chapter 6.

234 35 17
                                    

11&12.
A ki'dime Gwaggo ta ce "Baban Kasuwa ne ya fada miki hakan Yabi?".
Na girgiza kai na ce " A a Baban Tsakiya ne".
"Tirk'ashi"
Gwaggo ta fa'da a hautsine.
Na sunkuyar da kaina k'asa ina jin wani irin al'amarin tashin hankali na ratsa ni. Da kaina nake jin shekaruna sun yi k'aranci na dinga fuskantar irin wannan rikita rikitar.
Na rasa dalilin da ya sanya nake da ba'kin jini a cikin gidanmu.
Hatta a k'ofarmu mak'iyan da nake da su sun wuce misali.
Domin kafatalin y'an d'akin Mama Nazira ce take sona fisabidillahi, sai ko Yaya Salamatu ita ma kuma ba yadda za'a yi alheri ya samu ta doshe ni da shi, sai dai Nazira, tana dai bani kuncen kayanta da suka sha ruwa ainun.
Ni kuma murna nake yi domin tafi sauran yi mini adalci da sassauci.
Mama kuwa da tana da ikon da zata kore ni a gidan da tuni ta yi hakan tsabar yadda ta washi ta bude ido ta gan ni, mussaman yanzu da sana'ata take sake kafuwa.
Y'an dakinmu ne bana fuskantar adawarsu sai dai muna yawan haura wa sama da su a dalilinsu na ce wa ina daga wa Gwaggo hankali tunda kusan kullum sai na janyo mata bacin rai.
Inna kuwa tare wa yaranta fa'da da nake yi ne ya sanya na kubuta daga nata kaidin.
A hankali ta ce "Ai kuwa ribar ha'kurina gashi nan a bayyane tunda ban yarda na tafi na barku kun yi rayuwar ni y'asu a dalilin rashin uwa ba.
Kina gani ina nan din ma ya ya kuka kare ne, bare kuma na zubar da ku na tafi?
Ashe yanzu yadda yayunki suke dawainyar rike gidan nan bai isa abin alfaharina ba?
A bayyane yake kafatalin ya'yan gidan nan ba wanda Babanku yake mora irin yaran dakin nan. Ai kuwa ko iya hakan na ga ni ba abin da zan ce da Allah sai godiya. Domin wasu da yawa yaran nasu basu amfani kansu ba bare waninsu ya amfanesu.
Ubangiji ba abin da bai yi mini ba, na gode masa, kema na hore ki ri'ke ha'kuri ba abin da hakuri ba zai baki ba.
Ta ri'ke kaina ta ce "Àllah ya miki albarka, ya sassauta miki al'amuranki.
Ina fatan Ubangijin da yake sarrafa zuciya, ya sarrafa taki ta zama mai sassauci da afuwa".
Kuka ya k'wace mini sosai ina cewa "Ameen Gwaggo".
Ba komai yake sanya ni d'imuwa ba irin maganar Baban Tsakiya.
Maganarsa ishara ce akan aurena da Yaya J ba zai yiwu ba.
Zuciyata ta yi nauyi ainun. Na shiga rud'ani mai yawa, na sani idan har zan yi aiki da lura kamata ya yi na nisanci d'ansa tunda har yake neman maraba da ni a cikin gidanmu, ina kuma ace na zama cikin ahalinsa?
Mutumin da bakinsa yake ambaton jaje da alhini ga ahalin wanda d'ansu zai kwashe ni.
Bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da fashe wa da matsanancin kuka.
Saboda fishin Baban kasuwa ya sanya Baban Tsakiya tsayawa ya mini irin wannan tozarcin da zai yi wahalar gaske na sake ganin girmansa.
Na samu kaina da tambayar anya kuwa Babanmu ba dan uba ba ne a tsakaninsu?
Sai nake ayyana ai ko y'ay'an Baffanni suke (cousins) bai kamata su dinga yi masa irin wannan kaskancin ba, dan kawai sun fishi wadatar abin duniya. Balle kuma girman nasaba irin ta uba guda, sai dai kuma babu haufi cikinsu daya ma'ana Dada ce ta yi nakudarsa tun gabbannin a yi tasu.
Babban farin cikina d'aya, bai rasa wadatar zuciya ba, tunda duk tsananin wahala ba zai bu'de baki ya ce su taimake shi ba.
Idan sun yi niyya akan kansu sun yi masa kyauta to zai kar'ba, amma idan zamu kwana mu yini bamu ci ba, ba dai ya ce wane ga halin da nake ciki ba, sai dai idan ya'yan cikinsa ne.
Har ya k'wammace ya fa'da wa aminisa Alhaji Tanimu tsananin da yake ciki, ya tsananta.
Matu'kar kuma zai fa'da masa to kuwa zai sauke masa buhun masara, dawa, dana gero.
Sau tari kallon wadatar da ake yiwa su Baban Kasuwa yake hana masu k'arfi tallafa wa Babanmu.
Sannan mutanan yau suna da dabi'ar k'in taimaka wa matu'kar ba ro'konsu ka yi ba, yayin da mafi yawa aka fi taimako da azumi, shima fake wa ake yi da sunan neman lada alhali a ku'din zakkar da Allah ya wajaba a fitar ne suke siyan kayan abinci suna rarraba wa.
Oh mutanan yau mun rungumi *Bakaken Ta'adodi* daban daban.
Allah ya shirye mu kawai.
Muryar Inna na ji cikin sigar umarni ta ce "Ki cire Jabiru a ranki, nasan zai yi matu'kar wahalar gaske wannan al'amarin bai zama sanadin yin shamaki a tsakaninki da shi ba.
Ina son ki ninka jarumtar ki, tun kafin su miki 'kwalele da shi."
Kafin na bu'de baki sai ganin Baban Marina muka yi ya shigo a fusace yana fa'din "Ina Asiya?"
Da rawar murya na ce "Ga ni Babanmu".
Ya ce "zo ki fice ki bar mini gida tunda har zaki iya tsaya wa gar da gar ki zagi Badamasi da Iliya akan idonsu.
Ai bansan zaki iya irin wannan dib'ar albarkar ba. Na dauka abin naki akwai lissafi a ciki amma tunda kina ganin idan kin yi karo tsakanin kwai da dutse zai miki daidai sai ki je ki yi a wani gidan, amma ba a nan ba.
Ban haifi d'an da zai zagi dan-uwana akan idonsa na bar shi ba.
Na sha fa'da miki babu ruwan ki da shiga tsakanina da y'anuwana.
Amma sam kin k'i ji"
Cikin kuka na ce "Ka yi ha'kuri Babanmu!
Ba yadda aka fa'da maka al'amarin ya kasance ba. Ban zage su ba, har abada kuma ba zan zage su ba, kada ka kore ni a gidanka, zai iya zama sanadin tabarbare war al'amura masu yawa, ka mini dukkan hukuncin da zaka gamsu. Ka taimaki kanka, ka kuma tserar da ni fa'da wa halaka akan wad'anda basa nufin ka da alheri".
Ya jijjiga kai ya ce "Yabi ki yawaita hamdala da baki zo a cikin mutanan farko ba, lah shakka da irinku ne masu kafiya akan ra'ayinku ko da ya ci karo da gaskiya.
Na ji ba zan kore ki ba, amma dole ki yi nisa da gidan nan tun ban fusata na miki baki ba, tunda ba'kin cikin da kika cusa mini a sanadin musayar yawun da kika yi da iyayenki ba mai sau'ki ba ne, akan kannena mahaifiyata take mini mugun baki. Yabi kibi a sannu fa."
Na sake tsorata na ce "Àllah ya huci zuciyarka Baba, Allah ya shiga cikin al'muranka, ya iya maka da iyawarsa".
Nan da nan ya sauka ya hau fa'din "ameen".
Gobe ki shirya ki tafi gidan Salisu har sai na nemi ki, saura can din ma ki nemi gigita masa zaman lafiya a gidansa, dan nasan zaki gano masa laifukan da iyalinsa take yi wanda shi yake yin uzziri a cikinsu".
Na yi kasa da kaina na kasa cewa komai.
Washagari kuwa Gwaggo da kanta ta shirya mini kayana a ledar biba tana ta jaddada mini idan na kuskura na yi rikici da matarsa to ba tantama da ita na yi.
A sanyaye na ce "Komai zan ga ni zan runtse idona babu ruwana, ko da kuwa zata tsokane ni."
Wani irin salama ya shiga Gwaggo ta dinga fa'din "Yauwa Yabina Allah ya sassauta miki".
Anas ne ya fara yi mini gaba da kayana.
Yayin da zamu tafi da Nazira da Iki idan anjima.
Nazira sai kuka take akan tafiyar da zan yi na barta.
Na yi shirin zuwa gaida Dada wanda rashin zuwa wannan gaisuwar ba k'aramin abu take mayar da shi ba.
Babu kuzari na ce "Nazira mu je mu gaida Dada".
Ta girgiza kai tare da cewa "je ki kawai, bana jin dadi anjima na leka".
Na ce "Tom na tafi, ina jin da'di tare da k'arfafa wa kaina guiwar ko na rasa soyayyar kowa a fuskar zumunci ina da yakinin ba zan rasa soyayyar Nazira ba.
Tana sona fiye da zatona, haka nima nake sonta tamkar yadda nake son shakikiyata Yaya Ummi.
Tun daga bayan katangar Dada nake jin tashin muryoyinta da na Ya'yanta
Na karasa har cikin soron sosai na dinga jin kumfar bakin da Baba Maryo uwar Nasiba take yi akan ba zata ta'ba yarda a dauki Nasiba a bawa Tijjani ba.
Kuka take yi wiwi. Tana cewa "sai dai a ga laifina a banza, amma wannan ha'din ba mai yiwu wa ba ne."
Yayin da Babah ta Bulkachuwa take fa'din "Ai ban ga laifinki ba,  gaskiyar magana kika fa'da.
Kuma dama mutum shi yake mutunta kansa, da ya nutsu ya zama mutumin kirki ina ce a ko ina zai nemi aure a ba shi?.
Yanzu kuwa da ya zama abin da ya zama a cikin danginsa ma gudunsa za'a yi bare a waje".
Dada ta ce "Ya isa haka, ba cece-kuce zaku yi mini ba.
Na rufe wannan maganar, na yi zaton auren nasa da ita zai kawo masa dai-daito tunda tana sonsa, idan aka yi sa'a sai ya shiryu, ruwan wankan aure ka'dai maganin wanda ko wacce suka fand'are ne. Amma tunda abin zai zama tashin hankali a bar maganar haka nan
Nasiba ba matarsa ba ce."
Kafin na yi wani motsi sai jin muryar Baban Tsakiya ya yi yana fa'din "Kazalika wannan yar iskar yarinyar ba matar Jabir ba ce, ko bayan raina idan aka bari ya aure ta Wallahi Allah ya isa, na fa'da a gabanku, kuma yanzu ma idan na tashi zan je na sami Yaya Sani na tabbatar masa babu maganar aure, mun gama magana da Iliya, Maijidda zai aura.
Domin ba zan yadda ya dauko mini majuniniyar yarinyar nan ta zo ta tarwatsa mini zuri'a ba".
Daidai lokacin na yi sallama na gaida Dada sannan na gaishe su a jamma'u.
Babar Bulkachuwa ce ta amsa cikin karfin hali tana danne bacin ran da ya ke kutso mata.
Nima na yi jarumtar cewa "Ashe kin zo Babah?"
Ta ce " Na zo dazun nan kin san sammakon zuwa nake yi saboda motar Jos muke shigowa.
Na yi yake na ce "Sannu da zuwa".
Na mike da nufin tafiya sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Dawo ki zauna.
Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata.
Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da saba'a zaku bar gidan nan".
Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?"
Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi?
To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba."
Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan.
Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya, to ku musanya wa Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya ko sharholiyar da ni nake yi".
Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma, Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa".
Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so, shi kuma har yana kora ta saboda ku.
Ba komai Ubangiji ya sanya alheri".
Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi da furucina.
Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai majununai".
Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi gaban mari, kannen ubana ne, ta ko wacce fuska idan na yi musayar yawu da su ni ce bani da gaskiya. Sai kawai na had'iye.
Ina fitowa na yi kicibus da Bulkachuwa yana tsaye da buta a hannunsa, tabbacin daga bayi ya fito.
Na tabbatar kuma ya ji komai har maganganun da aka yi a kansa da Nasiba.
Domin gaba'daya manyan idanuwansa sun kad'a, sun yi jajur.
Na wuce shi ban sake kallonsa ba, kallonsa ka'dai ya sanya na ji tamkar na yi amai tsabar yadda na washe shi.
Wannan abin da na yi ya sake ki'dima wadannan bayin Allah domin dukkansu ba wanda maganar bata shige shi ba.
A ranar na koma gidan Yaya Salisu ban san wainar da ake toyawa a gidan Marina ba.
Zama nake yi irin na taka tsantsan a gidan, ba dan komai ba sai togaciyar da aka yi ta yi mini a gida.
Da safe zan yi wanke wanke da shara, na yiwa dansu wanka shi kenan sai na shige daki.
Idan ta gama abinci zata mini zubin auki.
Yadda nake gudun bata mata, hakan ita ma take kaffa kaffa dan kada na ga beken ta, ko idan na koma gida na bada ba'kin labari a kanta.
Ranar da na yi kwanaki hudu sai ga Nazira da Iklima.
Muka yi hira, sun kusa tafiya Nazira ta ce da Iklima ta fita ta jira ta a waje.
Ba musu Iki ta fita.
Ta sassauta murya tabbacin bata son a ji maganar ta ce "Kinsan me yake faruwa kuwa a gida?"
Na girgiza kai ina fa'din a ina zan sani Adda Nazi?"
Ta sake yin kasa da murya ta ce "wata yarinya ce ta yi cikin shege har ta kusa haihuwa fa, to ana ta shari'a, da ta lissafo wadanda suke mua'amalantar ta har da Yaya Bulkachuwa yanzu haka kullum sai sun je kotu".
Zuciyata ta harba da tsananin gaske, na ce "Tijjani gaskiya baya kyauta mana, gaba'daya sai ya gama ruguza darajar gidanmu alhalin shi ba dan gidan ba ne".
Nazira ta ce "Hmm abin sai ha'kuri ba ki ga yadda ya zama ba, ya kuma kafe akan ciki ba nasa ba ne ba zai kar'ba ba. Babah ta Bulkachuwa ita ma ta zama abin tausayi sosai tsabar ba'kin ciki."
Hawaye ya balle mini wata irin damuwa ta shige ni, kishin zumunta ya murde ni, ko yaya ba zaka so ganin jininka a cikin tozarci ba.
Mun jima a hakan kowa da k'wallarsa ta ce "Jiya Malam Yunus Econs ya aiko a bashi izinin neman aurena kinsan tunda matarsa ta rasu a wajen haihuwa har yanzu bai sake wani auren ba, ga yaron nan tuni ya shekara biyu."
Na ru'ko ta ina fa'din "Kai na yi murna sosai Allah ya tabbatar da alheri mutumin kirki ne, na amince Adda Nazi ta so shi ta bashi dama, Allah sanya albarka a tafiyar".
Muka fito ina musu rakiya tana ce wa "Abdul sau uku yana zuwa amma Baba bai bari an fa'da masa inda kike ba."
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

BAKAR TA'ADA Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon