15&16.
Bulkachuwa ya juyo ya ce "Tir da masu gori, Albarkar Annabi ba zaka samu Asiya Toro ba, tunda kallon kitse nake yiwa rogo, marar mutunci kawai".
Ya juya ya yi tafiyarsa a tunzure.
Ya juyo da nufin yi mini magana sai kawai na d'aga masa hannu na ce "Kada ka ce mini komai Yaya J.
Wannan maganar fa, gaskiya ce tsagwaro.
Na roki arzikin ka bar ni na ji da damuwata".
Na juya na tafi.
Na bar shi yana fa'din "Kaicon Bulkachuwa, ko har yaushe yasan mutuncin gaskiyar da har yake wannan zugar?"
Ina shiga d'akin Gwaggo na zube na fashe da kukan da ya ja hankalinta k'warai da gaske.
Ta jani jikinta ta ce "To mene ne kuma?
Kin yi k'ok'ari, kin yi ha'kuri, sake daure wa mana, komai zai wuce fa".
Na saka hannuna na rike ta sosai, baki na rawa na ce "Yi mini addu'a Gwaggo, ki yafe mini bacin ran da na yi ta sanya ki.
Ina jin mutuwa zan yi."
"Ba zaki mutu ba Yabi.
In sha Allah! Ubangiji ba zai bar ki hakan ba, ai yasan an zalunce ki, amma daure ki cigaba da nuna jarumta, ki cigaba da sha'aninki tamkar baki da wata damuwa."
Na ce "Abin ne yake neman fin k'arfina".
Na fa'da, kuka na sake kwace mini.
Ta dinga bubbuga bayana tana fa'din "yadda aka yi din ne akwai tozarci a ciki, amma ni dama bana son wannan ha'din domin tsananin da zaki fuskanta mai girma ne. Allah ya sa haka ne mafi alheri.
Share hawayenki ki d'oro alwallah ki yi ta nafila tunda hantsi ne yanzu."
Na kuwa mike ina share idon nawa, na fita da zummar yin alwallah.
Na dawo na tarar da ita, tana ganin kayan da suke cikin ledar.
Leshi mai kyau, da mayafin da ya dace da shi, da doguwar riga abaya, da takalmi da jakarsa, sai tarkacen sark'a da abin hannu ga kayan kwalliya da turaruka.
Da envelope mai dauke da wasika da kudin dinki.
Gwaggo ta ce "Wannan kaya masu daraja haka? Ajiye wa za'a yi sai Babanku ya ga ni".
Na tayar da sallah ban ce komai ba.Mama da zata dafawa Nazira kazar aure har da Maijidda ta hada ta dafawa.
Ina kallo yadda ta samo tattabaru ta hada da saiwowi ta sake dafa musu. Haka Gwaggo ta maze kamar bata gane ba.
*Mai bukatar saiwowin dahuwar kaza ko na tattabaru da sauran kaya na mussaman ta mini magana akan lambata 08032773332*.
Ina ji, ina ga ni aka daura auren Yaya J d'ina, da Maijidda.
A ranar kam buya na yi, a makwabta na yi kukan da ban ta'ba yin irinsa ba.
Na dinga jin wani irin abu tamkar zai fasa mini zuciya gaba'daya.
Fa'di nake "Ya Allah! Ya Allah".
Idan na tuna nagarta da sanyin halinsa sai na ga ba karamar asara na tafka ba, wacce na saddakar ba zan mayar da irinta ba.
Har dare ba wanda yasan inda nake, sai da na ji dirin isowar motar daukan amare sannan na fito.
Dan ba zai yiwu ace ban raka Nazira d'akinta ba.
Da na fahimci Nazira za'a fara kai wa domin motocin kai ta ne suka fara iso wa sai kawai na fa'da daya daga cikin motocin.
Sai a dakinta muka ha'du.
Duk yadda ta ke lullube a cikin mayafi said da ta riko hannuna ta ri'ke gam tana sake kankame shi tabbacin farin-cikin da take ciki bai sa ta manta tawa damuwar ba.
Sai da kowa ya watse aka bar ni da ita, domin dai bamu da wasu kawayen da zasu kai mana dogon dare.
Ta kalle ni ta ce "Mu yi ha'kuri Yabi, kara daure wa, idan muna ganin ki a hakan ba wanda zai samu sukuni. Kinga ma yunwa nake ji, tun jiya da muka ci abinci ban sake saka komai a bakina ba, ba wanda hankalinsa ya kai a bawa amarya abinci, na sani da kina kusa da ni da kin bani".
Na ce "Afuwan Adda Nazi, amma ai yanzun nan Malam Yunus zai shayar da ke nama da madara".
Ta galla mini harara tare da fa'din aku sarkin magana".
Na mike domin na ji ana fa'din mai motar ya dawo.
Da k'yar ta bar ni na tafi, tana kuka, ina yi.
Kwanaki ukun da suka biyo bayan bikinsu Yaya J sun fi ko wanne tsauri a gare ni.
Sa'ar da na yi ma ba a gidan aka yi masa gini ba, a can bayan gari ne da kansa ya gina abinsa sai dai da tallafin Baban Tsakiya.
K'aramin gida mai fasali na ban sha'awa, ba burin da banci akan wannan gidan ba. Ko bandakin gidanmu da yake sani takaici, da zarar na tuno bandakina a cikin daki yake a gidan Yaya J sai komai ya wanke mini, na yi ta zumudin zuwan lokacin da zamu yi aure, ashe dai wasikar jaki nake tsara wa.
Tayals a ko ina, ga furanni har da fasadabir ya shuka mini, ga bishiyar mangawaro da ni na bayar da kwallon ya shuka, ita ma ta kama sosai.
Amma tashi guda aka ruguza mini komai, Maijidda na cikinsa an kuma sake kawata mata gidan da kayan alfarma domin takanas aka tafi Jos aka siyo mata furnitures, ko yaran Baban Tsakiya su Firdausi basu samu gatan ta ba.
Haka na dinga rama tamkar ku'din guzuri.
Ban samu sassauci ba sai da aka doshi kwanaki ashirin da auren a dalilin na koma zuwa makarantar boko mun shiga aji shida.
Da k'yar Dada ta bari muka koma.
Gaba'daya na zama shiru shiru, idan ba kure ni aka yi ba, na daina fa'da, ko yara na gani sai dai na rabasu na yi musu sulhu. Amma na daina rama wa wani duka, bare ni na doku da kaina.
Duk da yadda na canja ba yaron da yake kuka sabo da ni, ban tsira a wajen mutan Gidanmu ba. Gaisuwata da kyar Baffanina suke amsa wa. Na rasa laifina, zamu gansu tare da Nasiba mu gaishe su, su amsa ta ta gaisuwar cikin walwala har suna ambaton sunan ta amma ban da ni.
Na fa'dawa Gwaggo ta ce "Na cigaba da gaishe su kada na gaji suna da hakkin na mutuntatasu.
A sanyaye na ce "Gwaggo ni bani da hakkin su sakar mini fuska su mua'amalance ni da mutunci tunda jininsu ce ba agola ba?
Nasiba fa ba yar gidan nan ba ce, amma ace ta fini a wajensu?"
A duk sadda na yi mata wannan k'orafin dauke kai take yi ta ce "To ai laifukan da kika yi musu ne, da yawa, sannan ita Nasiba ko ba y'ar gidan ba ce amma tana da wata alfarma tunda a ko ina ana son y'ay'an da yar'uwa mace ta haifa, ke ma ai har da halin ki ya sanya suke yi miki hakan".
Idan ta fa'di hakan sai kawai na kalle ta na yi shiru, domin na sani ta fa'da ne dan kawai na fahimci girmansu. Ba dan suna yi mini adalci ba.
Har sati uku sannan na warware na rungumi zuwa makaranta duk da karatun ma sai a hankali saboda kewar Nazira na damuna.
Dada kuwa fa'di take na fito da miji domin wanda za'a bawa Nasiba ya ce "Kowanne lokaci zai iya gama gidansa ba sai bad'i ba, ita kuwa ranar auren Nasiba ita ce rana ta, ko na fito da miji, ko a bani Malam Nata'ala shine damo sarkin ha'kurin da zai jure wa dukkan iya shegena.
Malam Nata'ala dattijo ne da yake zaune a unguwarmu mutumin kirki ne kwarai da gaske matansa biyu da yara da dama, tsanagaya ce da shi ma'ana Malami ne mai almajirai.
Ban wani dauki maganarsa da Dada ta ambata da muhimmanci ba, illah k'anzon kurege.
Kwanci tashi asarar mai rai har aka cinye kwanakin wata da auren su Nazira.
Har lokacin kuma ban yarda na je gidanta ba duk nacin aikar da take akan tana nema na.
Ikilima ce take zuwa akai akai duk sadda ta je kuma akwai abin da zata bata ta kawo mini na ci ko na sha.
Ga wasiku birjik tunda bani da waya duk da an kawo mini har uku amma Baban Marina ya ce "Baya son mu ri'ke waya.
Duk yadda Yaya J yake nacin mu hadu gaba'daya na tsike zuciyata, domin yanzu haushinsa nake ji ba ka'dan ba.
Kan dole ya koma makaranta tunda ya kammala sawes din da yake yi a Jos.
Ina cikin wannan yanayin da na cire komai a raina nake iyakacin bakin kokarina wajen mayar da hankali a karatuna, sai dai ba wani fahimta nake sosai ba.
Na dai yi sa'a zan iya karatu da rubutu.
Na gama fahimtar ni din basirata a wajen kirkirar abin ado ne, misali idan na samu kan mace mai gashi zan b'ata lokaci na yarfa mata kitson da kowa sai ya ce "wow".
Haka kuma duk gunjin gashi sai na kitse shi, zana adon lalle kuwa tamkar wanda aka bu'de mini ido.
To yanzu da nake sake koyon kwalliyar da ake ya yi, ban jima da fara koyo ba amma har hannuna ya fara fa'da wa.
Dan haka na daina takura wa kaina sai dai ina ta kokari dan na samu na ci jarabawar kammala sakandire.
Ranar asabar tun safe nake ta murnar zan je gidan Nazira, tunda muka zo duniya bamu ta'ba rabuwa na lokaci mai yawa haka ba.
Mutum uku kawai na yarda zan yi wa kitso, duk masu zuwa lalle kuwa ha'kuri nake basu, sai d'aya da take unguwar Nazira, layinsu d'aya domin Naziran ce ta turo mini ita.
Dan haka na saka mata lallen a gurguje na barta da nufin ta same ni gidan Naziran na yi mata kitso a can.
Da murna nake komai domin Allah ya sani ina son Nazira, ina samun farin-ciki idan ina tare da ita.
Har Malaminmu na tarar yana dakon iso wa ta, ga abinci an shirya mini tamkar wata babbar bak'uwa ta mussaman.
Spaghetti ce da miyar kifi, saboda ita ce favorite dina.
Ga kuma zobo ya sha ha'di an fasa masa k'ank'ara, gefe kuma babbar kula ce shake da pure water da aka jefa masa k'ank'ara yini guda aka yi mini tanadinsa.
Da farin-ciki yake taya amaryarsa marabta ta.
Ta rungume ni tana k'walla da mitar ashe zan iya yin watsi da ita na tsawon wannan lokacin?
Da dariya na ce "Babanmu ne ya ce "Ba zan dinga yi miki sintiri a gida ba".
Malam Yunus ya ce "Ba wani sintiri idan kin so ma ki tattaro kayanki ni bazan gaza ba".
Na yi dariya ina fa'din "Na gode da karamci, Allah ya sanya alheri".
Ya fice ya barmu tare da cewa "Ameen Asiya".
Tunda muka zauna hira muke yi, ba a gama wani zancen ba za'a sake, a kama wani.
Na bata labarin yadda muka yi da Dada akan Malam Nata'ala.
Ta dinga dariya tana tintsira wa tamkar ta samu tab'i.
K'wallar dariya a idonta ta ce "Lallai ma tsohuwar nan, ke ce za'a bawa wannan tsohon?"
Na taya ta dariya tare da cewa "To ba namiji ba ne? Kuma ai ta ga ya dace da ni ne, tunda ana kore mini duk wanda ya zo da niyyar aure na".
Ta yi shiru ta ce "Kawai lokacin yin auren ne da saura, amma ba dai Alaramma ba."
Muka shiga hirar duniya, muka ci abinci, muna santi a fili na ce "Na ji da'din ganinki Addah Nazi, Allah ya kara miki kwanciyar hankali, ya kawo zuri'a dayyiba".
Ta ce "Ameen Yabi! Yanzu addu'ata mafi yawa taki ce Àllah ya kawo miki miji na gari".
Na yi shiru.
Ta ce"Baki amsa ba?".
Idona ya cika dam da ruwa na ce "Baban Tsakiya ya lashi takobin duk wanda ya zo sai ya b'ata ni, ya fa'di munanan dabi'una kin ga kuwa aure ai zai yi mini wuya tunda kanin mahaifina ne yake fa'din munanan kalami a kaina."
Ta yi shiru sai kuma ta ce ",Ba abin da yafi k'arfin addu'a Yabi! Fa'da kawai yake yi ba zai yi hakan ba".
Na hade fuska na ce "bana son haka, wanne irin zance kike yi?
Kema kin san gaskiya, zai yi abin da yafi haka in dai Alle Badamasi ne"
Dariya ta subuce wa Nazira ainun, tana yi tana nuna ni da yatsa tare da ce wa "Ho Yabi".
Tsawon lokaci muna hira tana ta bani labarin aure.
Na dube ta na ce "Ya ya maganar da ake fa'da na ha'duwar farko, ya take kaya wa?"
Ta galla mini harara ta nuna kanta ta ce "Ni kika yi wa wannan tambayar?"
Na k'yal-k'yale da dariya ina fa'din "Adda Nazi manya. Yo wa nake da ita da zan tambaya, kawai fa'da mini Malama".
Ta leka ta ga ko Iki na jinmu, sai ta ga game take yi a wayarta a falo, mu kuma muna uwar daki.
Ta ce "Kawo kunnenki ki ji".
Da rawar jiki na mika mata, ai kuwa ta gantsara mini cizo. Na saki kara a ki'dime.
Ita kuma ta ci magani tana fa'din "Maganin mai son jin almarin da bai shafe shi ba, maganin mai son jin abin da Allah ya sakaye shi, maganin mai son ya ji sirrin da Annabi ya tsine wa mai bayyana shi".
Ai kuwa na fara hawaye ina shesshe ka.
Nan da nan ta hau shafa kafa'data tana fa'din "Yi ha'kuri mana Yabina a hankali fa na yi miki, menene zaki zubar da hawayenki?"
Na zum'bura baki ina fa'din "Mun bata gaskiya! Kuma dan kin zama babba ce ai dai kinsan fa'da na."
Ta yi murmushi ta ce "Ni ban girma ba."
Muka yi dariya gaba'daya.
Sai lokacin wacce na bari a gida da k'unshi, ta biyo ni, akan na yi mata kitso.
Muka fara, yayin da Ikilima ta hau wanke wanke ita kuma Nazira ta hau gyara wajen da muka yi dabdala.
Da zan taho ta hado ni da kayan kwalliya masu yawa har Ina fa'din ta kwashe mini kayan ai.
Da sabuwar doguwar riga da ko sata bata yi ba, da sabon takalmi.
Na kalleta na ce "Ki rage kayan sun yi yawa Adda Nazi".
Ta ce "Idan ina da fiye da hakan baki zan yi Yabi".
Na jijjiga kai na kasa cewa komai na yi gaba na bar Iki tana dauko mini.
Muna tafe ni da Iklima muna hirarmu na ce "Idan kin gaji dai, ki bani na karbi kayan."
Ta ce "zan iya Adda Yabi".
Muna tafe wani Alhaji sai binmu yake a hankali a cikin dankareriyar motarsa.
Duk hon dinsa ban yarda mun tsaya ba.
Har muka je gida, bai fasa ba.
Muka shige gida, ya yi parking.
Dai-dai lokacin Bulkachuwa ya danno kai.
Na shige na bar Iki tana lekensa.
Ba wani jima wa ta shigo da sauri tana fa'din "Adda Yabi wai ke ya biyo. Yaya Bulkachuwa ya fa'da masa babu maganar wani a kanki, ya bashi ku'di, ya kuma aiko shi wajen ki".
Tana rufe baki sai ko ya shigo, daga tsaye ya gaida Gwaggo da Inna yana fa'din "Asiya Toro zo mana".
Na yi kamar bazan kula shi ba, sai da Gwaggo ta ce "Yabi wai Yayanki ba magana yake yi miki ba ne? Ni fa bana son wannan wula'kancin na ki".
Na mike ina fa'din "Shi ai Tijjani kayan haushinsa yawa ne da shi."
Ya yi dariya ya ce "Ashe duk yadda na yi ba'kin jini a wajen Jabir akan ki ban wanke laifina na baya ba?"
Muka dan fita wajen k'ofa.
Ya sassauta ya ce "Kin ga Àllah ya dubi takaicin da aka cusa miki Asiya Toro! Kin zargo babban kifi. Wannan mutumin son ki yake yi da aure, kwamshinan harkokin addini ne na jahar nan, sannan babban dan kasuwa ne.
Mutumin kirki ne, kin ga abin da ya ba ni".
Ya nuna mini rafar dubu guda.
Na zaro ido na ce "Billahillazi dan yankan kai ne Tijjani! Ban da hakan daga haduwa ya baka dubu dari?"
Ya yi dariya ya ce "Kin san istigifari nawa na yi yau kuwa?
Na yi yafi dubu goma, Ubangiji kuwa ya yi al'kawarin warware mana komai matu'kar muka dimanci istigifari har da bude kofofin arziki.
Bana haufi Ubangiji ne ya turo mini arziki ta hannunsa.
Ki yiwa kanki fa'da Asiya kin ga dai ba shiri muke yi da ke ba, amma na fi jin ciwon abin da aka yi miki sama da wanda aka yi mini. Ki saurare shi, ki yi addu'ar zabin Allah.
Idan kin samu nutsuwa ki ba shi dama azo a yi auren ki ko kya samu sau'kin masifar gidan nan.
Nima kin ga wannan ku'din ajiye wa zan yi wani satin zan bayar akai mini ku'din aure, ko wannan yar'uwar ta ki zata shafa mini lafiya".
Na sauya fuska na ce "Nasiba fa bata da laifi Tijjani".
Ya kwabe fuska ya ce "To ai ni kuma ko ita ce ka'dai ta rage a duniyar nan na haramta wa kaina ita. Bulkachuwa bai yi wannan arahar ba, ba za'a ci mutuncinsa, a tozarta shi kuma ya lik'e ba".
Ya mik'o mini dalleliyar waya a kwalinta ya ce "Da caji da kuma layi a ciki ki kunna zai kira ki." Ya hade hannu alamun rarrashi ya ce pls ki saurare shi ko za'a dace".
Na ce "Baba fa ya hana ni rike waya, yanzu haka akwai sabbin wayoyina a ajiye, da wacce Yaya J ya siyo mini, da ta wajen Abdulrashid har biyu. Wai sai na kammala makaranta, ko idan na yi aure na ri'ke".
Ya ce "Wannan dai kin ga Babban mutum ne Yabi, ga shi kowa ya yi masa shaidar nagarta.
Ki boye ta ba sai an ga ni ba, bana son ya kubuce miki. Bauchi zai kai ki, ba zai ajiye ki anan ba, ko ma Abuja. Babbar waya ce ki yiwa Allah kada ki bari ta salwanta".
Ya juya na bi shi da ido ina raya ina ma yadda ake zuba masa kyakkawar sura kuma cikakkiya haka yake da kyakkawar dabi'a da nagarta.
Inda a ce shine yake da dabiun Yaya J da ya zama komai an hada masa.
Mafi yawan lokacin ina yawan ayyana da Yaya J ne yake ingarma kaman Bulkachuwa da an yi namiji tsayayye mai kyakkawar manufa.
Amma halayyar Bulkachuwa shine nak'asunsa, mussaman na yadda yake iya keta alfarmar shari'a yana aikata kaba'ira, ga rashin ta ido, ga shigar iyashege, yau har barima na ga ni makale a kunnensa, gashin kai ya sha tiri (dying) gashinsa mai kyau ne irin na fulanin Bulkachuwa amma ya mayar da shi cibiri cibiri tsabar fitina da son yaudare y'anmatan da ba susan ciwon kansu ba, ga kafiya akan ra'ayinsa, ko k'uda ya shafa masa lafiya wajen naci.
Amma akwai tausayi mussaman idan ya ga kina kuka, to kin karya masa lagonsa, sannan yanzu ya fara sanin kishin kansa har yana taya wani ciwon abin da aka yi masa.
Ashe da ya fita wajen Baban Marina ya raka wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba, ya nemi a bashi izinin fara magana da ni.
Baba ya ce "Ya bashi damar neman yardata, amma idan ban amince ba, ba zai mini dole ba.
Shi kenan sai Alhaji Mustapha Zaki yake zuwa, ni da kaina kunyar yadda nake yar mitsil a gabansa nake yi. Dogo ne sosai yana kuma da jiki, ga tumbi sai dai tumbin bai yi muni da yawa ba, ustazu ne sosai domin ya tsayar da gemun sunnah.
Ku'di yake sakar mini da suturu na alfarma, ga kuma mutunta ahalin gidanmu.
Dada kanta sonsa take yi a dalilin idan zai zo sai ya kawo mata rafar sabbin ku'di, y'an 100, da na 50, da na 20.
Yana cewa gashi ta ajiye canji a hannunta, duk zuwa kuwa. Ga ledar tufa da kilishi.
Nawa kuwa y'an 500 da 200 ne.
Bulkachuwa ya zama magayak'insa.
Kullum sai ya masa kamfen, fa'di yake "Gidan ki daban zai baki Asiya, idan kika yi sa'a ma Umrar bana da ke za'a yi, aikin hajji kuwa tabbas ne.
Ba ruwanki da tsufansa, lallaba ki zai yi.
Ni kaina alherin da nake samu a jikinsa ba ka'dan ba ne.
Kin ga "Na kalli hannunsa da yake karkada wa.
Mukulli na ga ni ya ce "Mashin ya ba ni sabo dal, gwamnatin jahar Bauchi take raba wa matasa, shine ya saka sunana.
Dan Allah Asiya ki so mutumin nan, oh wani hanin ga Allah baiwa.
Yarinya kin tako arziki, na tabbatar Gwaggo data haife ki da akwai wutar Nepa a time din Wallahi.
Na miki murna ma da wannan dan tsurut din bai same ki ba.
Ai ke babbar mace ce, sai manyan maza, amma yana tafiya tamkar iska ta hure, kirjinsa duk bai fi allona na makarantar tsangaya ba".
Na b'ata rai na ce "Yaya J din kake yiwa haka akan bare?
Sannan nima ai y'ar tsurut ce ta ina na zama babbar mace?"
Ya murmusa ya ce "Ba sai na bu'de maganar ba, ke ma kinsan yadda ake miki layi ai akwai sirri na mussaman a tare da ke. Na'kasunki biyu ne tsayayyiyar zuciya, kuma taurarriya, da fitsara, dole handle dinki sai tsayyayen namiji k'arfaffa ba lusari irinsa ba".
Na sake b'ata rai na ce "To yadda kake ganin zuciyata, tasa har tafi tawa tsayuwa da jarumta".
"Ke tafi can, me kika sani? Wai har yau son Jabir kike yi? Tabdi jam lallai so ba k'arya ba ne. Jiya fa na gan shi goye da Maijidda a mashin ina ga d'an yawon shan iska suka fito".
Nan da nan idona ya k'ada sosai hawaye ya cika su ya mike yana fa'din "So sorry Asiya Toro. Ki gode Allah da ya kawo miki Honarable Zaki. Domin da ki yi kuka a inda kike so, gara ki yi a inda ake son ki, da ki yi kuka a gidan cin abinci gara ki yi kuka a gidan daula sosai, domin mu maza da kika ganmu so baya hanamu murza kanku".
Na girgiza kai na ce "Zan amince ne idan kai ma ka yarda
zaka shirya da Nasiba, ni shaida ce akan ba wanda take kula wa saboda kai".
Ya bata fuska ya ce "Kin san Allah?
Zan ci mutuncinki Asiya Toro! Kada ki saurare shi mana, shawara na baki saboda ina nufin ki da alheri, idan baki so ba, ki sallame shi, ki jira wanda zaki dinga kuka a gaban murhun gawayi, da kishiya.
Ga kuma ba'kin cikin da zaki kunsa a wajen ahalinsa, shasha da bata san me ya dace ba".https://arewabooks.com/chapter?id=6504c04660ef31f52af5ad6c
✍️
YOU ARE READING
BAKAR TA'ADA
General FictionMurya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina". Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito...