chapter 4

231 26 6
                                    

*Akwia ingantattun Saiwowin chadi da basu da illah*.
*Idan kina da doya ko kanwar da zaku aurar to ki yi kokarin Siya mata wadananan kayan da basu da illah domin kuwa saiwowi ne da Ubangijin yaje tsirara da su da kansa*.
*Akwia saiwowin dahuwar kaza*
*Akwai saiwowin Tsumi*
*Akwai saiwowin sanyi*
*Akwai daka daban daban*
*Akwai gumba*
*Akwai y'aya'n gadali*
*Akwai turaren matsi na tsugunno*
*Da sauran kayayyaki masu kyau da aminci*
*Zaku same su cikin farashi masu sauki da ikon Allah*
*Kawai tuntube ni a wannan lambar 08032773332*
*Ina aikawa ko wanne gari da cikin amince war Ubangiji*.

7&8.
Maganar Baban Marina ta dawo da ni tunanin da nake yi.
Kamar a sama na ji ya ce "Na gode miki Asiya! Duk yadda nake jan kunnenki akan b'atawa Dada rai, da kuma dukan yaran gidan nan ba kya ji, saboda kin riga kin zama y'ar kuka.
Uwarki kullum cikin yi miki kashedi akan shiga fa'dan yara da kuma tsokanar Dada, amma duk a iska ko? Na gode sosai da wannan bacin rai da kika sanya ni, Allah ya shirye ki".
Ya tsugunna gaban Dada ya ce "Ki yi ha'kuri! Halin Asiya ni kaina ha'kuri nake yi da ita, amma zan dauki mataki akan ta'ba ki da take yi".
Ta kyabe baki ta ce "To ka fara dan takidin aurensu. Jiya mun tattauna da kannenka sun ce su babu matsala ko yaushe auren ya zo a shirye suke, kai dai za'a fa'dawa ka fara tanadin tunda yaran ka har biyu ne".
Ya yi gyara murya cikin k'arfin hali ya ce "Babu damuwa Dada ina saka rai Ubangiji zai kawo mini hanyar da zan samu na yi musu iya abin da zan iya."
Ta murmusa tamkar ba ita ce mai kuka tana face majina ba. Ta ce "To babu laifi  Allah ya basu na gari, masu kuma ha'kuri, domin mai yakana ne zai iya zama da Yabi dan wuyar zamanta ya kai inda ya kai, ba inda ta baro uwarta".
Cikin sanyin jiki Baba ya mike yana cewa"Dada sai da safe mu kwana lafiya".
Ta amsa masa da fa'din "Allah ya tashe mu lafiya".
Na mike, Nazira ma ta biyo ni  muka fice, ba tare da mun ce uffan ba.
Domin na sake fusata da ta ce sun tattauna da kannensa amma shi ba'a saka shi cikin zaman ba.
Muna jin ta tana fa'din "Wanda Allah ya bashi tsawon rai zai yi kallon tak'ama a wajen ki Yabi. Yarinya da ke amma kusan ke kike juya shashinku gaba'daya. Kina tashi Yayarki ta biki zungui zungui ko sallama ta kasa yi mini saboda tana rarrashin zuciyarki?".
Ban juya ba, bare na tanka mata, balle kuma Nazira da take da sau'kin hali.
Muna shiga shashinmu muka yi turus a dalilin halin da muka ga mahaifinmu a ciki, zaune yake akan tabarma a tsakargida. Sai fifita Gwaggo take yi masa, gumi na yanko masa babu kakkautawa.
Muka isa gabansa, muka tsugunna, baki na rawa na ce "Sannu Babanmu!
Abin mamaki sai ya daga mini hannu tabbacin ya amsa gaisuwar tawa.
Nazira ma ta yi masa sannu ya amsa ta hanyar gyada mata kai.
Mama ta fito daga bandaki ta kalle ni ta ce "Wannan ja'irar yarinyar sai kin zama sanadin mayar da kananun ya'yansa marayu, fitananniya tabtacciya.
Ai duk gwanin na iya a rana ya ke"
Ta ja tsaki mai tsanani ta wuce d'akinta.
Bata jima da shiga ba
ta k'walawa Nazira kira, ta mike a hanzarce ta nufi dakin nasu.
Daidai lokacin Baba ya dan samu sau'kin zufar da take karyo masa.
Ya yafito ni, jiki na rawa na isa gabansa.
Ga mamakina sai ya mik'o mini hannunsa na dama.
Hannu bibbiyu na ri'ke hannun nasa, cikin barin jiki gaba'daya.
A sanyaye ya ce "Ina alfahari da ke Yabi! Kafatalin ya'yana ke nake da tabbaci akan ba zaki cigaba da yin mini *Bak'ar Ta'ada* ta y'an ubanci ba, na tabbatar da hakan. Ina saka rai ta dalilinki yarana zasu dawo tsintsiya. Na so ace da wuri na haife ki Yabi. Da al'amuran da suka dame ni basu yi mini tsananin da nake ciki ba. Amma Alhamdulillah! Ubangijinmu baya kuskure na gode masa, ina kuma tuba a gare shi."
Hawaye tuni ya goce mini dukkan zuciyata a jagule take da tsananin tausayin Mahaifina da a yau nake ganin wani irin tashin hankali da raunin da ban ta'ba ganinsa a ciki ba.
Gwaggo tana fifita, tana kuma share k'walla.
Ya numfasa ya ce "Idan na mutu Yabi, duk runtsi ku gaisa da yan'uwana, ko ba zasu taimakeku ba, to lallai ku dinga saka su a cikin al'muranku, idan kina yi, sannu a hankali zaki samu wanda zasu yi koyi da ke, tunda tun yanzu al'amura sun haska ke ce mai tsayayyen ra'ayi wanda yafi kusa da kyau da kuma dace wa."
Murya na rawa na ce "Mu sasu a alamuranmu ko da ba  zasu taimakemu ba, ko da idan mun fa'da musun ba zasu dauki al'amarin namu da girma ba?"
Ya sake damk'e hannuna ya ce "Haka nake so Yabi".
Da karfin zuciya na ce "Da Ikon Ubangiji zan yi yak'i da dukkan zuciyata na yi hakan.
Amma ina ro'kon arziki ka mini afuwa, ka yafe mini muzancin da na janyo maka dazu".
Ya girgiza kai ya ce "Baki yi laifi ba, na sani. Sannan su d'in ma bana son ki d'auki abin da suka yi mini a matsayin muzanci ko tozarci, na sani baki da sauki, kina da ru'ko, dan haka na umarce ki, ki manta komai".
Na murmusa hawaye na kwaranyo wa na ce "Shi kenan Babanmu! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, yadda a ke mini habaicin tunda aka haife ni ka tsiyace, ina ro'kon Ubangiji kullum, ya saka idan na girma na samu sanadin da arzikinka zai dawo ta dalilina fiye da wadda ka rasa a shekarar da na iso duniya".
Ya ce "Rabu da maganar jahilai, ko iya hakan na ga ni ai na gode,  sanadin sana'arki na daina fargabar a tambaye ni ku'din sabulu a gidana.
Alherin da kika janyo mini mai yawa ne, mafi farin-ciki a ciki shine wanda kike yarda ya'yan da na haifa duka daya ne a wajenki ta fuskantar mua'amala ta zahiri."
Da'di ya tsirga mini ban ta'ba zaton Baba ya fahimci yadda nake da ra'ayin rikau akan kannena ba, bansan ya fahimci ina tare musu fa'da ba, hakanan ban san hakan yana yi masa da'di ba, tunda kullum a cikin kirarin bani da hakuri yake.
Sannan kuma baya ta'ba nuna mini ina abin a yaba, sai dai ya ce ai duka yan'uwane tunda ragowar ma y'ay'ansa ne da yan'uwansa suka haifa masa.
Cikin son na sake k'arfafa nasa guiwa na ce "Duk d'an da ka haifa ina jin sonsa har cikin zuciyata Baba".
Idonsa ya ciko da k'wallah cikin k'arfin hali ya ce "Allah ka shirya mini yarana, ka saukaka musu, ka basu lafiya, ka cika zuciyarsu da tsoronka, ka jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu. Allah ya yi miki albarka Yabi".
Daga ni har Gwaggo muka hau fa'din "Ameen ameen".
Na kalli Gwaggo na ga hawaye ya goce mata, jikina ya sake yin sanyi, domin ita din wata irin mace ce mai k'arfin zuciya k'warai da gaske,  abin da zai saka ta yi kuka to kuwa ya girgiza ta ba ka'dan ba, duk tsananin da take fuskanta a rayuwar gidanmu ban ta'ba ganin ta yi kuka ba.
Na yi kasa da kaina cikin rauni mai yawa na ce "Ameen Baba! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka. Na gode sosai".
Duk muka yi shiru kowa na cikin alhini. A hakan Nazira ta fito rai a bace da gani Mama sababin yadda ta like mini ta yi mata.
Kusa da ni ta zauna, cikin sanyin murya ta ce "Sannu Baba".
Murya ba amo ya ce "Sannu kadai Nazira, Allah ya kara miki ha'kuri kin ji. Ki cigaba da jajirce wa a kan gaskiya ko da hakan ya ci karo da ra'ayin kowa, ku so junanku, ku binne a tsakaninku, kin fi Yabi ha'kuri, a duk sadda kika ga zata yi aikin nadama yi amfani da fikon da kika yi mata ki dakatar da ita, komin runtsi kada ki bari ta dauki hukunci cikin fishi. Ke kuma Yabi kul kika ki jin shawararta, idan ta ce yi ha'kuri, to na roki ki bar abin nan komin girmansa.
Ina jaddada muku ne dan ku ri'ke su da kyau, ko babu ni idan kuka ri'ke maganganuna ba zaku ta'be ba. Allah ya yi muku albarka ya ha'da ku da maza na gari, ya raba ku da sharrin shaidan a cikin zumunta".
Muka amsa da Ameen amen cikin sanyin jiki.
Nazira ta mika hannu ta karb'i Maficin hannun Gwaggo ta cigaba da yi masa fifita, duk da gumin ya yi sau'ki.
Har lokacin kuma bai saki hannuna ba.
Ya jima kafin ya saki hannuna yana sake cewa "Na hore ki da ha'kuri Yabi! Ku zauna da yan'uwana lafiya, ku mutunta su, ku gaishe su da girmama wa".
Na gyada kai yayin da Nazira ta ce "Duk yadda kake so hakan zamu yi, amma ka taimake mu ka daina sanya damuwa a ranka Baba! Fatanamu mu ganka a tsaye akan kafafuwanka, idan muna ganinka cikin walwala ba abin da zai dame mu sosai."
Haka muka kwanta ni da Nazira tana ta jan kunnena na kiyayi Dada, tunda zata iya yin ha'din kitifo har ya zama sanadin da za'a samu damar cin zarafin Babanmu akan idonmu.
Tun daga wannan ranar na kame bakina a gaban Dada, duk karatun da zata yi bana tankawa, haka nan ban cika zama na yi doguwar magana da ita ba.
Zanje gaishe ta babu fashi, kuma sai na tabbatar mun ha'da ido sannan zan kama sunanta na gaishe ta.
Na daina jan magana a tsakaninmu ne kawai.
Sannan na soke zuwa hirar dare, amma matu'kar zata d'ora karatu sai ta sa an kira ni.
Janye war da na yi da ita kuma sai ya dame ta, amma ta kasa bu'de baki ta yi magana.
Tunda Nazira ma ba wani sake wa take yi ba, balle ta yi mata korafi.
            ***
Karshen wata Yaya J ya dawo. Mun taso daga Islamiya muka ganshi zaune akan dandamalin kofar gidanmu.
Sanye yake cikin kananun Kaya da suka yi matu'kar kar'barsa, sai kamshin turaren Dagmar yake tashi sannu a hankali.
Dukkan y'anmatan suka hau rige-rigen gaishe shi, yayin da ni na sunkuyar da kai kasa alamun kunya.
Na zo wucewa ta gefensa na saci kallonsa ai kuwa karaf muka hada ido, wani irin abu ya tsikare ni, kwalliya da tsabtar Yaya J ko mace ce ta kai a sata a masu tsabta, sannan kankantarsa tana sawa na ji mun dace da juna.
Domin da ka'dan ya zarta ni cika ido da tsayi.
Babban abin burgewa mai nutsuwa ne, sannan mai ha'kuri ne, bashi da hayaniya ko ka'dan.
Da sauri na janye idon nawa, murmushi yana subuce mini wanda ban shirya yinsa ba, na tsananin shauki ne.
Na wuce ba tare da na yi gaisuwar ba.
Cikin raha ya ce "Nasiba ki koya wa Asiyan Toro gaisuwa tunda ta zama bak'auya".
Da dariya ta ce "Yaya Jabir kaine da fa'din Asiyan Toro yau? Babu ruwana a shirginka da Yabi".
Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Tsoron ta kike ji ne Nasiba? Kin fita tirinya fa, to kuma ya za'a yi ne tunda ku biyu zan ha'da na aure rana guda?".
Ta yi maza ta ce "Lallai kuwa ka shiryawa darun Yabi domin har ka tafi ba zata saurare ka ba, ni kuma ba zan taya ka rarrashi ba".
Ta wuce ni da sauri ta shige shashin Dada.
Ni kuma na wuce shashinmu a dalilin yau Nazira ba ta samu damar zuwa ba, saboda tana fama da ciwon mara.
Zuciyata har wani tukiki take yi na tsananin bacin ran kalaman Yaya J.
Wai zai ha'da ni da Nasiba ya aura.
Na yi tsuka na ce "Sai dai ya aureta ita ka'dai. Dama na san dunbula dunbulan kirjinta na iya tafiya da shi, ba'kin ciki ya sake turnike ni a dalilin ni ba mai cikar k'irji ba ce. Har yanzu bana saka breziya sai dai half best, domin a manne suke a kirjina yan kananu da kadan suka fi  tsakuwa.
Amma Nazira da Nasiba kam kirjinsu a cike yake sosai.
Wataran har rayawa nake yi ko dai na fara shan ruwan baru ne ko zan yi sa'a su fito su cika mini kirji ni ma.
Amma sai na kasa, mussaman da sai na ro'ko ruwan kuma sai nake ganin kamar za'a gane dalilin shan da zan yi.
Da daddare ya dinga aiken na zo amma na yi mirsisi na ki fita.
Washagari a zauren Dada na tarar da shi.
Na sani sammakon tashi ya yi dan ya hadu da ni. Domin shi ba ma'abocin tashi sassafe bane, da zarar ya dawo daga sallar asubahi idan ya kwanta sai tara yake tashi.
Nazira ta gaishe shi ta shige, yayin da na dauke kai fuska murtuk zan wuce shi.
Ya yi maza ya sha gabana yana fa'din "Haba Yabin J baki san wasa ba ne?
Na yi bakam tamkar dai ban fahimci da ni yake magana ba.
Na yi kasa da kaina.
Ya sassauta murya ya ce "Yanzu Ashe zaki iya mini irin wannan fishin Yabi?"
Na dago na kalla shi na ce "Oh wai ka yi zaton ba zan iya ba?
To kuwa ka dauka zan yi maka fiye da hakan domin zan iya shafe babinka gaba'daya."
Ya jima yana kallona cikin ki'dima.
Ya yi k'arfin halin cewa "Me ya yi zafi haka, daga wasa?"
Na sake d'aure fuska na ce "Bansan wasa ba, ban iya shi ba, ban kuma ta'ba daukan al'amarinka a matsayin wasa ba, bare har na yi maka tsokanar da zaka ji ka tozarta".
"Hakane, na kuma gasgata ki, yanzu ki yi ha'kuri ba zan sake miki irin hakan ba kin ji".
Na jijjiga kaina tare da yin wata irin shakiyar dariya na ce "Ha'kurin ma ban iya shi ba. Ba kuma zan koyo shi a dalilin cin fuskar da aka yi mini ba. Na riga na barwa Nasiba kai, dan haka ka manta da wata Yabin Marina".
Ya yi tsam cikin kaduwa wata'kila yana mamakin yadda kishi yake kutsowa tunda ga kasan zuciyata ne, kallon yarinya k'arama yake yi mini, sai dai bai san yar shekaru goma ma zata yi kishin abin da take so ba, bare ni da nake da shekaru sha sha biyar, na ke harun sha shida.
Ya lankwashe murya cikin rarrashi ya ce "Ai na yi zaton ina da wata alfarma ta daban a wajen ki, ban ta'ba zaton zan yi miki laifin da zaki shafe ni a zuciyar ki ba.
Yau dai daya tak da na sab'a miki, ki daure ki mini uzziri, ni kuma na yi al'kawarin ba zaki sake kama ni da laifi irin wannan ba".
Na dauke kai na ce "To idan na yi ha'kuri na ce maka komai ya wuce, ya zan yi da tafasar da zuciyata take yi idan na ga Nasiba?
Ya zan yi na goge amincin da zuciyata ta yi akan ita kake so bani ba, tunda ita din ta fini zama y'anmata?"
Tsananin mamakin da na ba shi ya sanya ya kasa magana na tsawon lokaci.
Sai da ya jima kafin ya numfasa ya ce "Ni fa ba wacce take burgeni nan duniya idan ba Yabin Marina ba.
Kinsan dai ina tsokanar Nasiba tun fil'azal tunda abokiyar wasanmu ce, yar mace da dan namiji muke.
A kaikaice na ce "Oh oh, ashe dama ana wasa har irin haka?
To kuma wai ya matsayin wannan *Bak'ar Ta'adar* a shari'a tunda ba'a wasa da maganar aure?"
Ya dan tunzura ka'dan ya ce "Ke  Yabi".
Nima na ce "Ke Yabi ko kuma ke gaskiyar magana?"
Ya girgiza kai ya ce "Shi kenan na gode, na gode sosai da yadda kika ajiye ni".
Ya fice ya bar ni, kafin na shiga wajen Dada Bulkachuwa ya fito daga dakinsa.
Ya yi fitoh irin na tantiran yan-iska ya kalle ni ya ce "Asiya Toro rikakkiyar budurwa".
Ya kwashe da dariyar iyashege ko me ya tuna kuma sai ya gintse dariyar tasa.
A fili ya ce "Ban da ma shan koko d'aukar rai ne, ta yaya kamar Jabir da yake ganin Bigger babes zai tsaya wajen kwailaye irin Asiya Toro? Ya wuce yana sake fa'din " Soyayya da kananun yara menene a cikinsa ban da raini da ba'kinciki, yar yarinyar da bata gama iya wanka ba ma sai ta caccaba maka magana son ranta, abin ba'kinciki kuma dole ka rarrasheta ko ka hadu da gallazawar zuciya."
Na yi kwafa a dalilin yadda furucinsa suka sake sawa na washe shi.
A dole na shiga ciki na gaida Dada. Ina kallon yadda Nasiba take rawar jikin zuba masa ruwa a buta, dan ya yi brush.
A raina na ce wannan fa shine shan kokon.
Sai da ta gama barebaren yi masa hidima sannan muka fito muka wuce makaranta.
Gaba'daya wannan zuwan na Yaya J ban yarda mun shirya ba, haka ya koma Jos.
Ni kuma ina k'arfafawa kaina gwara mini Abdulrashid kamar yadda Gwaggo take so, domin ni da kaina ban san waya fi sona a tsakaninsu ba.
Sai dai me?
Juma'a da maghariba muna tsakar gidanmu sai jin ihun yara muka yi suna "Oyoyo Yaya Jabir, oyoyo".
Nazira ta ce "wannan dawowar taki ce Yabi. Na ro'ke ki huce hakanan ai ya garu".
Na tabe baki na ce "Rabu da shi, nifa dama ina ta neman hanyar da zan yakice shi a raina, ki ga fa irin yadda Baban Tsakiya ya yi wa Baban Marina, akan idonmu".
Ta fesar da iskar takaici ta ce "Amma Baban ya ce ba ruwanmu da kasafinsa da yan'uwansa, a gabanki ya tabbatar bamu fi yan'uwansa a gunsa ba.
Aure ai kaddara da rabo ne Yabi.
Banda haka da wani namijin bai isa auren wacce yake aure ba, sai kaddara ta ba shi, haka nan wata macen bata isa mijinta ya kalleta da nufin soyayya ba, amma saboda karfin kaddara da rabo sai kiga ta zame masa mata kuma uwar ya'yansa.
Matu'kar Yaya Jabir mijinki ne, sai kaddara ta sanya aurenku ya yiwu komin k'in da iyayensa zasu yiwa al'amarin. Mu da muka yi sa'a ma dukkan iyayenmu suna da ransu, kullum kuma suna roka mana mu dace da maza na gari, na yi imanin Ubangiji ba zai juyar da addu'arsu ba, hakan kuma ba zai hana mu ga kalubale a cikin ko wanne zabi ba, domin sunnar rayuwa ce komai na da irin nasa cikas din, sai dai albarkacin addu'ar iyaye sai ki ga komai ya saukaka.
Jikina ya yi sanyi, na kasa bu'de baki na ce komai.
Ta ru'ko hannuna sosai ta ce "Ki yi ha'kuri kin ji Uktina".
Na nisa na ce "Na yi ha'kuri saboda ke, amma ki fa'da masa bana son irin wannan wasan, bana so".
Cikin jin da'din na yarda da maganarta ta ce "Madallah da K'anwata kuma kawata YABIN J".
Na murmusa a raina kuma sai addu'a nake yi mata ita ma Ubangiji ya kawo mata saurayin da zan taya ta sonsa, domin hatta Abdulrashid da ba wani sonsa take yi ba, bata ta'ba kushe shi ba, illah iyaka tafi son Yaya J.
Idan ina yi mata d'an bikin ita bakin ganga ce, domin a gabansa bata ta'ba nuna masa akwai wanda take supporting sama da shi.
Sai ta murmusa ta ce "Tunda har zuciyar Yabina tana dan sonsa ai kuwa yafi karfin na wula'kanta shi, baya ga haka son ki yake yi, dan haka nake girmama shi. Amma ai bazan so shi na bar Yaya J ba domin yafi shi cancantar ya same ki".
Bata ta'ba nuna k'yashi ko takaicin ina da samari ita bata da su ba, duk da ta fini zama cikakkiyar budurwa.
Ni da kaina na sani Nazira tana cikin Yan ka'dan da Ubangiji ya wanke musu zuciya akan k'yashi.
Allah kenan! Sarkin hikima sai ya bawa bak'ar uwa karimi ko karimar yarinyar da za'a yi ta yi mata alfarma saboda kunyarsu. Hakan ce ta kasance domin sau tari sai na yi yun'kurin yiwa Mama iyashege irin ta dan yau dan ta fahimci dan Babanmu da Gwaggo suna shayinta, tunda laya ce ita, ni kuma mai zamani ce dole kuwa ta kiyaye ni.
Nauyin Nazira ka'dai yake sawa nake hadiyar dukkan matsatsin da take sanyamu. Domin na riga na ajiye alakar matar Babana ce tunda bata ta'ba yi mini karar ni din y'arta ce ko ta mijinta ba.
Ana idar da sallar isha ya aiko na je.
Yana jingine jikin katanga hannuwansa biyu a kirjinsa, sanye cikin shadda shud'iya kalar sararin samaniya.
Sai kamshi yake yi.
Na rakube gefe guda ba tare da na ce kanzil ba.
Ya matso kusa da inda nake ya ce "Assalamu alaikum Yabi".
Murya babu amo na ce "Wa'alaika Salam".
Ya ce "ki yi ha'kuri, na yi kuskure, tunda na gane da gaske ba kya son irin wannan wasan bazan sake yi miki ba shi kenan?".
Na yi kasa da kaina, ba tare da na ce komai ba.
Ya numfasa ya ce "Kin yi shiru".
Cikin yauki domin da k'yar na ce "Ya wuce".
Ya murmusa ya ce "Yabina sarkin ginshira, da rikici".
Na kawar da fuskata gefe ban ce uffan ba.
Ya dan damu ya fara fa'din "Kin ce "Ya wuce amma kin k'i sakar mini fuska, saboda ke fa na dawo".
Fuska ba walwala na ce "Ya wuce mana, mantawa ai sai a hankali, yo ban da ma dai ina ganin mutuncin ka ai da an rabu ke nan, ina ruwana da duk wanda zai nuna mini yana son wata dan ta fini tirinya".
Ya kame baki alamun mamakina.
Tsawon shudewar mintina sannan ya iya ce wa "Yabin Marina ho".
Na sake tsuke fuska.
Murya ba amo ya ce "Ba tone tone zamu yi ba, ai kin gama magana tunda na yi sa'a kina ganin mutuncina. Na gode miki da wannan karamcin, ina son ki fiye da komai".
Ya lankwashe murya ya ce "Mutunci da soyayya idan suka hadu fa'din irin al'amuran da zasu haifar na nutsuwa ma bata lokaci ne Yabin J".

Regular 500
VIP 1k
Via 2384876855
Surayya Ibrahim
Zenith Bank.
Tura shaidar biya
08032773332.


✍️

BAKAR TA'ADA Where stories live. Discover now