19&20.
Jin na yi shiru tsawon lokaci a dalilin tunanin da nake ta yi.
Ya sanya Dada ta ce "Yabi da alama zaki bawa Jabiru ha'din kai".
Na yi murmushi na ce "A a sai dai na yi imani Ubangiji ne yake shirya komai, dan haka shi na barwa al'amurana ya yi mini zab'i.
Dama kuma ban k'ullace shi ba domin ba shine ya mini laifi ba, sannan Dada idan har auren Maijidda da aka sanya ya yi ya bar ni, bai zama abin kaico da rikici ba, ashe kuwa nawa auren da yake hak'ilon yi a yanzu adalci ne da tsantsar gaskiya".
Jikin Dada ya yi tub'us tabbacin tasan gaskiya na fad'a.
Da k'yar ta ce "Ana barin halak dan kunya Yabi".
Are yi murmushin da yake nuna ba wananan maganar.
Ta sake ce wa "Kuma yanzu wannan dattijon arzikin sai ki bar shi, duk dawainyar da yake faman yi dake da dukkan dangin ki?"
Na sake murmushi na ce "To ai aure gaibu ne, sannan Allah ne ya gadar wa maza su yi ta hidima da macen da suke so dan su ja ra'ayinta. Abin farin cikin ba rok'arsa nake yi ba, haka nan wani nawa bai ta'ba rok'arsa ba."
Ta yi shiru ta rasa me zata ce kuma.
Sai ta hau addu'a da kamun k'afa a wajen Shehu kada zuri'arta ta rikice a dalilin wannan al'amarin.
Har k'asan raina da al'amarin zai yiwu ba wani nauyin da zan ji, domin nawa ne aka k'wace mini saboda kawai zuciyar ahalin gidanmu a cike take da gilli da ba'kin ciki mai yawa.
Kwanaki biyu kullum sai na ga Yaya J ya zo gidanmu, kusan a nan yake yini, ba shi k'ofarsu ba shi a wajen Dada.
Rashin sukunin da nake ga ni a tare da shi, ya tabbatar mini kasafin ya cud'e fiye da zatonsa.
Bai kuma neme ni ba.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa har aka samu kwanaki bakwai babu tartibiyar maganar Yaya J.
Dama na sani mawuyacin abu ne su amince, sai dai dan ya ce zai iya ha'diye gatari ne, shi yasa na sakar masa k'ota ko zai dace ya ha'diye, bayan ya sha kakarin tagwaitakar riskar ajali.
Ina cikin wannan yanayin sai ga wani b'acin ran, gidan da Bulkachuwa ya tura su Baba akai masa ku'din aure suka shafa wa idonsu toka suka ce basu san wannan maganar ba, ba zasu dauki y'arsu su bawa wanda aka bulale a bainar nasi bisa k'azamin laifi irin wannan ba, kuma marar tartibiyar sana'a.
A sanyaye su Baba suka dawo babu kuzari.
Dukkan iyayenmu ukun nan sun ji ciwon abin da aka yi musu. Amma ba wanda ya hango irin wannan tozarcin mai ciwo suka yiwa Babanmu ta hanyar hana Yaya J aure na.
Shi kuma Baban Kasuwa ya dauki tasa y'ar ya ba shi.
A gabana Baban Marina yake yiwa Bulkachuwa bayanin halin da ake ciki, cikin alhini da bacin rai.
Ba wata damuwa mai yawa ya ce "Babu damuwa Baba! Ban damu ba, domin an hana ni aure a cikin gidan nan ma. Dan haka dan waje sun hana ni ba zai zama abin kaico ko tashin hankali a gare ni ba.
Ciwon da nake ji daya ne! Da na yarda da hukuncin Allah. Na amince aka mini bulala sai kuma na zama abin k'yama a idon al'umma.
A wauta ta imani na yi, domin na yi biyayya ga abin da Allah ya zartar ba tare da bin ra'ayin turawa na yiwa hukuncin Ubangiji tawili ba.
Na sani na yi laifin da ku kanku na zubar da darajar gidanku, amma ina yiwa Allah kyakkawan zato zai katange ni daga sake aikata wa tunda na yarda da hukuncinsa, na zabi tereren duniya akan na lahira.
Matu'kar kuwa mutane zasu ci gaba da nuna irin wannan *BAK'AR TA'ADAR* Akan mai laifin da ya d'aura d'amarar taubatun nasuha ba shakka zasu dauwamar da mutum cikin b'ata, tunda idan ya dawo kan sahihiyar turba, ba zasu karbe shi ba, ba zai tsira daga yamididinsu ba."
Baba ya kasa ce masa k'ala domin jikinsa ya yi sanyi da kalaman na Bulkachuwa.
Ni kaina da nake gefensu ina wa Baban Marina wanki ba k'aramin sanyaya jikina kalamunsa suka yi ba.
Na sani gaskiya ya fa'da, hana shi aure da ake yi kuma ba shine mafita ba, illah bashi lasisin sake dulmiya cikin zunubin da ake k'yamarsa.
Baya ga hakan basu taimaki y'ay'ansu ba, tunda dukkan y'anmata nasa da aka hana shi auren su sonsa suke tamkar su bashi kyautar kansu, ashe kuwa idan ya so lalata rayuwar yaran nasu cikin ruwan sanyi zai yi hakan, tunda Ubangiji ya kyautata masa halittarsa k'warai da gaske .
Dan haka zai iya amfani da son da suke masa ya lalatasu a banza, idan kuma hakan ta faru zai yi wahalar gaske ya karbi aurensu domin komin lalace war namiji baya son lalatacciya. Cigaba aka samu ko tabarbare wa?
A wannan rana na fahimci ashe cikakken mutum ne mai nutsuwa, kawai sharholiyar ce ta yi masa k'awanya.
Ya katse shirun da Baba ya yi ta hanyar ce wa "Baba na gode sosai, zan cigaba da istigifari, idan al'amura suka sake daidaita mini zan fara sana'a, zan je Bulkachuwa na nemi aure ina da tabbacin a dangin mahaifina ko nafi hakan lalace wa zan samu mai k'arfin halin da zai bani aure tare da fatan auren ya zame mini sanadin shiriya da bud'ewar arziki."
Ya mike ya tafi yana sake godiya sosai.
Ajiyar zuciya kawai Baban Marina yake yi, na lura ba k'aramin ki'dima ya shiga akan al'amarin ba.
Murya babu amo ya ce "Yabi idan kina son Alhaji ki ce masa ya turo wakilansa, idan kuma ba kya sonsa to ki fa'da mini zan sallame shi".
Na yi k'asa da kaina na kasa amsa masa, daga haka kuma sai ya fita, na bishi da ido amma tunanin a yadda jikin Baba ya mutu murus akan al'amarin Bulkachuwa da ace Adda Nazira ba ta yi aure ba, Babanmu na iya juya wa nak'asunsa baya, ya bashi auren ta.
A fili na furta "Alhamdulillah da Allah ya sanya ta yi auren ta ta barranta da auren tantiri ma'abocin *BAKAKEN TA'ADODI*.
Haka kawai sai zuciyata ta buga da tsananin gaske, a dalilin ayyana wa da na yi, wata'kila fa idan ban tsayar da miji ba, Baba yana iya cewa ya bashi ni.
Nan da nan na tsirtar da yawu saboda kyankyaminsa da ya taso mini.
Gashi dai zabgegen saurayi ne dogo cak mai murdadden jiki tamkar ya fito cikin Kyawawan Tirkawa(Turkish).
Amma kwata kwata baya burge ni duk da farar fatarsa da bak'ar sumarsa, da suke rudar y'anmata.
Asalima Y'ar tsama muke yi, sassaucin rikicinmu a dalilin kwamshina ne, domin sosai yake yi masa alheri.
Ya karbi takardunsa, samun aikin ne dai shiru, amma ana saka rai tunda kwamshina baya wasa kuma mutuminsa ne. Tuni Yaya Salisu ya samu aiki a asibitin Toro a matsayin accountant na asibitin tunda dama bangaren ya karanta.
Yaya Rabi'u da Bulkachuwa ne shiru amma akwai kyakkawan zaton suma zai samo musu.
Wananan dalilin ne ya sanya ya daina tsokanata ta hanyar muzanta ni.
A fili na furta "dutse a tsakanina da Bulkachuwa ya Rabb".
Ina wankin ina jaddada wa kaina matu'kar Yaya J bai yi yun'kuri mai k'arfi ba, to nan da lokaci kankani zan bawa kwamishina dama ya fito tun zuciyar Baba bata ayyana masa wani al'amarin da zai iya kassara ni, ya dauwamar da ni a cikin ba'kin ciki mai tsananin gaske ba.
Na kammala wankina.
Mama ta fito ta ce "Yabi anjima zan aike ki gidan Nazira".
A ladafce cikin murna na ce "To"
Domin kuwa ha'din baki muka yi da Naziran, saboda na yi ta tambayar Baba zani gidanta yana hana wa, basan me yasa yake hana ni zuwa ba, amma bai ta'ba yin k'orafin zuwa koyon sana'ar da nake fita ba kullum.
Duk kuwa da ce wa ake yi shargalle nake yi da sunan koyon sana'a.
Shiyasa Nazira ta ce wa Mama ta bani kwanuka na kai mata kar aba wa marar wayo ya yi b'arinsu su yi lamba.
Tunda idan ita ce ta aike ni Baban ba zai hana ba, ba kuma zai tambayi aiken menene ba.
Dan haka a gurguje na shirya na tafi.
Muna zaune ina bata labarin yadda muka yi da J.
Ta galla mini harara ta ce "um um uhum. Ashe dai Yabin bata san ciwon kanta ba. Har wane ne Jabir kuma?
Idonta ya ciko ta ce "Allah ka sanya sai bayan raina zaki zama matarsa!.
Jikina ya sabe da rawa na ce " Addda Nazi!
Cikin gigita domin ban ta'ba ganin fishi mai yawa a tare da ita irin hakan ba, ita din mai ha'kuri ce, mai kuma sanyin hali ce tamkar dai ba daga tsatson Mama ta duro ba.
Murya na rawa na ce "mene ne na wannan mugun fatan Nazira?"
Idonta taf cike da hawaye ta ce "Da kin fahimci yadda na k'yamci al'amarin, da baki zo gabana da wannan maganar mai bak'i tamkar zunubi ba.
Ban iya fishi ba, shi yasa nake kaffa kaffa da duk abin da zai ha'da ni rikici da jama'a, domin ni kaina ina tsoron fishina ina kuma yawaita neman tsarin Allah da shi.
Amma zan fa'da miki, matu'kar kina son ganin fishina da barranta kaina daga al'amarinki to ki cigaba da yi mini wannan maganar da nake fatan ajalina ya riske ni kafin ta wanzu".
Sai ta fashe da kuka sosai.
Cikin kuma kukan take cewa "Yanzu duk ba'kin cikin da aka cusa wa ubanmu, duk yadda aka wula'kanta ki, dan ke ce asararriya har ki kalli dan Baban Tsakiya da sunan soyayya irin ta aure?
Na rantse miki da Allah idan ace Jabir ne ka'dai namiji a duniya gara ki tabbata babu aure, ko ni na mutu ki maye wa mijina madadina da dai Yaya Jabir ya same ki.
A haukanki Baban Tsakiya zai bar shi ne?
Ko kuwa kwantaccen tunaninki ya fa'da miki Baban Kasuwa zai bashi aurenki alhalin tasa y'ar ce matarsa?
Kaico da wannan maganar da kika nufo ni da ita.
Nima cikin kuka na ce ",Takura mini ya yi shine na yi masa gatse dan ya shafa mini lafiya."
Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fa'din "Amma shine kike rawar jikin fa'da mini, idan ba kya so me ya sanya zaki yi mararin sanar mini?"
Ta nisa ta zarce da fa'din "Idan zaki ha'kura da shi ki hakura Yabi. Domin Jabir ba mijinki bane, na tabbatar duk sanyayyar zuciyar Baban Marina ba zai ta'ba bawa Jabir aurenki ba, ban da dai ma mai k'arfin halin jure damuwa ne da kuma kawaici da tuni bai ha'du da ciwon shanyewar barin jiki ba a dalilin abin da yan'uwansa suka yi masa.
Ashe duk zafin ranki, da kishinmu da kike yi a banza ne a kuma fatar baki ce? Wallahi matu'kar zaki nemi zama ahalin gidan Baban Tsakiya ki tabbatar kin fita daga namu ahalin Yabi"
Ta tashi ta bar ni tana kuka sosai.
Jikina ya mutu wato ba k'aramin gaba ba ce ta shiga dangimu ba kenan? Duk ha'kuri da kawaicin Nazira ita ce take fadin tsauraran kalmomi akan zumunta irin haka?
To idan har Nazira mai sau'kin hali da k'ullaci zata yi hakan to ina ga Yaya Ummi shakikiyata kuma mai ra'ayin rikau?. Domin ita hatta zumuncina da Nazira adawa take yi da shi tana ganin ita ce tafi kusa da ni, ita ta cancanci mu yi irin wannan soyayyar, ta kasa fahimtar tazara mai yawa ce a tsakanina da ita, Nazira kuwa tare muka taso tamkar tagwaye, kuma Ubangiji ya jefa mana soyayyar juna duk da k'unbiya k'unbiya irin ta iyaye mata da kishi yake haifar wa.
Bare kuma mazan Gidanmu.
Yaya Rabi'u shine sa'an Yaya J tare suka taso, bayan jini da ya ha'dasu, abokanta suke yi sosai, amma Yaya Rabi'u da kansa bayan an yiwa J aure da Maijidda na ji yana fa'dar bai k'i wani a duniya har cikin zuciyarsa irin Baffanninmu ba, yana kuma fatan kada a k'addara auren zumunci a tsakanin y'an k'ofarmu da tasu ila yaumil k'iyamati.
A sanyaye na bita uwar d'akinta na dinga rarrashinta da k'yar na shawo kanta ta ha'diye kukan nata tamkar yarinya y'ar k'arama haka ta koma mini.
Wannan yinin bai yi wani armashi ba tunda zuciyarta ta riga ta baci.
Har na dawo gidanmu a takure nake jin kaina, domin ban ji da'din yadda Nazira bata sake mini kamar yadda nake so ba.
Na iso gida na tarar da Yaya J gurfane a gaban Baban Tsakiya kansa a k'asa da alamun kuka yake yana fa'din yayi masa alfarma ya bar shi ya yi abin da Allah ya hallata masa.
Ba sassauci ko nauyin ganina ya ce "Na gama magana idan baka gamsu ba, ka je ka nemi wanda zai shige maka gaba, babu damuwa, amma fa babu albarkata a ciki".
Na shige da sauri, ina ambaton "Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun".
Ina shiga gida sallar almuru kawai na gabatar na dauki waya na k'ira kwamishina na ce "Baba ya ce ka turo waliyyainka".
Ya dinga murna yana sanya alheri da albarka, tare da addu'ar Allah ya sanya yadda na aminta da shi, kada ya kunya ta a idona.
Na ajiye wayar ina mamakin ni kuwa a duniya me na tsare wa Baban Tsakiya ne?
Na dinga Jin haushin kaina yadda na makance ina son Jabir! A yau na yarda na gamsu tazarar da take tsakaninmu tamkar tazarar sama da kasa ne .
Ba zan ce bana son Yaya J ba, domin kuwa ikon zuciyata ba'a hannuna yake ba.
Amma na yarda da maganar Nazira ko shi ka'dai ne namiji a duniya to haramun ne a gare ni.
Bayan Baban Marina ya dawo gida bayan sallar isha a tsakar gida Inna ta shimfida masa tabarma a dalilin zafi da ake fama da shi.
Ya kammala cin abincin da ta gabatar masa kenan.
Ya kalli ni duk da muna da tazara ya ce "Yabi zo nan".
Zuciyata ta harba da tsananin gaske.
Na matsa kusa da shi kamar yadda ya yi mini umarni.
Babu sukuni ya ce "Ya ya maganar Alhaji?"
Kaina a kasa na ce "Na isar da sakon na ka".
Ina rufe baki ya ce "Madallah da Yabi! Ubangiji ya tsare ki, ya sanya albarka a dukkan sha'aninki".
Farin-ciki ya mamaye ni, na amsa da ameen da karsashi.
Ya sallame Ni.
Na shiga dakinmu na tarar da Gwaggo tana ta kulla siganta hankali kwance.
A zuciyata ina ta jinjina mata na yadda bata raina riba duk kanknatar ta.
Domin sigan nan mafi yawa sai ta yi ciko duk sadda za'a auno mata.
Idan na ce ta bari, sai ta ce da bata siyar wa, da ba zamu sha yadda muke so ba.
A hankali na ce "Sannu da kokari Gwaggo! Allah dai ya nuna mini ranar da zan hutar da ke zaman kullin sigan nan dan kawai mu saka siga a koko ya ji".
Ta yi murmushi tana fa'din Yabi da dogon buri kike, dama ana wuce yin sana'a ne?
Na ce "Indai bata kawo ku'di ba.
Ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba.
Na bu'de baki zan yi maganar sai kawai muka ji sallamar Yaya Jabir a tsakar gidan.
Baba ya amsa masa tare da cewa "iso mana Jabiru".
Ya zauna a tabarmar ya gaishe shi cikin nutsuwa.
Baba ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa iyali da karatunsa.
Tsawon lokaci Yaya J bai iya cewa Baban komai ba.
Sai Baban ne ya ce "Akwai matsala ne Jabiru?".
Cikin rauni sosai ya ce "Baba so nake ka bani Yabi na aura".
Zuciyata ta buga, na yi matu'kar kasa kunne a kansu, ko kwakkwaran motsi bana son yi.
Hatta Gwaggo tsaya wa ta yi tana saurare.
Murya da walwala Baba ya ce "Jabiru ka zo inda za'a yi maka komai, ina tabbatar maka da a ce a wani wajen kake son auren da na je na nemo maka.
Sai dai da yake y'ar tawa ce shiyasa bazan iya komai ba. Kana da siffar da za'a baka aure babu haufi. Amma akwai mishkiloli da baza su bari na baka Yabi ba.
Farko matarka da take hannunka itama y'ata ce da kanina ya haifa. Kasan kuma matan yau basu dauki lamarin kishi da sassauci ba. Ha'dasu kishi zai iya ruguza komai ya mayar dasu abokan gaba, sannan zuri'armu zata dare ne, wasu na bawa Yabi kariya, wasu na bawa Maijidda.
Da ace Yabi ka fara aura, ka zo kana son Maijidda daga baya to ina tabbatar maka da sai inda karfina ya kare, domin ina da tasirin da zan lank'awasa ta a zauna lafiya. Amma tunda ka riga ka auri Maijidda a farko, dole a ha'kura da maganar Yabi dan a samu a cigaba da lallaba zumuncin da ya dan yi saura."
Tsawon lokaci ban ji Yaya J ya ce komai ba tabbacin ba haka ya so ji ba.
Murya ba amo ya ce "Baba kai ne tsanin da nake ganin zan taka dan na samu cikar burina."
Baba ya numfasa ya ce "Ai kuwa a wannan karon ba zan zame maka tsanin ba Jabiru.
Domin ina sane da yadda Mahaifinka bai amince maka ba, ka yi kankanta da yawa ka jefa kanka a cikin manyan matsaloli, domin auren da kake son yi ba zaka samu nutsuwa da shi ba tunda babu albarkar iyaye, sannan su kansu matan naka ba gode wa kokarinka zasu yi ba, kullum zaka zauna ne cikin zullumin zarge zargensu."
Yana dasa aya Yaya J ya ce "Zan jure Baba, zan iya, da sannu Ubangiji zai hore mini su gaba'daya.
Sannan ina fatan sanadin wannan auren ya zama silar daidaita al'amura a gidan nan".
Ga mamakina sai jin muryar Baban Marina na yi cikin kaushi ya ce "Jabiru ba zan baka ba, na rok'e ka, kar ka kuma dosa ta da wannan tatsuniyar domin ko mak'oshina bata je ba, bare ta shiga zuciyata.
Bana son na yi maka abin da zaka mini kallon marar kirki, ko na rashin inganta zumunci, amma idan ka cigaba da dagewa to ba shakka zaka sha mamaki, domin kuwa na riga na haramta soyayyarku a zuciyata, dan haka kai ma ka shafe ta domin ba rayayya bace".
Bamu gama fita da mamakin maganganun Baba ba, Yaya J ya sake shayar da mu wani sabon mamakin ta hanyar cewa "To Baba idan kuma Allah bai shafe ta ba, ya raya ta fa?"
Takaicinsa ya k'ume Baba ya kasa ce masa komai domin bai ta'ba zaton Yaya J zai iya fada masa hakan ba tunda mutum ne mai biyayya, mai kuma gudun zuciya.
A sanyaye ya ce "Kowa ya ki fahimtar halin da nake ciki, me yasa zaka biyesu wajen yin watsi da zumunci Baba?
Annabi cewa ya yi mu yiwa wanda basu yi mana ba".
A matu'kar zafafe Baban Marina ya ce "To dai ni ne uban Yabi! Ni kuma shari'a ta girmama ta mayar a hakku ya za'ba mata miji, idan kuwa hakane, ko mutuwa ce ta riske ni gabannin na aurar da ita da kaina. To waliyyinta baza su baka ita ba, bare kuma ina fatan a ara mini dama na aurar da ita da kaina. Ka je ka yiwa Mahaifinka biyayya, na gode sosai da soyayyarka. Mu cigaba da addu'a da sannu komai zai dai-daita mana. Amma Yabi kam ba matarka ba ce".
Tsawon lokaci bai amsa ba. Ni dai daga sama na ji muryarsa yana cewa "Sai da safe Baba".
Ajiyar zuciya mai nauyi na ji Gwaggo ta yi tare da cewa "Alhamdulillah! Ubangiji ka sake nisanta wannan al'amarin kamar yadda ka nisanta gabas da yamma."
Na kasa magana, amma dai zuciyata ta yi nauyi, na kuma gamsu da gaske Yaya J yana sona da dukkan zuciyarsa.
Gefe guda kuma ina gasgata tsinkayen Nazira da ta ce Baban Marina ma ba zai bashi aurena ba.
Na k'udire bazan sake bari mu hadu ba, bare zuciyata ta dinga karaya a dalilin ta so mini da soyayyarsa da nake ta kokarin danne wa da dukkan iya wa ta.
Washagari na tashi sukuku ba wanda ya tayar da maganar.
Da yamma sai ga kwamshina ya zo, sai da ya fara zuwa wajen Baban Marina a wajen sana'arsa, ya sanar masa nan da kwanaki biyar zai zuro a yi maganar aure da saka rana gaba'daya.
Shi yake fa'da mini hakan.
A wannan ranar ma kayan da ya kawo mini ba k'aramin yawa ne da su ba.
Tunda ga kan sutura, ga provisions tamkar wacce nake rike da kaina.
Sai kuma dalleliyar waya da zoben gold wai a matsayin tukuicin amincewa da shi.
Tuni Baba ya sallama ya bar ni ina rike waya.
Wadanccan ma da ya rike tuni ya fito mini da abina.
Dama k'ananu ne sai kawai na ce ya bawa iyayenmu mata tunda uku ne dama.
Ni bansan me yake faruwa ba, ashe Yaya J bai fasa sintiri a wajen Mahaifinsa da Dada ba.
Da ya kasa samun tallafinsu, sai kawai ya doshi Baban kasuwa mahaifin Maijidda.
Nan ma fatattakarsa ya yi tare da alwashin idan mummunar k'addara ta afko aurenmu ya tabbata, to kuwa ya kwana da sanin sai dai ya sako masa Maijidda.
Hankali ya fara tashi domin gaba'daya Yaya J ya susuce ya rasa nutsuwa har ta kai Maijidda ta dawo gida a dalilin zaman nasu babu da'di sam, ita kuma ta gaza ha'diye damuwa ta taho, da k'yar Dada ta mayar da ita.
Baban Marina da kansa ya fa'da wa Dada da yan'uwansa cewar ranar asabar za'a zo neman auren Yabi, kada su yi nisa.
Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa suka gabatar da uzzirin suna da daurin aure muhimmi a wannan ranar.
A wannan karon hankalin Baban Marina ba k'aramin tashi ya yi da wula'kancin da suke yi masa ba.
Ya gabatar da korafinsa gaban Dada cikin kankan da kai ya ce
"Ba zai yiwu na dauko wasu daga waje su marabci masu neman auren y'ata ba. Alhalin ga y'anuwana ban da ransu da lafiyarsu, har wanne daurin aure zasu je da yafi al'amarina muhimmanci Dada?
Ki shiga cikin wannan maganar, ina jin tsoron kada na kasa jurewa fa."
Ita da kanta ta sani ba'a kyautata masa ko ka'dan amma da yake bata iya tsawatar wa wadanccan shiyasa bata iya magana, har komai ya rincab'e.
Da rashin walwala ta ce "Zamu zauna da daddare dukkanmu".
Da daddare kuwa dukkansu uku suka hadu a gaban mahaifiyarsu, a sanyaye take gabatar da k'orafin da yayansu ya zo da shi.
Babu kunya dukkansu suka ce suna kan matsayarsu ba yadda za'a yi suna cikin hankalinsu su jagoranci bawa mai saka d'agaggen wando aure, kema da za'a fito k'arara a fa'da miki ainihin yadda ak'idarsa take da kin k'yamace lamarin wannan mutumin. Mun yi shiru ne kawai dan kada ace hassada muke yi. Ko bamu da kirki, amma waye a jahar nan bai san yadda Mustapha Zaki ya yi k'aurin suna wajen yiwa masu akidar yin maulidi kafar ungulu ba.
Duk wani masallaci indai ba na yan kungiyarsa bane sai ya durkushe shi, ke kan ki da yasan yadda kike son shehu da ya d'aure ki saboda zuciyarsa babu alheri."
Dada ta kad'u kwarai da gaske. Domin babban b'acin ranta a nemi ta'ba mata mutuncin ra'ayinta. Ita din mai mai zazzafar akida ce akan hakan.
Ta fara tafa hannu tana cewa "Ashe hakane? Allah na gode maka da ka kubutar da jinina fa'da wa hannun wanda zai yi mata sanadin rashin samun rabo ranar gobe".
Sai ta hau kuka tana sake godiya ga Allah da Annabi.
Jikin Baban Marina ya yi matu'kar yin sanyi ta yadda yan'uwansa suka shammace shi, suka gabatar da hujjar da ba mai kankareta a zuciyar Mahaifiyarsu.
Ya tabbatar sun dade da kitsa maganar dan sun tabbatar auren ya rushe gaba'daya, kuma wannan hanya ita ce mafi sau'ki da zasu ja hankali gyatumarsu ta lalata komai.
A zuciyarsa ya dinga ayyana shin wanne irin zamani muke ciki wanda dan-uwanka ma baya son ya ganka a inuwa?
Me ya tare musu ne?
Shi ka'dai ne yake fuskantar irin wannan tsananin ko kuwa a ko wacce zuria ce?
"Allah kai ne mai zamani, a kawo mana mafita, da sassauci" ya fa'da a ransa.
Ya sake kallonsu, yana ganin sun hade sun bar shi daban, sai dai a zahiri ne suke shiri a bad'ini kuwa ba wani taimakon juna a tsakaninsu, tunda kowa iya y'ay'an da ya haifa ne dolensa. Sannan kowannensu boye wa dan-uwansa wadatarsa yake yi.
Ya sauke gauron numfashi kafin ya yi magana ya ji Dada tana fa'din "matu'kar ina da iko akan ka ba za'a bashi aure ba, idan kuwa ka kafe sai dai na barka da Ubangijin gizagizai ya bi mini kadina a wajenka".
A ki'dime ya ce "Har abada maganar ta mutu, Allah ya yanke mata wahala ya fito mata da wani mafi alheri wanda za'a yi alfahari da shi".
Dada ta goge idonta tana fa'din "Ameen".
Baban Tsakiya kuwa ya ce "ai y'ar fariya ce , ba zata tsaya a matsayinta ba, dama ya ta kasance? bare yanzu da wannan tsohon banzan ya sake kambaba burinta.
Ai idan ba tashi aka yi akan ta ba, sai ta tsofe tana gabanmu tana zuba d'ibar albarka, ko yanzu tana ganin sakamakon hatsabibanci, tunda duk kintsatsse ba zai zo wajenta ba.
Har yau ta k'i barin Jabir ya fuskanci matarsa sosai, da sun fara zama lafiya idan har ya yi tozali da Yabi zai gigice.
Gashi kuma Maijidda matarsa ce, tunda cikine da ita, idan ba'a bashi aurenta da ake ta munafurci ba, ta ya ya ake so wannan rabon ya bayyana?"
Baban kasuwa ya ce " Ai ha'kuri Muna cikinsa, amma sai ace mune da laifi, ban da sha'anin jini tasirinsa yawa ne da shi ai wata shari'a sai a lahira kawai."
Dada ta ce "To ni kam ba zaku bar gun nan ba sai an samo wanda za'a ba shi auren Yabi. Domin na fuskanci matsalar gidan nan tana 'damfare da ita."
Baban Tsakiya ya sake cafe wa da cewa "Kinsan dai ni da Iliya bamu da mutuncin da zamu yi irin wannan ikon da ita, wannan maganarki ce da ubanta."
Cikin rawar murya irin ta sare wa da lamari Baban Marina ya ce "Yau muna watan Safar ko Dada? To matu'kar rayuwata ta kai, watan jibi na gaban maulidi ke nan, zan aurar da ita.
Domin ina da wadanda zan basu aurenta su kar'ba, sannan ita ma Ubangiji ya hore mini ita zata ta yi mini biyayya.
Ubangiji kuma zai duba manufar kowa a nan ya cusa wa wanda zan ba shi auren ya kar'ba da dukkan zuciyarsa".
Dada ta ce "Allah ya tabbatar ya nuna mana lokacin, amma ba za'a tashi ba sai ka fadi wanene, d'an wacce haular ce? Gudun kada a sake kitso da kwarkwata."
Baban Tsakiya ya ce "yarinyar nan fa ta riga ta rik'a, idan aka kai ta wani wajen ma mutuncin gidanmu zata zubar, me zai hana a lallaba a bawa wannan yaron kawai, tunda shima yana da tambarin da aure zai yi masa wuyar samu wa?"
Baban Kasuwa ya ce "Ni ma tuntuni nake son na fa'di hakan, to amma ina jin tsoron sharrin zuciyar da take raina alheri, yanzun nan sai a juya magana a ce da mugun nufi aka yi kaza".
Dada ta ce"Ku yi magana sosai mana, ni duk kun saka ni a duhu ban gane wa kuke nufi ba?"Tirk'ashi
Karshen littafi na d'aya.*Gaba'daya wadannan shafuka shimfida ne dan ku fahimci labarin da kyau, asalin labarin da turka turkarsa yana littafi na biyu da na uku*
*Bisa soyayyar da kuke yiwa rubutuna ya sanya zan yi muku tsarin VIP.
*In Sha Allah babu jira, dan zan kammala muku posting a cikin kwanaki ashirin da izinin Allah*
*Sau biyu za'a yi posting a Rana*.
*Ku zo mu yi tafiyar da babu nadama*
*Zaku dara, zaku koka, jikinku zai tsumu, zuciyoyinku zasu motsu. Tunani kuma zai tafi cancanken me zai faru a gaba*.*Marubuciyar HALIN YAU da SABO DA KAZA*
*Yanzu kuma alk'alaminta yana tafe da BAK'AR TA'ADAH*500regular page
VIP 1k twice pages
2384876855
Surayya Ibrahim
Zenith Bank.
08032773332.*Surayya Dee*
*Yar mutanan Gwaram*✍️
YOU ARE READING
BAKAR TA'ADA
General FictionMurya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina". Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito...