5&6.
*Dandano*.
A zaune na tarar da ita tana kullin siga, da yake tana auno rabin kwano tana k'ullawa, idan an zo siyan koko ana siya.
Ikilima tana gefenta tana faman barci.
Na ajiye ledar a gabanta.
Ta kalle ni ta ce "Yabi na sha fa'da miki, jikina na bani sha'aninku da Jabiru ba mai yiwuwa ba ne, ba sa'an auren ki ba ne, gara ki tsaya akan Abdulrashid zai fi mana sau'ki da kwanciyar hankali".
Na yi shiru, amma zuciyata sai tsalle take yi.
Babban tashin hankalina a duniya shine Gwaggo ta ce mini aurena da Yaya J ba zai yiwu ba.
Na yi k'asa da kaina a hankali na ce "Gwaggo fa'da mini dame ya fini da kike ganin yafi k'arfina?"
Ta murmusa ka'dan ta ce "Saboda Babanki ba shi da arziki, sun tsere mana, sannan uwarsa tana da buri a kansa, bayan haka ga Mama k'ut take da uwarsa, dan haka zata yi dukkan mai yiwuwa ta sake b'ata lamarin tunda akwai haske a tare da shi, ba zata so wannan hasken a tare da ke ba.
Sanin kanki ne kuma mutanen gidan nan baza su dauke ki su ba shi ba, tunda kuna da yawa, zasu yi kwarya tabi kwarya ne a tsakani.
Da ace ke din diyar Baban kasuwa ce to, da ba fargabar da zan yi".
Na numfasa k'irjina ya daure ainun.
Na dinga tambayar kaina shin zan iya rabuwa da Yaya J?
Da gaske har lalacewar zumunci ya kai za a iya hanamu aure ba tare da wani dalili gamshasshe ba?
Ashe har za'a iya ture karfin jini saboda kawai dan-uwanka ba shi da wadatar abin duniya?
Na sauke nannauyan numfashi na ce "Ki daina damuwa Gwaggo! Ban tsananta ba, ban kuma dage sai shi ba.
Ki cigaba da yi mini addu'a".
Ta sake kafe ni da ido ta ce " Ina yi miki addu'a sosai Yabi, amma zata yi tasiri ka'dai idan kin barwa Allah ya yi miki zabi, kin kuma yak'i zuciyarki akan Jabiru. Ina nufin ki rage zurfafa a al'amariinsa."
A sanyaye na ce "To Gwaggo".
Sai kuma na zauna ina taya ta k'ulla sigan ina bata labarin yadda ta kaya a tsakanina da Dada.
Ta nisa ta ce "Ba kya jin magana ne, ban da hakan mene ne zaki dinga janyo wa tana yi miki mugun fata?
Kinsan kuwa bakinta zai kama ki domin ita ma uwa ce a wajen ki".
Jikina ya sake yin sanyi, na dinga yin addu'ar Allah yasa na daina tanka mata akan Shehu tunda mafi yawa saboda hakan take fusata.
Ta ke tsanata mini, har take yi mini
mummunar addu'a.
Washagari takwas saura muka d'unguma zuwa makarantarmu ta jeka ka dawo ta gwamnatin jahar Bauchi.
Ajin mu hudu wato ss1.
Ko wacce tana cikin tsafta, duk inda muka wuce sai an kallemu wataran akan kunnenmu mu ke jiyo yadda ake fadin "y'an Marina ne, kasan yawa ne dasu tamkar tsaki."
Ko muji an ce "kai wato gidan Marina akwai zuka zukan zaratan y'anmata fa."
Muna tafe ina tambayar Basira da Nazira jiya Dada ta d'ora musu karatun kuwa bayan na tafi?.
Nasiba ta ce "Bayan kin bata mata rai yaushe zata iya yin karatu? Kin san kullum sai ta ce haramun ne yin karatun addini a cikin fishi ko a cikin rashin tsarki".
Muka k'yal-k'yalale da dariya gaba'daya.
Muka isa makaranta hatta Malamai kwarjini muke yi musu saboda yawanmu da kuma yadda muke kama da juna baya ga hakan tare ake ganinmu tamkar kashin awaki alhalin a gidajenmu babu wannan soyayyar da jin kai da ake gani a tare da mu.
Lokacin tashi yayi muka dawo a jiga ce a dalilin rana ake yi duk da zafin ranarmu da sau'ki akan ta Bauchi da Jigawa.
Wajibi ne idan zamu tafi sai mun shiga mun gaida Dada, haka nan idan mun dawo.
Tsabar saka ido da kwakkafin baiwar Allan nan duk wacce bata je ba sai ta ga ne, hakan kuma na iya zama sanadin rikici a gidan, domin bai zame mata komai ba, ta kira uwar yarinya ta yi mata tass, ta ce da sa hannunta y'arta ta raina ta.
Kuma abin mamakin idan baka kama sunanta ba, to da kai da wacce bata je ba daidai kuke.
Ina tsaye suka dinga shiga suna fitobwa ba abin da ake ji sai "Dada mun dawo, sannu da gida" .
Yayin da ita kuma take kama sunan kowa tana cewa "Sannunku da dawowa, lale da y'anmata Dada".
Sanin da na yi garina da tsakuwa da ita, ya sanya nake jingirta wa sai na je gabanta sosai ta yadda zata shaida ni da kyau.
Tunda kullum sai na je, amma idan ta so ci mana mutunci ni da Gwaggo sai ta ce ban je ba, ko kuma na yi mata gaisuwar gadara da wulakanci daga bakin k'ofa
Dan haka da na k'ara wayo sai nake isa gabanta mu hada ido sosai sannan na yi gaisuwar.
A gajiye na k'arisa k'ofarmu na tarar da bacin rai domin tsagwaya na tarar an yi a matsayin abincin rana, wani irin nau'in abinci ne da ake sirfa dawa sai a dafa a ci da manja.
Na tsani abincin ba dan babu da'di ba, sai dan kawai bana so.
Na zauna a tsakar d'akin Gwaggo ina kunci sosai.
Ta shigo ta kalle ni ta ce "ban ga kin cire inifom din naki, kin yi sallah kin zuba abinci ba?"
Na tumbatsa da fishi ban tanka ba.
Ta kafe ni da ido ta ce "Yabi kullum aka yi tsagwaya sai kin tayar mini da hankali? Sanin kan ki ne mahaifinku ya saka takunkunmin siyo abinci a waje ko a ro'ko a wani waje. Me yasa ba zaki rufe ido ki ci dan ta yi miki maganin yunwa ba?
Idan kin yi ha'kuri ai wataran barin gidan zaki yi, ranar da Allah ya kai ki dakinki komai kike so sai ki yi wanda bai wuce wadatar mijinki ba".
Cikin bacin rai na ce "Ki taimake ni ki bar ni na jika gari na sha, Allah ya sani yunwa nake ji kamar na mutu".
A sanyaye ta ce "To ki jika amma nafi son ki dinga ci tunda idan kin ci din ba illah take miki ba."
Haka na jika gari na bu'de jakar makaranta na dauko gyada maro na bushe na zuba, ina sha, ina fa'din "ba dan na k'osa ba, da Iklima ta siyo mini madara, to aikenta bana me sauri bane ko wanda yake a matse irina, domin shad'arta ta yi yawa".
Gwaggo ta girgiza kai ta ce "Ke dai duk salon k'wadayi kin san shi, ki dinga bin duniya a sannu sannu Yabi".
Na yi dariya na ce "Gwaggo tuni aka daina bin duniya a sannu. Saboda gaggawar mutanen cikinta ba zasu bar mai binta a sannu ya kai ga gaci ba, yanzu da nake yin kitso na ha'da da lalle ba gashi muna d'an samun taro da k'wabo ba, da sannu nake bi iya kitson kawai zan yi Gwaggo. Yanzun ma so nake na koyi wata sana'ar na sake ha'da wa domin ina da burin na samu ku'di masu nauyi na jiyar da ke da'di, na jiyar da su Iklima".
Ta girgiza kai ta murmusa ta ce "Na gode sosai Yabina! Allah ya ida nufi, amma dai ki bi a sannu da ikon Ubangiji komai zai saukaka a gareki, kullum sai na rokar muku kada a jarrabe ku da rashin abincin a gidan aurenku kamar yadda aka jarrabi Yayarku, ita ma ina fatan da'di ya biyo bayan wannan wahalar da take ciki".
A sanyaye na ce "Allah ya amsa bakinki Gwaggo".
Ina kammala wa na yi haramar sallar azahar, sannan na shiga wanka dan shirin tafiya Islamiya.
Dai-dai lokacin Babanmu ya dawo daga wajen sana'arsa.
Gwaggo ce mai girki ta hau hidimar kai masa abinci, a raina sai kiyastawa nake yi ina ma ina da hali na dinga soya masa miya mai d'auke da naman kaji ko na shanu zuk'u zuk'u a ciki. Din ya dinga ci da abinci.
Na fito na gan shi zaune a rumfa akan tabarma jikinsa duk ya yi futu futu, ga alamun gajiya mai yawa a tare da shi.
Tausayinsa ya tsirga mini, cikin rauni na ce "Sannu Baba, sannu da kokari".
Ya dan sassauta ya ce "Sannun ka dai Yabi Asiya".
Na dan murmusa domin shi ka'dai ne yake ha'da mini sunan guda biyu. Tunda ya fahimci ina bacin rai idan ba'a ce mini Yabi ba, sai ya kankare kirana da gayan Asiya.
Na wuce shi na fa'da d'akin Mama wajen Nazira.
Na tarar itama shirya wa take yi.
Tare muka fito muka risina muna cewa "mun tafi Baba".
Ya amsa da cewa "A dawo lafiya, ku kula da kanku".
Muka shiga sashin Baban Tsakiya muka fito da su Firdausi da Saratu.
Amma wani irin abu ya tsirga mini mai nauyin gaske, ba dan komai ba illah ganin da na yi Baban Tsakiya yana cin dafadukan shinkafa gefe kuma kunshin balangu ne, ga pure water mai sanyi a gefensa cikin yar bak'ar leda da alamu shi ya shigo da su.
A banzan ce ya amsa gaisuwarmu tamkar ma bai ganemu ba.
Na tuna gabzar da muka baro Baban Marina yana ci zufa tana yanko masa.
A hankali na ce "Àllah ga Yabi! Ka buda mata hanyoyin arziki ta jiyar da iyayenta da'din duniya".
Kafin muje k'ofar Baban kasuwa muka yi kicibus da Maijidda, ta fito.
Na ji da'din hakan domin shi kam ma tsiyatakunsa sun fi na Baban Tsakiya yawa.
Gaba'daya muka d'unguma k'ofar Dada dan yi mata sallama da kuma biya wa Nasiba.
D'aya bayan d'aya muke gaisuwar tamkar masu neman tabarraki, kuma dole sai an kama sunanta idan ba hakan ba sai ta dauke kai tabbacin bata karbi gaisuwar ba. Abin da zai biyo baya kuwa ba mai sau'ki ba ne.
****
An idar da sallar isha dukkan mun hallara a k'ofar Dada.
Sai jiranta muke ta kammala nafilfilinta ta d'ora mana karatu, domin karatun nata ba k'aramin nisha'di yake sanya mu ba.
Ta idar ta dinga jan dogon carbinta wanda kafin ka kammala jan k'afa d'aya ma lokaci ne mai yawa.
Amma haka muka jira ta kammala. A fili ta cika addu'arta da salatil fatih.
Dada tsohuwa ce da bata samu ilimi sosai ba, amma Ubangiji ya cika zuciyarta da son addini, ta rabauta da yawan yin istigifari, matsalarta guda tana da son zuciya, matu'kar zaka bata abin duniya to zata juya gaskiya ta koma karya.
Hakan kuma ya yi tasiri a zukatan ahalinta, domin kuwa a tsakaninmu ma mun k'ullaci yadda take fifita Nasiba akanmu, ta yadda ta fimu gata da iko a gidanmu. Kowa yasan Dada tafi son jikokinta da y'ay'anta mata suka haifa, mussaman su Nasiba sannan Bulkachuwa.
Saratu ta ce "Dada muna dakon karatun ne, jiya kin ce addu'ar tsari da makarai da miyagu zaki d'ora mana."
Ta dan yi tari ka'dan ta ce "Hakkun Saratu".
Ta numfasa ta ce zan biya sau uku daga nan sai ku dinga fa'da bayan na fa'da."
Muka amsa da cewa "To".
Ta yi Basmalah, ta yi salati ga Annabi, sannan ta nemi tabarrakin SHEHU.
Na yunkura zan yi magana sai kawai na yi maza na saka hannu na kame bakina.
Da karsashi ta ce *"Wa makaru, wa makaru, Wallahu kairan makirina".*
Na amsa karatun nata ina ganin kuskuren ciki ka'dan ne.
Muna saurare har ta biya sau uku kamar yadda ta fa'da.
Sannan muka koma tana yi, muna amsawa har kuma ta ce mu yi da kanmu.
Muka dinga yi har muka rike dama kuma mun biya ayar a islamiyya.
Ina son na yi mata gyara amma ina jin tsoron abin da zai biyo baya.
Ganin mun ri'ke sai ta ce "To zan baku addu'ar farin jinin samari, ku yawaita yinta atafe kuke, ko a zaune ko kuma a kwance".
Muka yi shiru dan nuna kunya.
Ta numfasa ta ce *"Ya tifa risubuha ragadan".*
Muka k'yal-k'yalale da dariya, na kasa daurewa na ce *"Min kulli.."* kafin na karasa ta ce "Lah! Ai iya inda na tsaya, zaku dakata, duk wacce ta yi karambanin cika ayar to ta kuka da kanta. Domin maza kala kala zasu yi ta bin ta har mazan dabbobi sai sun bi'de ta da sunan soyayya saboda karfin addu'ar, kunsan Annabi Isibu aka saukar wa ayar."
Muka kasa cewa uffan domin kowa dariya ce a bakinsa yake gimtse wa".
Ta kalli Nazira, Saratu, da Nasiba ta ce ku dimance ta babu kakkautawa kune masu nauyin jini, ke Yabi ba sai kin yi ba, ku kuma ragowan saffa saffa zaku dinga yi tunda kuna samun mane ma."
Nasiba ta bata rai ta ce "wanne irin nauyin jini kike magana Dada?
Duka duka fa shekarunmu sha shida ne wasu ma basu cika ba, ban da dai ana auren wuri a gidan nan ina ma muka isa a samu a sahun y'anmata a wannan zamanin?".
Dada ta ce "A wajena kun wuce y'anmata ma kun zama iyayen mata, tunda ba wacce bata yin wanki duk watan duniya, ni kam kullum sai na yi tuba sama da sau dari uku, tare da addu'ar Allah ya cika mini burina wajen sallar layya ace ko wacce maneminta ya tsaya duk sai mu tattara mu rabu da ku salin alin.
Amma a duk sadda na hango zugar ku gabana faduwa yake yi, inta shiga firgicin yadda sallolimmu suke goriya a madakata basa isa gaban Zati".
Cikin dariya na ce "Wai a ina kike koyon wadannan karatun naki irin na makafi ne?".
Haka kawai na fa'da ta rusa ihun da ya janyo hankalin ahalin gidanmu, mu kuwa gaba'daya muka zuba mata ido muna mamakinta, yayin da jikina ya yi mugun sanyi, zuciyata ta shiga kaiwa da komowa cikin fargaba mai yawa.
Cikin kankanin lokaci dukkan iyayenmu maza sun bayyana, wasu daga cikin matan gidan suma sai iso wa suke yi cikin zullumi duk da dai ta kan yi irin haka sa'i, sa'i.
Tana kukan tana fa'din "Yabi ce, Yabi ta zage ni, ta mini gorin mijina makaho ne".
Mamaki ya sake kama mu, domin sai a ranar muka san kakanmu Alh Garba wai ashe ya makance a karshe karshen rayuwarsa, duk cikinmu ma ba wadda ta san shi bare har a yi mata gori, sannan dama ana gorin ciwo ne?"
Haka Baban kasuwa da yake jin shine a saman kowa, ya hau cin mutuncina yana fa'din ba zai yiwu kullum sai na tozarta uwarsu ba.
Zai dauki mummuna mataki a kaina ya ga take takena so nake na gagari kowa, to shi ba zai zame masa komai ba akan mahaifiyarsa ya kore ni daga gidan, ko kuma ya dauke Dada su bar mini gidan, idan ya so iyayena su shata jan layi da shi.
Baban Marina kuwa cikin sanyi yake fa'din "Haba Iliya yaushe zan haifi y'ar da zata shiga tsakaninmu, komai zaka yi mata ai ka isa ne".
Baban Tsakiya ya ce "A a ai yaran yanzu basu da kunya balle mutunci baka ganin yadda ta saka uwarmu kuka to mu kuma idan muka ce zamu shiga shirgin ya'yanka ai sai dai su rufe mu da duka tunda a cikin idonsu muke ganin bakincikin da suke yi da mu, tamkar dai mune muka hanaka ka sake tara arziki, ko muka hanasu yin zuciyar tallafa maka. Ban da lalace wa Musa ka'dai bai isa ya ri'ke kofarka ba? Ya'yanka wajen hudu ko biyar ne a daki amma duk wula'kantattu ne, basa taimaka maka da komai, amma abin kaico sun raina kokarinmu akan ka."
Baban Marina ya sunkuyar da kai kasa gwanin tausayi yana fa'din sai ha'kuri da yaran yau, ni kuma har yau din nan basu fiye mini ku ba".
Na kalli Nazira na ga hawaye na tsere akan fuskarta, na sake kallon ragowar, su Firdausi kowa idonta a bushe tabbacin basu da kaico akan cin mutuncin da iyayensu suke yiwa ubanmu.
Na kasa hawaye a dalilin ba'kin cikin da yake cina yafi gaban hawaye.
Ba abu mai ciwo irin wanda ba za'a barka ka keta shi ba, ya tisa iyayenka a gabanka da cin mutunci akan idonka.
Na sake kai idona kan Dada da take matsar hawaye, na dinga mamakin yadda ta tara mini jama'a haka.
Na gama yarda kafatalin jikokinta ba wacce take jiran kiris akanta iri na.
Duk yadda Nasiba take zage wa suna yin sa in sa, hakanan kowa a cikinmu tana mayar mata da magana amma ba wanda take mayar da laifinta garma sai ni.
Tausayin mahaifina ya yi matu'kar kama ni ta yadda kannensa suka tsaya a gabansa suke fa'da masa maganganun da komin sanyin halinsa sai sun mintsine shi.
Kirjina ya sake nauyi akan wanda ya yi dazu da naga Baban Tsakiya yana cin da'di a kofarsu amma mu muna cin abinci irin na yan fursuna, kuma suna da halin tallafa wa. Amma sun runtse idonsu.
Haka Baban Marina ya dinga bawa Dada da sauran y'ay'anta ha'kurin katobarar da na yi tamkar dai shi din ba uwarsa ba ce.
Sai lokacin hawaye mai ciwo ya goce mini, ina jin tsanar mutanan da a baki Baffanina ne.
Maganar gaskiya kuma na fi jin ciwon Baban kasuwa.
Haka suka fice suna kumfar bakin na fitine su, na fitini y'ay'ensu, tunda ba'a sati ba a doku da ni ba a cikin gidan.
Rainin da aka yi mana ne ya sanya dukkan mutanan gidan suke ganin zasu mayar da mu gidadawa, shiyasa ni kuma na lashi takobin duk wanda ya nemi ta'ba ni, ko taba wani cikin yan k'ofarmu la shakka ni ya ta'ba domin zan siyi fa'dan ne ya dawo kaina, duk yadda nake yar shafal amma Ubangiji ya hore mini wani irin karfi tamkar shari'a, ko dan da dukkan zuciyata nake yin fa'dan ne oho.
Yadda nake tare wa kannena fa'da da muke daki d'aya haka nake tarewa na yaran Inna amaryar Babanmu babu banbanci.
Hatta Nazira da take yayata ni nake tare mata fa'da domin duk wanda ya fa'da mata maganar banza zan yi ruwa na yi tsaki na shiga na dinga yarfa bak'ar magana har sai abin ya juye kaina.
Duk yadda nake jin haushin Mama bai shafi son da nake yiwa Nazira ba.
Domin yar-uwata ce da uba ya ha'damu, idan da abin da na tsana ban kuma yarda da shi ba shine yan'ubanci.
Ina matu'kar takaicin yadda wai gidanku daya da mutum, cikinku daya, gadonku daya amma babu yarda da amana a tsakaninku.
Duk wani alherinka baka son dan-uba ya ji, zaka iya fa'dawa bare matsalarka amma ban da dan-uwanka da uba daya ya hada ku.
Kuma mafi yawa iyaye mata ne suke bari yaransu su shiga cikin rikicin da ba nasu ba.
Da ace Nazira tana biye hudubar Mama da tuni ta gurbata mana zumunci da soyayyarmu, mun koma muna adawa da junanmu.
Wai uwa ce zaka ji tana zayyane wa y'ay'anta laifin kishiyarta, ko kuma laifin y'a ko d'an da ba nata ba.
Da ace iyaye mata zasu dinga ha'diye rikicin kishi a tsakaninsu, suna boye rashin jituwarsu a gaban yaransu, sannan idan matsala ta faru suna barinta a tsakaninsu da an samu sassauci wajen yan ubancin da ake yi a yau.
Idan d'an kishiya ya yi miki laifi ko ta yi miki, daure ki ha'diye ba sai kin baza wa yaranki da basu sani ba, gudun haddasa gabar da baki san iyakacinta ba.
Ko wanne d'a a duniya gaibu ne, ba wanda yasan me gobe zata zo da shi, ba lallai d'an da kika haifa ya samu daukaka ba, wata'kila sai d'an miji ya samu daukaka fiye da yaranki, adalcin ki ne zai sa Ubangiji ya sarrafa zuciyarsa ya ji k'anki, haka nan ke ma babu jin kunya ko nauyin kin yi abubuwa a baya marasa da'di.
Na sani mutanan yau bamu cika gode wa da yaba kokarin abokan zamanmu ba, muhimmi dai mu yi adalci a tsakanin zaman kishi da yaranmu, ko ba a shiri ya zama akwai sassauci da ha'diye bacin rai, shi adalci yana haifar da farin-ciki da yalwar arziki da hadin kai a cikin gida.
Addinin musulunci cewa ya yi ko wanne musulmi dan-uwan musulmi ne, bare kuma wanda jini mai k'arfi ya ratsa a tsakaninku.
Daga shakiki sai li-Abbi a duniyar musulunci da zumunci amma mutanan yau mun dauki wata irin *Bak'ar Ta'ada* ta mayar da dan-uba abokin gaba kuma makiyi.
Da kaina na jinjina wa kaina da duk wacce bata da wannan mummunar manufar a ranta.
Madallah da mutanan da suka yarda Ubangiji ne yake zaba mana mutanan da zasu zama iyayenmu da yan'uwanmu.
Alhamdulillah, Allah ka bamu ha'kuri da juriya wajen mua'amalantar mutanan da ka d'ora mana hakk'in zumunta da su.*Kafin lokacin zaku iya fara payment ta yadda idan an fara babu dogon jinkiri.*
*Madallah da masoyan RUBUTUNMU*.
*Madallah masu sauke hakki komin kankantar sa, madallah da masu k'arfafa guiwarmu*.
*Fatan alheri ga masu kiyaye hakkin sana'ar y'anuwansu*.
*500 for regular*
*1k for VIP**2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*ZENITH BANK*
✍️
YOU ARE READING
BAKAR TA'ADA
General FictionMurya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina". Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito...