12

31 4 0
                                    

12

LATYFAH IMAM

Na nana diso

 
  Ataƙe jikin nawal yayi sanyi cike da rikecewa da ƙidemewa yasa taƙara danna numbar amma abun mamaki bata shiga, wannan wacce iriyar masifa tasaka ƙanta? Nan taƙe tafara kuka, tare da dawowa ciƙin kamfanin dan ta yankewa ƙanta gudu tabar garin gaba daya zata koma kudu can taje tayi rayuwarta.

  Nasamu magana da'ita Barrister yanzu ƙai nake jira kawai sai muje gurinta. " Kayi hakuri sir bazan iya wannan shari'ar ba." Da mamaki sir tahir ya juyo yana kallonsa, kamun yace wane yahanaka ne?" " ko daya babu wanda yahanani bazanyi bani ba."
" Haba Barrister yazakayimun haka nasan kai kadaine zaka tsayamin gaba da baya dan kwatowa wannan yarinyar hakkinta, wallahi bata aikata ba, idan da kaga halin datake ciƙi acikin gidan yari sai kayi mata hawaye." Tsayawa yayi da magana yana mai goge hawayen da suka zubo masa.
Mikewa Barrister yayi yace "  Aikina yafi taimakon da zan maka dan idan narasa aikina nashiga uku nima kayi hakuri bazan iyaba." Binsa yayi da kallo har yabar offices din nasa, karar message din da yashigo wayarsa ne yasakashi sauƙar da wayar kan idonsa yana mumushi ganin daga gurin manyansu ne ko karin girman da yaketa fata yasamu? Budewar da zaiyi sai yaga transfer akayi masa zuwa kudu yabar aiki anan. Atake gabansa yashiga waduwa me haƙan yake nufi? Innalillahi wa'inna illahir raji'un yafaɗa kuma harda bayanin gobe akeso yahuce saboda aiyuƙan can. Hank'alin nawal bai tashiba sai dataga an aiko mata da taƙardar kora,tashin hankalin datake ciki yafi mata million goman data samu wannan wata baƘar masifar ce taƙe binta? Jaƙarta ta dauka da komanta ta bar ciƙin company din."

****

  Tunda Aliyu yafito yayi hanyar bolar cikin gidansu, zura hannunsa yayi yashiga kwasar bolar da dattin yana Tarawa ajiƙinsa, daga nan kuma sai ya huce sashin ammiey yana wata iriyar dariya da zai tabbatar maka baya ciƙin hankalinsa, amiey dake zaune abun duniya ya'isheta ta kallesa ganin jiƙinsa da datti sai ya samu saman kujerarta ya juye sharar nan kuma ya dauki ledojin yashiga sakawa abakinsa. " cikin tashin hankali ta nufosa tana kiran sunansa." Nan yasaka dariya yana faɗin kema zakici ko in baki ki cinye ko ki haɗeyi, sai muyi aure daga aure sai mu mutu ko, sai yaja rigar Ammy yace " menene wannan kai kai yashiga zare idanu." " laila laila laila Asabe ammiey ta kwala masu kira, tunda suka shigo hanƙalinsy yaƙara tashi ganin ya ɗane ƙan kujera." Laila ce tace menene haka ammiey tana zaro idanuwanta. " zama ammy tayi akan kujera tana fashewa da wani kuka mai taɓa zuciya. Wannan wacce iriyar kaddara ce shaye shaye aliyu yafara kuduba kuga fa bola yashiga tafada tana kara fashewa da kuka." Laila ce ta nufi sashin mumy tana sanar mata, ko dataje momy har ta yafa mayafinta tafito tana faɗin " Innalillahi wa'inna illahir raji'un me yasamu aliyun." Yadda take salati hawaye yana zuba afuskarta zaka tabbatar wannan ahali suna ciƙin rudu, " Aliyu aliyu menene haka zaka tayar mana da hankali menene haka? Bamu gama jimamin ɗan uwanka ba shine kuma zaku daga mana hankali tafashe da kuka itada mumy, " laila dakko key din motar wannan asubuti zamuje." Asabe dake tsaye a raƙube tace " Amma ammiey wannan kamar shafar jinnu fa bai kamata akaishi asubuti ba." " Mumy dake kuka tace " Nima na zargi haka Amma tayaya za'ace jinnu kuma." " mumyn umar babu maganar jinnu anan wallahi shaye shaye ne kumuje asubuti mufara samun maganin abun." " ammiey karkuje asubuti danAllah cewar asabe afara gawada na hausa tuƙunna zai iya yihuwa gamo yayi." Kuma kin faɗi gaskiya ammiey abarshi gidan mu gwada na hausan." Riko aliyu tayi yana fusge fusge daga karshe ma fizge hannunsa yayi sannan ya hanƙada mumy datayi gefen bango ƙanta ya fashe,  nan yashiga da sakko da glass din dake ƙan table dinsu yana fasawa, ko da ammiey tayi hanzarin kamoshi kasawa tayi sai da suka kira umar atake yatawo da likita aka danna masa allurar bacci. " Ammy stop crying." Kallon umar tayi da yanzu take kallonsa kamar abdul take " Son indaina kuka fa kace?" " Yes ammy please kiyimasa addu'a yafaɗa yana mai rike mata, uwa kike gurina ganinki cikin damuwa zai saka zuciyata zafi." " murmushi tayi tana kallonsa ciķe da kauna tace " Allah yayi muku albarka." " Ameen ammy bari naje nagayawa malam haruna ko akwai abunda za'ayi, tunda laila ta gafi da mumy asubuti."

****

   4:30 agogon wayarsa yashiga bugawa ciƙin sautin kara mara hayaniya, Mikewa yayi zaune yana mai ambatar addu'oin tashi daga bacci, a hanƙali kuma ya sakko da kafafunsa kasa yashiga bandaƙi, baƙinsa dauke da addu'ar shiga bandaƙi, ruwan yasaƙarwa kansa wata fitinanniyar sha'awa tana addabarsa, a gaggauce yashirya zuwa masallaci kamin kuma ya huce zuwa gurin gym ya dauki loƙaci Nan sannan kum ya nufo gida , bai tarar da kowa a palour dinba sai saukar kuka da yaji daga daƙin kanwartasa nana tura kofar yayi tare da sallama abaƙinsa yana zuba mata idanuwansa, jingina yayi ajiƙin garun daƙin yana kallonta dake kuka kamar ranta zai fita." Nana menene haka kikeyi? Ko ummy ce ba lafiya? Ya cefeta da kalmar a zafafe. " Yayanmu kullum na kwanta sai naga latyfah imam acikin wani hali wai tana tsintar abu a bola tanaci, na maimaita mafarki yakai sau 3 and idan nakira wayarsu basa shiga har na kakarta iyami and na mijinta ma bayashiga." " Yanzu nana ƙinkyauta kenan akan mafarki kike kukan nan sai kace anyi miki mutuwa? Kawa dai ke bakida zance sai na kawarki bazakiyiwa ƙanki faɗaba kenan? Kitsaya ki karasa karatunki wannan abun da kike gani dama kika samu wallahi kuma gata abiy yake miki nasan idan yaji maganar nan har nima sai kinsaka ya ɓatawa rai." " Yayanmu please ka fahimce ni." Daga mata hannu yayi yace " ai na fahimta kiyi mata addu'a ita addu'a dum inda mutum yake ana turamasa ita kitashi kiyi sallah har 6 kina kwance." " To yaya tafaɗa tana shigewa bandaƙin shikuma yana fita. Tana shiga ta dasa wani babin kukan ba'ita tafito ba sai kusan7 tayi sallah ta nufi kitchen saboda yunwar datakeji. Ganin yayan nata tayi daga shi sai singlet da dogon wando ƙallonsa tayi tanaso ta hana ƙanta dariya, idonta ya sauka ƙan kunun da yake haɗawa. " Yayanmu tafaɗa tana dariya what are you making daman ummy tacemin ka iya girki ashe da gaske ne?" " Na gaji da wannan abincin nasu kullum shiyasa jiya na tsaya nasiyo garin kunun nan kinsan dakyar nasamesa sai da naje wani African store harda kosai na haɗa gashinan ya nuna mata har ya dora mai." " Kai mashaaAllah yaya wallahi ka haɗu anty amina shiyasa take maka WANI SO, maza nason shayi kai kuma abunda bai dameka ba." " Banason kayan zaki da abinci mara nauyi shiyasa nake ɗan ji da anty ai zaki lura indai naje gida to abincin gargajiya takeyimun ni nafison su." " Jiyama bakaci friedrice ba." " Banaci ai nafison tuwo da wannan abubuwan sai dai kuma ina cin salad ai kinga yau kema sai kinfi jin daɗin aikinki idan cikinki yacika." Sai data fara soya kosan sannan tace " Inama ace kai ka auri kawata ba ɗan iskan mijin nan nata ba, nasan tana nan tana shan takaicinsa, yayanmu kaga yadda yake wulakantata." " Uhm Nana haramun kikeyi taya zakice dama ni na aureta kinsan tanada aure akanka stop this!. " Am very sorry yayanmu wallahi mijinta bashida kirki at all sunaye marasa daɗi ugly, fat girl irin kalmomin nan marasa dadi and yayanmu kasan she is not fat wallahi batakai anty aminan ka ba fa." And yake zaginta haka? Why not araba auren." " Saboda mahaifinsa take zaune dashi." That's funny Nana batada ra'ayin kantaba?." " Yayanmu bakaji komai ba wallahi." Allah yabata mafita yafaɗa yana suna karasawa taƙai musu komai dinning shikuma yashiga bedroom dinsa domin wanka! Sai da yayi wanka yashirya cikin kayan aiki sannan yafito, ko da ya'isa Nana da abiy sunfara karyawa," abiy barka da asuba." " Ashe har yanzu kana taɓa girkin?" Murmushi yayi ya zauna. " Nafison abu mai nauyi shiyasa." " madallah ai gashi kasamu lada, daman zan maka magana akan kursum kun daidaita ne? " Da hanzari ya ƙallesa yace " Abiy wacce kursum kuma?" " Au bama kasanta ba kanwar matarka nake magana naga mahaifinta yayimun magana." " DanAllah abiy a ajiye maganar aure zuwa gaba ni banason yarinyar nan, banma shirya wani aure ba yanzu." Murmushi kawai mahaifin nasa yayi baice masa komai ba.

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now