18

32 5 1
                                    

18

LATYFAH IMAM

Nana diso

Idanuwa na Na dago na zuba masa su, atake suka canza kala! Cikin girmamawa da iyayena suƙa koyamin Nace " Allahn daya halicce ka shine wanda ya halicceni!  Nayi mamakin furucin da ƙayimun domin bantaba tsammanin ɗan gidan Alhaji mai lema zai kasance mara tarbiya ba! Kana tunanin inasonka ne? Kokuma ina son dukiyar mahaifinka? Ko daya mahaifinka abunda yayimana mu da iyayenmu bazamu iya biyansa ba! Kamar yadda kake ganin an tilasaka to nima haka aka tilasani! In har zakaje ka bijerewa mahaifinka akan afasa auren da nima ka taimakamin dan bansan ɗan da baba yakeyiwa kuka yakai haka gurin watsar da tarbiyarsa ba! Kunsan da yadago manyan idanuwansa me yayi min? Marina yayi marin da Na manta rabun da ayimun na manta rabon da ataɓa lafiyar jiƙina, bai tsaya anan ba sai ya ciro bandir sin ƴan naira dari ya watsomin yana faɗin " who are you da zaki gayamin irin wannan kalmar? Who is your father? Wacece uwarki? Ƴar Ladanin masallacin k'okuma mai awara ? Doyi kikeyi wari kikeyi? Ni Abdulkarim mai lema nafi ƙarfin tarayya dake ƴar gidan talakawa! Yaja motarsa yayi tafiyarsa! Me zanyi? Kuka ko ihu? Ai ƙam zuciyata kasa rike kuƙan tayi kuma naƙi dauƙan kudin nayi cikin gida ashe karamin ƙanina abbas yana ƙallon komai! Sai ya tattaro kud'in yashigo gidan! Kuka nasaka ina rusa ihu, iyami dake girki tafito tana tambayata ko lafiya? Haka umma ma tashigo tana fadin ai idan da kwadayi da wulakanci yarinya sai muni amma saboda rashin son gaskiya da tsoron Allah kin dage sai kin auri mai kudi! To ai da alhaji mai leman kika aura ba ɗansa ba!" " Iya baƙinki kamin na cimiki mutunci." Iyami tafaɗa tana nuna umma. Umma tafita tana dariya ! Mutunci daman kunada sauran mutunci tasa dariya harda shewa!. Bakin cikin lafazinta yasa nasakawa kukana ƙarfi ina kallon kakara kuma uwata ubana ƴar uwata! " Iyami." " Basai ƙin gayamin komai ba naji duk lafazin yaron, ai nayi tunanin zaki iya? Ashe bazaki iyaba kika amince? Inake ina yaron nan mai kama da turawa saboda Allah? Inake ina yaron da turawa suka raina? Tun farkon maganar nan sai da nasanarmiki akan kice baki amince ba kika nunamin kada muzama butulu, abunda bakisani ba latyfah imam rayuwar aure ta huce duk yadda kike tunani, morewa aure ki aure wanda yake sonki yafi naki ba laifi idan duk kunason kanku amma idan namiji ya aureki bayasonki ai zan iya kiramiki da abunda zaiyi miki sai yafi ta'addanci! Kinada kyau kuma ke kyakyawace kada ki barinwani yadinga sakaki awani tunani ke kikace zaki iya dan haka sai kicigaba da haƙuri." Bance mata komai ba duk da ina sauraron duk abunda take cewa sai dai nacigaba da kukana muna zaune abbas yashigo shima idonsa yayi jajir, kamar yadda nagayamuku abbas ɗan ummane amma yana mutuƙar sona. Mikomin kudin  yayi yace " Yaya kiyi hakuri Allah bazai bari wani bawansa ya wulakntaki ba." Kallon kudin hannun nasa nayi inajin wani baƙin ciki acikin raina! Ganin bazan karba ba yasakashi ajiyewa yafita.

  Aciƙin satin aka kawo lefena, ashe bakaramin rigima akeyi ba agidan alhaji mai lema dan Rikicin da Ammy takeyi sai yasaka alhaji mai lema buɗe baƙinsa yace indai takara magana akan lamarin auren nan to tabbas a baƙin aurenta, hakan yasata kauda kanta akaina amma duk wani alkabair tana jifana dashi! Kawo lefe unguwar mu Sai yazamana yajawo cecekuce acikin mutane anata faɗin ankawomin lefe zanje na saida kaina saboda kudi! A satin nana ta dawo daga tafiyar datayi! Suka zauna da iyami suka tsara yadda zasu gabatar da bikin nikuma ina gefe abun duniya ya isheni duk yadda natsara aurena da irin soyayyar da zamuci da mijina yau ta ruguje! Innalilahi wainna illahirrajiun aduk lokacin dana tino da abdul abunda nake ambata kenan! Nana ce ta tsayamin akomai na bikin nawa, abikin ma dangin mahaifiyata haka sukace basuda hali kunsan ummyn nana itace tayimun gado set da kujeru da tv da fridge kai naga kauna ranar kuka nayi saboda farinciki dan komai tsiya anfidda ni ƙunya, ranar da aka ƙaini bayan kowa ya watse ƙunsan Abdulkarim bai kwana gidan ba. Inada kwana uku agidan sai ga kaninsa aliyu da laila ƙunga irin zagin da sukayimun apalour daman tunda naji yadda suka shigo yasa nasakawa kofar bedroom dina key har suka karaci zaginsu amma ban fito ba suka gaji suka tafi. Ranar ma kwana nayi ina kuka! Ranar da abdul ya dawo ranar satina daya agidansa cikin girmamawa nace masa barka da zuwa ina mikewa! Kumsan menene  abunda yafito daga baƙinsa! " tasarmin agujerar nan dan ba kujerar talakawa bace ba ba'a saba hawa agida ba..and wannan ne naƙarshe da zan kara zuwa palour na naganki zauni da mummunar fuskarki a palour na to tabbas sai na ƙona fuskarki, hawayen fuskata na share nayi shigewata daƙi shikuma yana jan tsaki, tunda nashiga daƙin sai yazamana damuwa tanason illatani wani zubin da rana nana zatabiyo musha hira, idan kuma tanada aiki a offices bata biyowa! Rana tsaka alhaji mai lema yace in fara zuwa aiki hakan yasa nadinga yimasa addu'a ina gode masa, amma sai yacemin ai abunda nayi masa komaima ayanzu zai iyayimun dan ni zaiyiwa godiya da na zauna da abdul, kuma duk wani abu idan yayimun in tabbatar na sanar masa nadai amsa da to ina kashe wayar bayan munyi sallama!.

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now