26

29 3 0
                                    

26

LATYFAH IMAM

Nana Diso

Fuskatace ta sauƙa akan mutumin da bazan taba mantawa aciƙin rayuwata ba shine mutumin daya taƙa mahimmiyar rawar bayan rasuwar iyayena Ataƙe na zabura nakara sauri gabana yana faɗuwa ko nemana yaƙeyi zai kara makani a kotu ataƙe duk wata nutsuwata ta gushe a yayin da nake hango irin azabar danasha agidan yari yadda nashaƙi iskar nan ai bazanso na koma ba batare da na waiwaya sosai ba, da dan gudu naƙarasa gidan namu ina saka saƙata narufe kofar nashige ciƙi. " Latyfah ce Nagani? Dady ya tambayi driver dinsa." " Alhaji da itace ai inajin zata jiyo gaba dayanta kuma wannan tanada ciƙi ajikinta kuma ramammiyace gaskiya banida tabbacin itace ranka yadade." Okay kawai dady yace suka karasa gidan zuciyarsa naƙara tafarfasa game da lamarin.

    Ke kuma daga ina haka kamar an hanƙadoki? Zuba mata idanuwa nayi ina faman haƙi tare da sauki ajiyar zuciyar a hanƙali a hanƙali, magana nake miki ina kikaje ke bakya tausayin ƙanki saboda Allah?. " Daman Awara Naje Na Nunnu nawa maƙota." " Ai da ƙin barni naje ko?" Bata idda maganarta ba sai ƙawai mukaji ana bugun kyauren gidan namu nidai ciƙina har juyawa yayi nayi maza dauƙar karamar butter nayi bandaƙi nama manta munada ruwa agidan nashiga ina addu'a. Iyami kuma taje ta buɗe kofar tana tambayar wanene sai wani dattijo yace awara yakeso ko banan baniba aka nuna? Tace ta nawa kakeso? Yace Ta dubu daya amma danya. Sosai iyami taji daɗi taje ta yanƙo masa kusan fiye da rabi dan dama a lissafin da muƙayi ta dubu da dari biyu ce ta dari biyun kuma sai iyami ta soye mana mukacinye.

   *****

Bance ƙi barmin gidaba? Me kikemin acikin daƙi? Wato ƙin maidani dan iska ? Wallahi tunda faɗima tatafi kema sai ƙin tafi Dady yafaɗa yana nunata da yatsa duk da ta durkusa har kasa tana bashi hakuri, ganin yana kara zafi yasata saurin fita tana kuka. Hameed kunna muga camera dinnan. Wallahi tun dazu nake gwadawa taƙeyi. Ali dake gefe yace ko nakira abokina yasan harkar irin wannan abubuwan sosai. Yaune nafarko da dady ya amsasa tun bayan dawowarsa dan haka jiƙinsa na rawa yakira amir akan yazo yasaita masa.Mintuna kusan talatin kamin ameer yazo ya hau saita musu laila datashigo da abinci ahannunta da farrah takawowa mahaifin nasu ta ajiye tana masa sannu da zuwa ya amsata kasa kasa duk hanƙalinsu na ƙan babbar TV din. Daukar irin wulakancin da Abdul yakeyiwa latyfah ne suƙa fara bayyana har sanda yaƙe watsa mata yawu kowanne jiƙinsa sanyi yayi dady kuma yabada uwarni da suyi gaba da wannan video din yanzunann, sai da aka duba date din da abun yafaru sai sukaga Abdul yashigo d
Palon tare da wata karamar yarinya aliyu yace wannan ai nawal ce, dady yace kasantane? . " Guri daya muke aiki dady ko da suka shigo da alama maganganu sukayi tunda babu murya daga nan kuma sukaga ta caka masa abu aƙansa sai kuma tayi ahnyar fita da gudu shikuma ya wadi daga baya kuma sai ga latyfah tashigo.Kowannen su yafaɗi innalilahi wainna illahirrajiun dady kuwa jiƙinsa har rawa yaƙeyi hatta shiƙansa ameer da bai san abunda ke faruwa ba sai da hanƙalinsa yatashi, sautin kuƙan dady yasakasu dagowa su ƙalleshi " Yaya zamuyi da haƙƙin yarinyar da batajiba bata gani ba? Har aka haɗa baƙi daku aka tozarta ta kukaita gidan yari kunkuwa san menene aciƙin gidan yari? Yafaɗa muryarsa tana rawa, laila da tafara kuka tace DanAllah kayi hakuri dady wallahi sharrin shaidan ne ni zamuje har gidansu mu basu haƙuri. Sallamar driver dayakeyi yasa hameed miƙewa da duk jiƙinsa yayi sanyi tabbas babu maƙawa gidan can gidansu latyfah ne kuma itace wacce yagani, driver ne yace ayiwa alhaji sallama nan Hameed yace masa bazai samu fitowa ba yadawo anjima yayi gaba sosai zuciyarsa take zafi ji yaƙeyi kawai ya nufi gidan nasu gadan gadan.

  Aliyu atabbatar anyimun bincike aƙan yarinyar nan! .

   Ƙarfe 3 Na Dare.

Tunda Nashiga gidan yari nafito sai sallah ta dare ta zame mun jiki yanzu duk daɗin bacci na sai na farka nayi alwala nayi sallah, haka ma yau ta kasance da wurwuri Na kwanta nakuma tashi karfe ukun dare, sai da nayi sallah raka hudu sallama biyu sannan na dauki qur'ani nashiga karantawa Najima ina karatun sannan nadaga hannu ina kuka ina yiwa Allah kirari tare da haɗawa da addu'oi Na sosai Nake roƙan Allah akan yarabani da ciƙin jikina lafiya, Dan kullum fargabata tsoron haihuwa ce! Ko da nagama addu'ar kuka nashiga rairawa ina tunanin maraici irin nawa daga wannan sai wannan in banda Allah ya tsallaƙar dani datuni har yanzu ina rayuwa acan gidan yari, ko tunawa nayi da gidan sai gabana yawadi  sautin kukana ne yasaka iyami tashi tana kallona tana faɗin Lafiya! " Haba latyfah damuwa kikeso kisakawa ƙanki kina shiga hakkin cikin nan naki, banda azabar dayasha yanzu kuma da hankalinki ya kwanta bazaki kwantar dashi ba? Kokuma ina miki wani abunne?" " Iyami kome kikayimin ai bana tunanin zan damu kece komai nawa nakashe miki komaj domin kizo kiyi rayuwa dani, kinada wasu jikokin amma kin sakani samansu ƙin hanani nayi kukan maraici tun bansan dadin uwa ba har kikazo kika ciki gurbinta, yaya kikeso inyi inyami damuwata dayawa narasa yazanyi in yakiceta? Idan abunda na haifa yazo duniya ya tambayi ina mahaifinsa me zance masa? Ance ni nakashe shi? Narasa sukuni iyami fargabata kara yawa takeyi." Kallona tayi duk da naga tsantsan tausayina atare da'ita Amma sai tacemin " Allah shine gatan kowannen mu ko da iyaye ko babu abunda Allah ya zartar shine daidai latyfah, kiyi hakuri kikara hakuri kikuma sani jarabawa bazata ƙare ba har sai mun mutu munshiga Aljannah Amma indai kina cikakkiyar mumina to Allah bazai daina jarrabar kiba share hawayenki hawi gado ki kwanta Allah yayimiki Albarka ya saukeki lafiya!.
Zafi da azabar ciwo shiyasa ni farkawa ƙarfe 8 nasafe salatin danakeyi shine abunda yajawo hankalin iyami ƙaina tatawo aguje tana faɗin haihuwar ce? Bari nasamu mai mashin duba da yanayin unguwar sai kayi tafiya mai nisa kamin kasamo napep haƙan yasaka iyami tana fita taga hameed kofar gidan mu jiƙinta har rawa yakeyi tashiga faɗin lafiya ɗan nan? Shima zuba mata ido yashiga yi yana nazartar ta ko bata gayamasa ba yasan akwai matsala jin sautin salatina yasashi fahimta haƙan yasa yace ta kamoni mutafi...

AYI MANAGE ZUWA GOBE BANGAMA EDITING BA🤩

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now