa kowa yake jan kunnen y'arsa a kansa, barin ma ni, kullum ne sai Gwaggo ta ce kada na sake na bashi fuskar da zamu dinga doguwar magana.
Gaba'daya dabi'unsa na tantiran yan-iska ne, sannan k'azami ne, baya damuwa da yin wanki sai kayansa sun k'are.
A hakan kuma shashan y'anmata suke sonsa, ko da yake baya yarda ya fita da dattin sosai, yana wanke wa ya jira su bushe, guga ce sai ya samu ku'di, sai ya bayar da kayan ma a wanko a gogo masa, amma da wahalar gaske ya yi guga da kansa.
Duk yadda Dada take kulafacinsa, matu'kar ya shigo muna nan sai sun haura da shi, domin yafi kowa takalarmu da magana, yana yi yana lumshe ido ta yadda zai sure zuciyoyinmu.
A hakan ya yi nasarar yin wuf da zuciyar Nasiba.
Idan Dada ta ga yana sakin maganganu ko lumshe ido a gabanmu ta dinga bagarar da shi, ko ta tsiri aiken sa, ko kuma ta ce mu je ta sallame mu, duk yadda take sonsa to bata son doguwar magana a tsakaninmu, kazalika kuma bata son a k'i gaishe shi.
Burgar da yake yiwa mata ya sanya har yanzu bai bar dauke dauke ba, komai ya gani zai dauka ya siyar ya kashe wa budurwa ku'di. Amma iya kayan Dada yake dauka.
A duk sadda take yi masa fa'da kuma zai waske ya ce bashi ba ne, ko kuma sharri ta yi masa, haka kuma sai ya d'auke mata wuta, har sai ta nemo shi ta bashi ha'kuri. Bayan soyayyar da take yi masa, yana sake samun alfarma a wajenta saboda sunan SHEHU ne da shi.
Kullum bakin ta akan ya nutsu ne, ya bar shiririta ya kawo matar aure, tunda ga Yaya Salisu nan da yake sa'an sa tuni ya yi aurensa har matar ta haihu, amma shi ko maganar aure baya yi saboda sharholiya da mutuwar zuciya.
Duk da k'arancin shekaruna ina tambayar kaina ko waye zai iya d'aukar y'arsa ya bawa Bulkachuwa aurenta?
Tabbas sai idan yarinyar ta kasance shasha ce irinsa.
Na tabbatar mahaifiyar Nasiba ba zata ta'ba bari a bashi ita ba, domin kuwa kowa nasa yake so, bare idan maganar gaskiya za'a yi bai cancanci a bashi ba, domin bashi da sana'a, gashi manemin mata, shiyasa kowa yake masa kallon shasha.
A duk sadda Dada take yi masa fa'dan shigar da yake yi ta gajerun wanduna yana yawo a gari babu kunya, ko tara suma ya gegareta daga gefe, ko kuma wani zubin ya sauya launinta bayan ya mayar da ita cibiri cibiri.
"Akan kunnena na sha jin tana ce wa "Saboda bamu da mutunci a idonka shiyasa kake iya zuwa gabana a hakan ko kuma gaban kawunanka".
Ba jin nauyi yake ce wa "Tunda nake yin sallah a hakan, ai kin ga bai zama aibu dan kun gan ni a hakan ba. Domin Ubangijina ma a hakan yake gani na, kin takura mini fa Tsohuwa"
Nan da nan ta zabura ta ce
"Imaninika ai a makogaro yake shi yasa kake hakan, amma da za'a jarrabe ka da son wata yarinyar ba zaka yarda ka je mata a hakan ba. Alfarmar Shehu sai ka samu wacce sonta zai hanaka yin wannan shakiyancin. Tunda ka ki daina wa saboda Allah da Ma'aikinsa."
Dariyar iyashege yake yi ya ce "Ni da nake da y'anmata kamar jamfa a Jos suna bina dan na so su, shine har son wata zai canja ni?
Lah! Ba dai Bulkachuwa ba".
Da wani kuma a Cikinmu ko a cikin samarin gidan matu'kar ba Yaya Anwar ba ne zai saka musu baki, a take Dada zata nuna wa mutum shine bare a tsakaninsu.
Tana kuma sake kambaba shi da kawar masa da kai saboda alfarmar mai sunansa ne, domin ko ta yi masa sababi, sai ta yi ta tuba tana kamun kafa da mai asalin sunan akan a saka mata jikanta cikin shirayayyu. Hatta shi kansa dariya take bashi akan yadda take tuba idan ta saki harshe a kansa.
Amma wani ikon Allah jarumi ne na gaske.
Idan na ce jarumi ina nufin zai tsaya ya fafata da kowa akan hakkinsa, matu'kar kuma ya sanya kansa zai yi abu, to duk tsananin wahalar abin sai ya ga abin da ya turewa buzu nad'i.
Baya ga hakan kuma tausayi ne da shi, duk zafinsa inda zai ga kana kuka to zaka ga ya bar yi maka tijara.
Sai dai kallon marowa ci nake yi masa na gaske, ni dai ban ta'ba ganin ya yi kyauta ba.
Ko garinsu ya je ya dawo, duk abin da zai samo ba dai ya kawo gidanmu ba. Amma kullum a cikin karbe wa jama'a nasu yake, mussaman Dada da ko ta hana shi a k'arshe take kasa juriyar ganinsa cikin rashin sukuni, sai kawai ta bashi.
Mazan gidan kuwa basa bashi duk irin yadda zai karyar da kai yana fa'din bashi da lafiya, tunda suka gane matu'kar ku'di ya shiga hannunsa y'anmata banza yake kashe wa, sai kowa ya kulle bakin aljihunsa dama kuma masu k'aramar niyya ne. Sai dai gara shi ma suna bashi, amma da a ce wani ne cikin y'an k'ofarmu baza su bayar ba, daman kuma bamu isa mu ce a bamu ba.
Haziki ne na sosai, kwarai da gaske yake ja, amma lalacewar da ya yi ya sanya da k'yar ya iya kammala Diploma a kwalejin Tatari Ali data ke cikin Bauchi.
Ya riga su Yaya Salisu samun gurbin karatu a jami'ar amma yak'i mayar da hankalinsa akan karatun har sai da aka kore shi. Hankalin mahaifinsa ya yi tashin gauron zabi, domin zaryar da ya dinga yi tsakanin Bulkachuwa zuwa Toro ba ka'dan ba ce.
Haka ya sake samo masa yin diploma akan shaanin tsaro da tafiyar da gwamnati wanda da k'yar ya kammala dan ma shekaru biyu ne.
A hakan kuma sakamakon ya yi kyau, domin ya wuce fallasa. Duk da hakan Babansu bai bar shi ba, sai da ya sake samo masa gurbin karatun digiri a jamiar jahar Bauchi ta garin Itas-gad'au. Inda zai karanci ilimin halayyar dan Adam. Wannan kam da taimkon Ubangiji ya kammala domin ba ya zuwa sai an kusa fara jarrabawa, sannan bai fasa al'amari da y'an mata ba.
Shekaru biyu da rasuwar mahaifinsa kenan. A kuma wannan shekarar ya tafi bautar k'asa, da shekara ta dawo ya kammala. Yanzu zaman kashe wando kawai yake yi. Sai dai yana yar buga bugarsa domin kusan kullum sai ya je Bauchi.
Haka ya dinga satar jiki yana siyar da kadarorin da ya mallaka. Abin kaico kuma ba komai ya yi da kudin ba sai sharholiya da burga a mata.
Wani k'aton fili a Bauchi kawai ya tsira da shi, shima dan an zuba masa matakan tsaro ne.
Yau da wata sana'a yake da ku'din ko kuma wani gini yake fa'da'da wa da an samu sau'kin bacin ran da ake ciki.
Ya zauna kusa da Nazira da take kusa da karshen tabarmar.
Murya ba amo ya ce "Madallah da Dada da y'anmatantanta".
Duk suka hau rige rigen gaishe shi Amma ban da ni.
Ya amsa hankalinsa na kaina.
Ya kasa ha'kuri ya ce "Asiya Toro how far?".
Na yi banza da shi.
Domin dai na tsani yadda yake gatsa ainihin sunana, dan kuturun wula'kanci har sai ya ha'da da Toro.
Kusan kowa Yaya Bulkachuwa yake ce masa, ni da bama shiri bana ce masa Yaya Bulkachuwa.
Amma sai nake mutuntunta shi wajen kiransa da Yaya Tijjani amma bai yaba ba, bare ya gode. Yabin da zai ce ne yake ganin asara saboda an cika zuciyarsa da k'yashi. Shi yasa nima na janye yayan tuntuni nake gatsa Tijjani gatsal wanda na lura shi ko oho.
Ina nan, ina kallon wadanda basa ce mini Yabi, duk ranar da Ubangiji ya sanya na je Saudi akan girma da hankalina ko tsarabar abin da ba'a so ba zan basu ba.
Tijjani na cikin sahun farko.
Yaya Ummi ce mutumiyarsa, baya zuwa gidan kowa amma yana zuwa gidanta, har idan da ku'di a tare da shi ya yi wa ya'yanta alheri. Sosai suke d'asawa, mutimiyarsa ce ta sosai.
Dada ta fusata ta ce "Mugun nufi ya k'are miki Yabi! Ko wacce ta gaishe da dan-uwanku amma ban da ke, bai yi fishin wula'kanta shi da kika yi ba, ya sake bu'de baki ya yi miki magana amma kina ji sarai kin k'yale shi, saboda ke din kina gaji nunkufurci da ba'kin hali ko?"
Raina ya baci domin a kullum kalaman Dada a kaina kenan, bansan me Goggo ta tsare mata da a kullum sai ta jingina mata munafurci da ba'kin hali ba, ko da yake na taba jin labarin cewar tun haihuwar Yaya Ummi da dangin Goggo suka zo suna daga garinsu na Kangire cikin k'aramar hukumar Birin Kudu suka fuskanci wulakanci daga wajen Mama. Shikenan duk haihuwar da take yi basu sake yin gayya sun zo ba.
Sai dai a samu mutum biyu su zo su ganta washagari su juya sassafe.
Wannan matakin da suka dauka shine ya zama laifin da yak'i wuce wa a wajen Dada da take ta musguna mata da gorin ba y'ar babbar haula ba ce, sannan yan'uwanta masu k'ullaci ne, duk kuma cikin matan gidan mahaifiyarmu ce kawai bata da kowa a garin Toro shi yasa ma wani abin ake yi mata da gan gan.
Duk da ba jin dadin zaman take yi ba, ta jure dukkan kalubale dan kawai ta zauna da mu yaranta, amma bata tsira ba tunda Babanmu ma haka siddan sai ya dauke mata wuta na tsawon lokaci mai yawa. Mama kuwa bata fasa yi mata yankan baya a duk inda ta zauna ko ta samu damar yin hakan ba.
Ko yaushe Gwaggo a cikin mutuntunta Dada take hatta wankin kayanta har yau bata daina yi mata ba, amma babu gwaninta bare yabawa.
Nan da nan na tunzura na ce "Da yake shi kina jin tsoron kada ya keta ki shiyasa kike fa'din hakan. Amma ni kin bu'de baki kina niyyar tozarta ni.
Tunda ban gaishe shi ba, ya yi mini magana ban amsa ba, ba sai ya rabu da ni ba?
Bana son harka da shi ne, a duniya na tsani sunan da yake kirana da shi. Sannan idan zai mini magana sai ya lanjare murya, kuma kinsan dai ba sosai nake ji ba, bare na ji shi da kyau".
K'wafa ta yi tare da cewa "Kowa ya yi na gari ai dan kansa Yabi".
Basira ta ce "Yi ha'kuri Dada d'ora mana karatun kawai".
Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Kayya Basira zuciyata ta jagula ainun karatun nan sai gobe kuma".
Firdausi ta ce "Yaya Bulkachuwa saka baki Dada ta d'ora mana karatun, bata ha'kuri mana".
Ya kalle ta ya ce "Dadarmu share kawai, nima na ha'kura ai. Kinsan hankalin Asiyan Toro a k'auri yake".
Na sake hauro wa na ce "Tijjani ka bari, ka ga dai bana shiga harkarka akan me zaka nemi takure ni ne? Gaskiya bana son haka".
Dada ta sake yin k'wafa tare da cewa "Yabi kin janyo muku, domin na lura tashen balaga kike ji, zan kuwa yi maganinki."
Kafin wani ya yi magana sai ga Ikilima k'anwata da a yanzu take shekaru tara.
Ta shigo cikin nutsuwa ta kalle ni ta ce "Adda Yabi ki zo".
Da azama na mike domin nasan Yaya Jabir ne.
Saurayin da yake gigita zuciyata da ruhina.
Ban ce komai ba, na mike ina cewa "Sai da safenku".
Dada ta bimu da ido tana cewa "Jabiru ne ko kuwa wani ne?"
Ban kula ba, ba kuma wacce ta tanka.
Domin dai na fi su farin jinin mane ma duk kuwa da ba finsu kyau na yi ba, asalima wasu sun fini kyau, sun kuma fini cikar mace.
A bakin kofar Shashenmu ya jingina.
Matashin saurayi mai cike da nutsuwa da kamala.
Wankan tarwada ne, siriri mai matsakaicin tsayi, mai sanyi a halayya da kuma dabi'a.
Bashi da kwaramniya tun tashinmu, mai hakuri ne na gaske, da wahalar gaske ka ga fa'dan Yaya Jabir.
Sosai muke shiri da shi, duk kuwa da ni din mai tsiwa ce, mai kuma hayaniya ce.
Amma jininmu ya ha'du sosai.
Kusan tun soyayyar kuruciya ce ta rikide ta zama ta gaske.
Dalibi ne a jami'ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Ajinsa uku sawess yake yi a cikin Jos.
Sannan ya yi sa'a ma'aikaci ne a karamar hukuma da aka dauke shi aiki da sakandire a lokacin kawunsa kanin mahaifiyarsa kansila ne a yankin gundumar Toro.
Na isa gare shi, yana sanye cikin farin yadi fari k'al.
Wato duk samarin gidanmu babu mai tsabtar Yaya J.
Ina jin da'din k'iransa da Yaya J. Na lura shima ba karamin son sunan yake yi ba. Ni ka'dai ce nake fa'da masa hakan kuma.
Kusan halayyarmu daya ni da shi, domin nima tsabta ce da ni, har fa'di ake yi aljanun tsabta ne da ni. Baya ga haka muna da son y'anuwanmu, bama jin k'yashi wajen salwantar da duk abi da yake namu ne akan d'an-uwanmu, har rashin girman jikinmu iri d'aya ne.
Shine d'a na farko a bangaren Baban Tsakiya.
Mutane da yawa suna fa'din kama muke yi ni da shi, ni kuma bana ganin kamar kawia dai yanayinmu ne daya tunda shi din ba wani girma ne da shi ba, haka yake dan madaidaici avarage height ne.
Haka nima duk cikin y'anmatan da muka taso ko wacce ta fini tsayi, bani da tsayi, nafi kusa da gajerta.
Ina da gashi sosai, sannan ina da manyan idanuwa baya ga hakan fara ce sosai.
Yadda nake yar cif cif sai nake matu'kar daukar hankalin mutane.
Kullum idan zan fita sai Gwaggo ta ce ban da wulakanci Yabi, domin al'adar gidanmu ne yarinya bata kammala karatun sakandire.
Shekaru sha biyar ake aurar wa, amma mu da alamu za'a bari mu kammala duk da dai Dada ta fara fa'din mu shirya dama kuma ita ce take matsa lambar sai an yi aure.
Ya zuba mini ido babu walwala jikina ya yi sanyi na yi kasa da kaina ina fa'din "wannan kallon tuhumar fa Yaya J?"
Ya saki gauron numfashi ya ce "kin kama kanki da kanki Yabi. Jiya ma fa sai da kuka tsaya da yaron nan dan gidan Sarkin k'ofa ko?".
Na yi murmushi na ce "Ai dai baka ji me na ce masa ba".
Na fa'da cikin shagwaba shagwaba.
Ya sake yin kasa da murya ya ce "Ban ji ba, amma yanzu fa'da mini na ji".
Na yi k'asa da kaina na ce "Na fa'da masa cewar ni bana sonsa akwai wani bawan Allan da ya riga shi yin wuf da zuciyar Yabin Marina".
Ina kallonsa ya dan murmusa ya ce "Waye wannan bawan Allan?"
Na dago amma ban kalle shi ba a dalilin hasken kwai na kanmu.
Na juyar da fuska na ce "Yaya J mana".
A wannan karon murmushi mai sauti ya yi.
Ya nisa ya ce "Yauwa Yabin J, kin biya ni.
Amma idan kina son ki burge ni, ki daina ma sauraronsa ba shi kawai ba, kowanne namiji ma.
Sannan ki daina fa'da dazu ma sai da kika yi dambe da Saratu.
Kin ta'ba gani na ina dambe?"
Na girgiza kai tare da cewa "Ha'kuri ne ya yi maka yawa, ni kuwa bani da shi, domin duk wacce ta ta'ba ni ba zan k'yale ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ha'kuri fa falala ne da shi Yabi".
Na girgiza kai na ce "To ka dinga yi mini addu'a na shiga sahun masu ha'kurin domin kuwa ni duk wanda ya ta'ba ni idan ban rama ba sai nake ganin na zama sullutu".
Ya murmusa sosai domin ba mai dabi'ar k'yal-k'yala dariya ba ne.
Ya zuba mini ido ya ce "Wai Goggo ce ta haife ki, al'amarin Ubangiji da girma yake.
Waton idan kika rama baki zama sullutu ba?".
Da hanzari na ce "Ras Yaya J domin dai kai din shaida ne na yadda ake kaffa kaffa da ni, da duk kayana".
Ya zuba mini ido ya ce "Allah ka sanyawa Yabi ha'kuri da juriya, a mayar mini ita ta zama mai shanye dukkan kalubale da ha'kuri da kuma kawaici".
Na ce "Gaskiya Yaya J kada mu yi haka da kai, roka mini na zama yar gwagwarmaya mana, sai kawai ka roka mini na zama mai ha'kuri komai aka yi mini sai dai na yi kuka, ko ya yi ta cina a zuciyata, watarana sai dai kawai a budi ido aga Yabi ta ha'du da jinya ko ta mace ma gaba'daya. To ni ba zan zama hakan ba".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kinsan darajar ha'kuri kuwa Asiya?"
Na kalle shi domin bai cika fa'din zahirin sunana ba, tunda ya fahimci ina son inkiyata ta Yabi shikenan ya wajabta ma kansa fa'da mini duk da dai yafi son Asiya.
Domin an sha dakuwa da ni akan ce mini Asiya, ina ganin duk wanda ba zai ce mini Yabi ba, to hassada yake yi mini, tunda an yi dawafi da ni a ciki, an yi tsayuwar arfa da ni, an yi jifa da ni, an yi sa'ayi da ni to mene ne na tauye mini Hajjin?"
Ban bashi amsa ba ya ce " wanda Ubangiji ya masa baiwar ha'kuri to ina tabbatar miki an ba shi arzikin duniya da lahira, ba kuma abin da ba zai cimma ba a rayuwarsa, daure ki zama jaruma amma ba jarumtar rashin ha'kuri ba".
Na girgiza kai ina murmushi domin dai ban gamsu ba.
Har yau da na fara mallakar hankalina ban ga ribar ha'kurin da mahaifiyata take yi ba.
Ban ga ribar kawaici da ha'kurin da mahaifinmu yake yiwa zumunci ba.
Ban ga ribar ha'kurin da Yaya Ummi take da mijinta da uwargidanta ba.
Tunda har yau ita ce a wahale, kuskure ka'dan zata yi ya mata tijara a tsakar gida a gaban kowa tamkar ba ita ce mai k'uruciya ba.
Dan haka na k'udire a raina ba wanda zai nemi ta'ba ni, na k'yale shi, zan yi komai dan na tabbatar ban bari na zama gajeriyar katanga mai da'din k'etara ba.
Yanayina ya tabbatar masa ban yarda zan iya yin hakan ba.
Ya girgiza kai ya ce "Ai shikenan sai dai zan cigaba da yi miki addu'ar dace wa da babban arzikin duniya wato Ha'kuri".
Na yi dariya na ce "Dama addu'ar na zama hamshakiyar y'ar kasuwa kake yi mini, ta yadda kasuwacina zai d'auke mini hankali daga dukkan wani rashin ha'kurina da kake ga ni".
Da sauri ya ce "Ina yi miki Yabina! Da ikon Ubangiji komai kika kasa sai kin sayar, kullum sai na roka miki Ubangiji ya baki dauwamammiyar sana'a da zaki tsufa kina cin gajiyarta".
Da'di ya kama ni, domin Yaya J ne kawai ya fahimci irin yadda nake son na zama shahararrriyar y'ar kasuwa.
Ya miko mini tsarabar Jos leda biyu da ya ajiye a bayan k'yauren shiga shashinmu.
Na karb'a ina godiya sosai.
Na tabbatar Atile ce da kuma turare, tunda sune abu mafi soyuwa a mini kyautarsu.
Fahimtar hakan da ya yi, sai ya dimanci yi mini tsarabarsu.
Shine ya fara koya mini amfani da turaren Far-away.
Daga haka muka yi sallamah.
Kai tsaye dakin uwata na nufa ban koma wajen Dada ba.Tallah
Kayan chadi a sauwake.
Akwia ingantattun kayan gyara ma chadi.
Saiwowin dahuwar kaza
Saiwowin maganin sanyi sadidan
Hadaddun daka.
Gumba
Tsumi
Y'aya'n gadali
Da sauran kaya na alfarma da basu da illah.
A hannuna zaku samu cikin farashi mai sauki.What'sapp no
08032773332.✍️
YOU ARE READING
BAKAR TA'ADA
General FictionMurya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina". Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito...