chapter 7.

245 42 12
                                    

13&14.
Da azama na shige cikin gidan na bar shi domin na samu sau'kin halin da nake ciki.
Kuka na dinga yi tamkar zuciyata zata fa'do k'asa, bansan son Yaya J ya tumbatsa a zuciyata irin hakan ba sai yau, domin sai na tsinci kaina da addu'ar na zama gawa kafin igiyar aure ta d'auresu da Maijidda.
A wannan daren barci rabi rabi na yi shi.
Washagari da hantsi sai ga shi ya dawo, kallo d'aya na yi masa na gane yana cikin zullumi mai yawa domin gaba'daya ya zube ya sake fige wa.
Yaya Salisu da ba shi da matsala da kansa ya masa iso har cikin falon gidan da yake dakuna uku ne a jere falle falle.
Na fito a sanyaye sanye da hijabi idanuwana a kumbure a dalilin kuka da rashin barci.
Na zauna a kujerar da ta yi nesa da wacce yake zaune.
Tsawon lokaci muna zaune jigum jigum, tamkar masu makoki, daga karshe dai ya k'osa cikin murya marar amo ya ce " Yabi babu gaisuwa ne?"
Kaina a kasa na ce akwai gaisuwar da tafi nema maka amincin da na yi?
Shin ka raina sallamar ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakkun Yabi. Kin fini kusa da daidai, kin yi barci kuwa?".
Kaina a k'asa na ce "Me zai hana Yabin Marina barci a wannan duniyar? Sai mutuwa, ko ciwo".
A matu'kar sanyaye ya ce "Idan kuwa hakane ki shirya kwanan zaune domin kullu nafsin za'ikatul maut. A kowanne lokaci muna iya rasa mutane mafiya daraja a rayuwarmu, ko kuma a jarrabemu da ciwo mai hana runtsawa. Fata dai Allah ya bamu ikon cinye dukkan jarabawowin da suke dunfaromu.
Ban da dai dan-adam an jarrabe shi da tsoron mutuwa, mene ne abu mai da'di a cikin wannan duniyar da a kullum tsanani da bacin rai suke sake yiwa mumini k'awanya?"
Ban tanka masa ba, domin kuwa gaba'daya zuciyata babu sukuni, kuma cike take da ba'kin ciki mai nauyi.
Cikin alhini ya ce "Yabi ban yi zaton munin dambarwar da take faruwa ta kai lalacewar da ta yi ba!
Na gamsu, na ha'kura da aurenki a yanzu, dan na tsaremu daga fa'dawa halaka.
Amma na rantse miki babu wata macen da zan sota irin son da nake yi miki, zan kuma dauwama a cikinsa.
Tsoron hakkkm iyaye ne kawai zai sanya na yarda na yi aure kuma na mua'amalaci matar cikin adalci. Amma ban ha'kura da ke ba, zan cigaba da kokarina har sai Ubangiji ya mini taimakon tabbatar da aurenmu.
Hawaye ya balle masa tamkar ba namiji ba.
Da rawar murya ya ce "Akwai bukatar mu tsananta addu'a a cikin zumuncin Gidanmu Yabi. Daga jiya zuwa yau na fahimci BAK'AR TA'ADAR wariyar launin fata, ta yi kane kane a cikin gidan".
Na dago idona jage jage da hawaye na ce "Komai zai dai-daita idan arzikin Baban Marina ya dawo, ko idan ya'yansa suka kawo k'arfi."
A kasalance ya ce "Ba wannan ce matsalar ba kawai.
Shin menene ribar hana ni auren ki?"
Na dago na ce "Saboda ana ganin zan samu cigaba, ana ganin ban cancanci na samu irin wannan darajar ba, bai kuma kyautu ayi wa Baban Marina irin wannan zumuncin ba tunda ba za'a amfana da shi ba, an kuma rufe ido an mance irin amfanar sa da aka yi a shekarun baya".
Ya yi shiru ya ce "ban gamsu ba, idan kuma wannan ne hujjar da gaske?
Menene dalilin da zai sa ba za'a bawa Bulkachuwa auren Nasiba ba?
Ai duk lalacewarsa jininmu ne. Idan za'a hana shi mace a cikin danginsa to ina za'a bashi? kawai halin da ya jefa kansa ne  ya sanya baya iya tanadi. Amma idan aka bashi mace na tabbatar indai yana samun nutsuwa da ita, zai nutsu ya zama mutum na sosai, sannan zai daina zalama da tsilla tsillar da yake yi tunda yana da tasa ta halal a dakinsa ."
Duk da matsananciyar damuwar da nake ciki sai da maganganunsa suka jefa ni cikin kunya da takura.
Na kasa magana.
Ya sake cewa "To saboda Allah idan ba'a taimake shi a cikin danginsa an rufa masa asiri, an tsaya kai da fata wajen ganin al'amarinsa ya kintsu ba, me za'a yi masa? A wajene ake son ayi masa irin wannan sadaukarwar da kishin kai?
Babban tashin hankalin ita Nasiban sonsa take yi kamar ta kai kanta dakinsa. Da ace bata sonsa na zan ga laifin kowa ba.
Shin wanne irin zamani muke ciki ne mai cike da son zuciya?"
Nan ma na kasa cewa uffan domin tunanina ya riga ya tsuke, ban sani ba ko dan har yanzu ban gama fahimtar al'amuran da shi ya fahimta a tsakanin yammacin jiya zuwa yau ba.
Ko dan ya fini shekaru, ya kuma fini ilimi da hangen nesa ne oho.
Gaba'daya a rikice yake, k'warai kwamacalar da take cikin gidanmu ta gigita shi.
Nasan bai san haka abin ya tsananta ba, tunda ba kasafai yake zaman garin ba.
Ya jima kafin ya sake cewa komai.
Ya mike ya zura hannunsa a aljihunsa.
Ya ce "Bansan me zan ce miki ba, amma nasan zan rayu da son ki a raina muddin rai.
Zan kuma rayu tamkar wanda ya rasa bangare guda a jikinsa. Ina fatan Ubangijinmu Allahu ya sanya mu cikin masu soyayya dan Allah. Har kuma yanzu da nake miki wannan jawabin ban cire alkalamina a cikin tawada ba. Ban cire rai cewar kaddara tana iya bani damar mallakar ki a matsayin matata ba.
Ina neman alfarma, komin kankantar damar da zamu samu ta cikar burinmu kada laifin da bani na yi ba, ya shafi hakan Yabi.
Ina da burin idan mun yi aure na mayar da ke makaranta ki zurfafa a ilimummuka daban daban.
Amma ko yanzu ma ban fitar da rai ba, lokaci zai zo da zaki tsaya ki yi karatu tuk'uru, ki cire shiriritar da kike yi.
Mu tsananta addu'a, mu barwa Allah ya yi mana zabin da ba zamu koka ba. Kin fini gaskiya duk al'amarin da babu saka albarkar iyaye to tsinannen al'amari ne.
Fatan alheri gareki Yabin J".
Ya fice da sauri.
Jikina ya yi matu'kar sanyi, domin na tabbatar akwai abin da Yaya J ya ga ni a cikin zumuncin Gidanmu da ya warware masa duk wani confidence dinsa.
Na kagu na samu labarin irin wainar da ake toyawa a gidan Marina.
Na rasa yadda zan yi, domin Yaya Salisu ba mai zama ya tattauna magana da mutane ba ne.
Na matsu kwarai na ga Nazira domin a bakinta zan ji komai kuma babu k'arya ko karin gishiri a cikin kalamunta.
Kwanaki suka yi ta shudewa, ban samu ganin Nazira ba, ban kuma ji labarin komai ba.
Abin da yake damuna daya ne takunkunmin hana ni zuwa gida da aka sanya mini.
A hakan har na shafe kwanaki ashirin da biyar a gidan Yaya Salisu.
Na riga na kai k'ololuwar gajiya da son jin makoma ta.
Gashi ba wanda ya zo daga gidanmu.
Dan ma ina samun y'an kitso da k'unshi, suna biyo ni, haka na unguwar ma suke yi mini layi.
Rannan da na gaji, sai kawai na zari jiki na doshi gida a sayyadata duk da tazarar gidan Yaya Salisu zuwa Gidanmu tafiya ce mai tsayi ainun.
Tunda na kusa k'arisa wa na fara jin jikina na kakkarwa, ga kuma luguden da zuciyata take yi tamkar ta faso ta fito.
Bakina na ambaton sunan Allah, duk da idan ance na fa'di me nake fa'di ba zan iya tantance wa ba.
Na fa'da zauren na yi kicibus da  Baban Tsakiya, zai fita, da alamun rashin sukuni a tare da shi.
A farko kamar ba zan gaishe shi ba.
Bansan ya aka yi ba, cikin rawar murya na ce "Baban Tsakiya ina yini?"
Ina daga tsaye ban rusuna ba.
Ya mini dak'uwar da ta zame masa dabi'a ya ce "Baban farko ba na Tsakiya ba. Wato ke tabbataciyar yarinya ko? Sai kin ha'da da inkiya saboda ba kya mini kallon arziki.l?
Zan ga mai daura miki aure, sai dai Ubanki ya waklice ki da kansa.
Kuma indai ina numfashi duk wanda ya zo neman auren ki sai na fa'da masa rashin d'aarki da hatsabibanci irin na ki, domin fadar gaskiya a neman aure jihadi ne kabiran".
Na yi k'asa da kaina ba tare da na ce komai ba.
Ya juya ya tafi yana ta yi mini sababi da kwashe albarka da fatan tsiya iri iri.
Na jingine a jinkin garun ina tambayar kaina "Wai haka kowa yake fuskantar bacin rai da danginsa ko kuwa iya ni ce?
Take na tuno Nazira bata fuskantar tsanani irin nawa a wajen Baffannin namu. Amma kuma ko ka'dan bata samun sakin fuska da alherin da suke yiwa ya'yansu.
Na sake tafiya dogon tunanin yadda Baban Marina yake mua'amalantar nasu yaran.
Mua'amala ce ta sassauci da ja a jika.
Domin duk talaucinsa, yana k'ok'arin siyan albasa ko su mangwaro ya ce mu mika kofofinsu.
Hakanan indai zai yi aski sai ya ha'da da ya'yansu an musu ya biya.
Bayan nan duk wani rikicin da ya'yansu zasu rakito shine zai yi ta zarya yana bada ha'kuri har sai komai ya daidaita.
Amma su ba ruwansu damu, wani ikon Allah Yaya Musa da yake a lalace sun fi sonsa, sun fi yinsa, sun fi tattalin farin-cikinsa.
Na jijjiga kai a fili kuma sai na ce "Allah haska kofar Baban Marina, Allah ka jibanci al'amarinsa da na ya'yansa.
Na shige cikin gida ban doshi k'ofar Dada ba.
Yanayin da na tarar da Babanmu da ahalinsa ya sake sanyaya mini jiki.
Na shiga bakina da sallama na isa kan tabarmar da suke zaune na tsugunna ina gaishe shi cikin girmama wa.
Ba walwala Baba ya ce "Asiya me kika zo yi?
Ba na ce sai na neme ki ba?"
Da rawar murya na ce "A mini afuwa Baba! Na kasa jure ji daga gareku ne."
A sanyaye ya ce "Na miki afuwa Yabi zo ki zauna.
Da rarrafe na karisa kusa da shi a dalilin rawar da jikina yake yi ya sake ta'azzara.
"Na yi godiya Baba Allah ya k'ara maka lafiya, ya shirya maka zuri'a, Allah ya mayar da ahalinka wasu masu fa'da aji".
Ya yi murmushin da babu nisha'di.
A sanyaye ya ce "Ameen Yabi! Duk yadda zan yi ba zan iya cire miki wannan BAK'AR TA'ADAR k'ullaci da ta shiga ranki ba.
Amma abin da zan fa'da muku duk taku, duk wanda bai mutunta y'anuwana ba, to nima kar ya mutunta ni".
Jikina ya yi sanyi, na yi kasa da kaina, na kasa cewa komai.
"Yabi".
Ya k'ira ni murya babu amo.
Na amsa a hanzarce "Na'am Babanmu".
Ya yi gyaran murya ya ce "Nan da kwanaki goma sha biyu auren y'anuwan ki.
A duk wanda kuka taso ke da Nasiba ne kawai babu ku a cikinsu.
Da gobe zan je na sanar da ke maganar a nutse cikin kwanciyar hankali.
Na tura wa iyayen Abdulrashid su turo ayi magana to bansan inda aka haihu a ragaya ba, sai suka aiko mini da sun yi wa d'ansu mata tuntuni, ba da yawunsu yake neman auren y'ata ba."
Jikina ya sake daukar bari a dalilin idan na fahimci maganar Babanmu kenan zan rasa Yaya J da kuma Abdul tashi guda, wannan shine biyu babu, kamun gafiyar b'aidu.
Na tattaro dukkan jarumta na yafa a dukkan sassan jikina da fuskata.
Na ce "Babu damuwa! Allah ya sanya alheri. Amma Baba har da Adda Nazi kenan?"
Na fa'da cike da karsashi irin na tsananin karfin hali.
Ya ce "Da ita Yabi, sai dai bana jin za'a yi tariya da ita, domin ban mallaki komai na aurenta ba, tunda titsiye aka yi mini."
Na kalli dukkan yaran gidanmu masu hankalin suna wajen hatta Yaya Musa kuwa.
Hawaye ya b'alle mini na ce "A a Babanmu da ikon Ubangiji a ranar zata tare.
Na kalli Yaya Salamatu na ce "Yaya"
Sai kuma na fashe kuka sosai.
Dukkansu matan sai suka taya ni kukan in ban da Yaya Ummi da take Jin zafin yadda nake damuwa da lamarinsu 
alhalin ita ma ba sonta suke yi ba in aka dauke Naziran.
Da rauni Yaya Salamatu ta ce "su uku sun kawo dubu sha biyar biyar, yan dakinsu kenan.
Sai ummi ta kawo dubu biyar, Ni kuma na bayar da ashirin maigidana kuma ya bada buhun masara da na shinkafa ayi hidimar biki da su".
Su Salisu kuwa sun ha'da hamsin a tsakaninsu dan haka dari da ashirin ne a k'asa kacal".
Nan da nan na zaro magana tamkar babbar mace na ce "Ai kuwa sun isa Yaya, kuje ku siyo mata katifa da labule da ledar tsakar daki.
Na kunce hannun zanina na kunce na fito da kudi kimanin dubu sha bakwai da dari takwas.
Na ce ga nawa a siya mata bargo da zanin gado. Su Mama ku fito da kwanuka da tukunya.
A kai ta a hakan da ikon Ubangiji watarana sai ta yiwa wani kayan daki na alfarma, ai duniya ce mai rawar y'an mata na gaba ya koma baya".
Hatta Mama a wannan ranar na ga kallon sassauci da adalci take yi mini, domin da ta ga na sake dauko bankina na mik'a wa Nazira na ce "Ki fasa ki yi dinkin fitar biki nasan zasu ishe ki tunda kinsan mu din masu k'aramin karfi ne, masu nema a wajen Àllah."
A fili take fa'din "Yabi da Nazira sai Allah".
Baba kuwa zuba mini ido ya yi, tsawon lokaci kafin hawaye ya goce masa.
Duk muka ha'du aka yi ta kuka tamkar an ce ya mutu ne.
Domin ita kanta Mama da take ha'da kai da matan su Baban Tsakiya suna sake tsananta mana, ta sha mamaki da ta ga suna yiwa ya'yansu hidimar aure basu yi kara sun saka da Nazira ba.
Wata'kila a haukanta zasu yi ko saboda da ita.
Da rawar murya Baba ya ke fa'din "Allah ka sake  jefa soyayya da tausayi a tsakanin ya'yana, Ubangiji na gode maka".
Yaya Indo ta kira Malam Yunus ta fa'da masa ku'din lefe ya bayar yadda zai iya ba sai ya yi ba , domin kuwa muma abin da zamu iya za'a yi.
Da yake ba yaro bane ainun, sai ya gamsu ya ce zai yi mata lefen yadda ya sauwaka, sannan zai bawa Yaya Salisu ku'din da ya sauwaka shi mutunci ya gani dan haka komai zai yi.
Ba wanda ya san me ake ciki domin kowa ya zuba ido yana jira aje ganin dakunan amare
Yayin da ta bangarena nake ta danne damuwar auren da Yaya J zai yi da Maijidda.
Ita ka'dai ce amaryar da bata da kuzari a dalilin babu ha'din kai ko zumudin ango, komai sai dai mahaifinta ko na angon su yi mata.
Gefe guda kuma Nasiba ta susuce domin ba karamin son Bulkachuwa take yi ba, wanda aka ce ya fito kuma a dangin Babanta sun ce bai shirya ba sai bad'i.
Bulkachuwa kuwa yarinyar da suke takaddama ta haihu an yi gwajin halittar dan Adam bashi da alaka da jaririn.
Sai dai an yi masa hukuncin bulala tamanin tunda ya amsa da bakinsa ya ta'ba takarta.
Wannan lamarin, da bulalar ya yi matu'kar sururuta shi.
Ya zama abin tausayi, duk wani iyashegensa ya zubar da rabi.
Kowa ya ganshi sai ya tausaya masa.
Hatta ni da bama ga maciji sai da na yi masa jaje. cike da alhini, ya dinga fa'din na gode "Asiya Toro, ki yafe mini, a duk sadda na tuna addu'ar da kika yi mini cikin fishi da kika ce sai na hadu da sharrin mace, sai na ce ashe dai Asiya bayan samun tallafin dan aljani yayin fa'da, har baki idan kika yiwa banu adam sai sun taimake ki, ya zama wajabat. Shiyasa na k'udire zan roke ki, ki mini addu'a na zama yadda mutane na gari suke".
Na girgiza kai na wuce shi "Ina cewa "Allah ya shirye ka Tijjani".
Ya d'aga murya ya ce "Da biyu  kika yi wannan addu'a domin da zuciyarki fes take da ni Yaya Tijjani zaki ce".
Ban tsaya ba, bare na tanka shi, a zuciyata kuwa ina fa'din mashiririci, ba sauya wa zaka yi ba, borin kunya ne kawai, ka zubar da mutuncinka a idon  kannenka da iyayenka, Allah ya shirye ka kawai.
Shikenan sai na dawo gida, muna ta shirin bikin Nazira. Auren da ya zo tamkar dirar mikiya, ya yi matu'kar rage mini tashin hankalin da nake ciki.
Kitso da lalle nake yi babu hutu, tun safe idan na zauna sai magariba, sallah kawai take tayar da ni.
Haka nake mika ku'din ga Baba ina fa'din "A dinga siyan kayan cefanen biki Baba"
Da farin-ciki yake fa'din "Madallah da Yabi Asiya".
Kallo daya za'a mini a gane ina cikin tasku kawai boye wa nake yi, sannan son Babanmu ya fita kunya da tozarta da ake son ya yi, ya danne wanccan damuwar.
Domin yadda nake kishin Babanmu da yan k'ofarmu bana jin anan kusa za'a samu mai yin hakan.
Shiyasa na cire son jiki, da lalaci nake sana'a, Ubangiji kuma ya haska, ya saka mini hannu, domin a rana ina hada dubu shida zuwa bakwai, mussamna idan kwanakin da ake yin biki ne. Da ce a birnin Kano nake yarfa kunshin nan ai da ku'di masu nauyi zan dinga ha'da wa, amma hakan ma na gode sosai, tunda mafi yawa manyan mata idan sun zo basa bayar da iya ku'din sai sun mini k'ari.
Bana kuma jin k'yashin na bayar da komai dan mu yi hidimar mu cikin rufin asiri.
Duk yadda Yaya J yake son mu ha'du na rufe kofofin da zasu sa mu kebe.
Ranar litinin dukkanmu muna wajen Dada.
Ana ta hira, na yi lakwas a dalilin bani da kuzari, ba k'aramin cizona auren J da Maijidda yake yi ba, har addu'a nake yi kada a wayi gari aga zuciyata ta buga a dalilin ba'kin ciki.
Kwana nake yi ina kuka, ina kalubalantar wannan hukuncin da aka zartar mini tare da tsanar Baban Tsakiya da Baban Kasuwa.
Tabbas a idona su din ba kowa bane face mutane masu son kai kuma y'an jari hujja.
Dada sai farin-ciki take zata aurar da jikokinta kusan goma.
Ta kalle ni ta ce ",Ke da Nasiba ne aurenku ya yi gardama, ga shi kune fitanannu."
Ban kula ta ba domin abin da yake zuciyata fadinsa da ciwonsa sai ni da mahaliccina.
Balle Nasiba da ta bari halin da take ciki ya bayyana a komai na ta.
Ni mamakin da take bani wai akan Bulkachuwa take wannan ba'kin cikin, sannan abin kaicon shi bai ce yana sonta ba, kawai ya lura da yadda take mararinsa sai yake amfani da hakan yana sata tana yi masa bauta.
Misali komin dare zai kawo indomie ya ce ta dafa masa, ko kuma ya ce ta dafa masa ruwan wanka, ko shayi.
Haka idan zai fita zai bata mukullin dakinsa ta je ta gyara masa.
Bai zame masa komai ba, ya kawo mata kayansa matu'kar zai ga tana wanki, yana fa'din "Ga karo".
Bata damuwa hakan zata karba, ta wanke, ta goge.
Shikenan sai yake sassauta mata ya daina yarfa ta.
Ita kuma ta dauki son duniya ta dora masa bata ko lura da rashin nagartarsa, duk kuma wanda zai zo da nufin yana sonta bata sauararansa, sai Dada ta yi mata wuta wuta. Matu'kar kuwa yana gida ba zata yarda ta fita ba, duk tijarar Dada kuwa.
Tunda mahaifiyarta ta ce bai cancanci a bashi aurenta ba, ya dauke mata wuta, ya daina kula ta, ya koma muzurai ne a tsakaninsu shikenan sai ta k'aratan wa kanta walwala, tunda ba yadda bata yi ba, ya fahimce ta shi kuma ya taurare.
Saura kwanaki biyu aure domin tuni gidan ya fara cika da jama'a ana ta hidima tuni an yi wa amare jere.
Da ni aka je jeren Adda Nazi, na dinga k'walla a dalilin irin rufin asirin da Ubangiji ya yi mana.
Komai ya yi, ba wanda ya zaci za'a samu hakan.
Na dawo Yaya J ya rutsa ni a soro.
Murya a dushe ya ce "Yabi menene ya yi zafi ne, shin gaba zamu yi?"
Da sauri na ce "Eh mu yi gabar kawai, yafi mini sauki da na saurare ka."
Ya numfasa ya ce "Oh no! Kada ki yi mini hakan, ya miko mini leda mai dan dama.
Na dauke kai na ce "Bana bukatar komai na ka".
Ya rausayar da kai ya ce "saboda zumunci na baki fah".
Na ce "To kuwa bana so, domin na shafe alakar da ta ha'damu".
Ya fusata, sai kuma ya ha'diye dukkan fishin ya ce "To karbi dan Allah, dan soyayyar da nake yi miki".
Na mika hannu na kar'ba ba tare da na ce uffan ba.
Ya sassauta ya ce "Wannan auren ba zabina bane Yabi, ba abin da zuciyata ta za'ba mini ba ne. Dan haka zan yiwa kaina auren da zuciyata take so take kuma muradi.
Na rok'e ki, kada ki juya mini baya. Kada ki haramta mini farin ciki a zuciyata da rayuwata."
Yana diga aya sai kawai na rushe masa da kuka mai tsananin gaske.
Fadi nake "Lallai kuwa wato zan yi ta zaman jiran ka ko?
To ko dai kallon Yabin mahaukata kake mini ba ta Marina ba?"
Ya ki'dima ya ce "me ya kawo wannan maganar?
To ai ni ko a turu nake kallon ki ra'ayil aini, zan cigaba da son ki babu gazawa, cikin kowanne hali son ki nake yi, zan kuma cigaba da son ki YABIN J".
Na ha'diye kukan da nake yi.
Na zuba masa ido na ce "Na gode da soyayyarka, Allah ya bada lada".
Kafin ya yi magana Bulkachuwa ya shigo, ya kalle mu kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya kasa ha'diye maganar ya ce "Poor baby haka kawai kin zuba ido an k'wace miki abin da yake na ki ne, ni fa akan abin da nake so sai dai ayi kare jini, biri jini da ni."
Ya kalli J ya ce "Jabir ka daina tare yarinyar nan tunda dai an baka wata ka karba, bar ta ta ji da suyar da kirijinta yake yi mata kawai".
Yaya J ya daure fuska ya ce "Menene hakan kuma Bulkachuwa?"
Ai kuwa ya ce "Gaskiya ce mana Jabir, ni yanzu da aka hana ni Nasiba ka ga na damu ne?
Ai saboda dama soyayyar ba mai karfi ainun ba ce.
Da son ya zama so deep da komai zai faru, ba zan yarda na musanya ta da wata ba".
Takaicinsa ya shake Yaya J. Ya nuna shi da yatsa ya ce "Bana son irin haka Bulkachuwa".
Ya make kafa'da alamun ko oho ya wuce yana sake fa'din "Ato ai gaskiyar magana kenan, ku barta ta ji da bacin ran da take ciki mana, ai kowa yasan tana sonka, akan idonta da na iyayenta aka dauki wata aka baka, ka karba da sunan biyayya, amma ka kasa gwada kwanjin ayi maka alfarmar ka ha'de su biyun ka yi wuf da su.
Sai kuma ka dinga tare ta kana tayar mata da hankali a wofi. Ita ma k'uruciya ce ya sanya take zubar da hawaye akan ka.
Ni yanzu da na fahimci inda aka ajiye ni, na sake yiwa Nasiba kallon soyayya ne? Duk nacin ta bana sauraron ta".
Daga haka ya fice gaba'daya.
Yayin da Ba'kin ciki mai tsananin gaske ya dabaibaye Yaya J.
Ya ce "Ban da ma idonka babu kunya Bulkachuwa har ka iya tsayawa ka ce zaka fa'da wa wani dai-dai?
Ina ka santa, ai kanka zaka fara yiwa bitar gaskiyar kafin wani, wanda tsoron Allah baya iya hana shi aikata kaba'ira, shine zai yi kishin ana bata wa wata lokaci, kai kuma *BAK'AR TA'ADAR* lalata y'ay'an jama'ar da kake yi fa?
Ko an ce maka daga sama suka fad'o babu mai kishinsu?"

✍️

BAKAR TA'ADA Where stories live. Discover now