7

33 3 4
                                    

7

LATYFAH IMAM

Nana diso

   WANNAN SHAFIN NAƘINE HAJJ HAUWA🥰

Tsoro, firgici, kaɗuwa yanayi, suman hucen gadi shine halin da latyfah imam tashiga, atake idanuwanta suƙa kaɗa cike da ruwan kwallah mai nuni da hawayen da yaciƙa yafara bin kwancinta, gaba dayaa duniyar tata taji ta ɗauke mata wani ƙalar dumm kunnanta yayi yadda ƴar sandar maccen ta dagowata daga zaunen datake yasa tafara dawowa cikin hankalinta, tarasa me zatayi addu'a ko kukan kokuma ihu. Sautin kukan nawal da kururuwar da ammy takeyi yasata kara zubawa gawar Abdul idanuwa, atake tafirgita tare da gigicewa tana kallon ammy dake kokarin kwaɗa mata ƙarfe ana riketa " Kutafi da'ita ku kasheta kokuma kubarni nakasheta nazhiga uku tsinanniyar yarinya ta kashemin ɗa, daman kin auresa dan ki kashe shi?." Duk irin yadda aliyu da ammy ke zaginta bata dago ba sai idonta da yasauka akan taƙardar da tasakata ƙara fashewa da kuka, sosai ta wara idonta tashiga karantawa _NI ABDULKARIM MAI LEMA 'NASAKE KI LATYFAH IMAM BABUNI BABU KE'_ wani sabon hawayene yafara zubar mata zuciyarta kamar zata fashe saboda zafi, daya daga ciƙin ƴan sandan ne ya hanƙaɗata itakuma dayar tashiga tura ta tana kokarin saka mata ankwa. Alokacin ne takara shiga ɗimuwa rikici da gigita, " Ban kashe shi ba banice nayi kisan ba wallahi ban kashe shi ba." " Idan baku fita da'ita ba wallahi sai na kasheta ni cewar ammy tana jijjiga abdul da akashiga yimasa gwaje gwaje. Tare da jami'an tsaro da ammy da mumy harda aliyu fa umar aka tafi asubuti inda ammy tabada damar amakata a kotu. Mumyce tace " dadai kinbari angama bincike." Tana kuka kamar ranta zai fita tashiga faɗin" Haba mumy wanne kotu kina ganin tayi kisa nasan ta kashemin abdul ta kashemin ɗana tashiga faɗa tana mai rusa kuka." Aliyu ma da idonsa gaba daya yayi jajir saboda tashin hankali sai kiran wayar dady yake amma taki shiga haka ta yaya hamid shima taƙi babban yaron dady da aka tafi dashi shikuma tana shiga amma kuma ba'a dagawa. " I can't find them amiey akashe latyfah akasheta inbahaka ba ni zan kasheta yafaɗa kuka yana ƙufce mata.

   Karfin arzuki da rashin gata ba karya baniba ko ba'ayi maka bayani ba zaka tabbatar da mai kudi asaman talaka yake batare da anhuce da'ita police station ba akayi babbar kotu da'ita wanda tuni manyan ƴan sanda sun haɗa rahotunta na statement, bata gani bataji bata sauraro tadawo mahaukaci babu abunda kunnenta ke jiye mata saka da ta kasheshi? Haka tata kaddarar tazo wannan shine tukuicin alkhairi wannan shine sakamakonta, sauƙar babban kulki dataji akanta yasa hawayenta kara tsiyaya, ko da suka isa kotun akwai case na mutune sosai, amiey da mumy da duk wasu ƴan uwa da yaran mumy kowanne ya isa kotun domin na buƙatarsu nawal ma da mai gadi sun isa kotun, mubugun zuciyarta bazai iya bayanuwa ba radadin da zuciyarta take mata bazai iya lissafuwa ba, tashin hankalin da take ciki ƙanta yakasa dauka, acikin duniyarta ta haukaci ta makance takuma kuramce!

Ya mai girma mai sharia ayau 12 ga watan April munsamu case din matar da takashe mijinta ta hanyar caccaka masa kwalba akansa saboda zaiyi mata kishiya.

  Sai alok'acin ta dago ƙanta ta kalli alkalin tana kara rushewa da wani sabon kukan, iyami datashiga cikin ihu da kururuea tashiga faɗin wallahi bata kasheshi ba sharri za'ayi mata wallahi bata kashe shi ba karya sukeyi azzalumai, umarni aka bayar da fita da iyami dake tsinewa ahalin mai lema. Sosai ta runtse idonta zafin zuciyarta yana kara tsananta haɗe da zafin da kanta keyi.

  "Nine Barrister Suleiman nine lauyan masu ƙara."

  " ko zamu iya ganin lauyan wacce ake ƙara?"

  Ya mai girma mai shariah batada lauya.

  Tunda Barrister Suleiman yafara magana batace masa ƙanzil ba har yagama sai kuka datakeyi hakan yabawa kotu daga shariah zuwa nan  da watanni biyu karshen watan. " Dan haka kotu ta aika wacce ake tuhuma da laifin kissan mijin zuwa gidan yari. A hankali ta ambaci innalilahi wainna illahirrajiun tare dakara rushewa da kuka! Atake aloƙacin ƴan sanda suka shigo suka tafe da'ita amiey nata tsine mata albarka.takalmin da su laila suka shiga wurga mata yasa ƴan sanda tsawatar musu. Ko da aka fito iyami tana tsaye an rirriketa kallon iyami tayi tace " iyami an aikata ba banyi ba bansan tayaya hakan yafaru ba iyami anzalunceni." " nasani latyfah imam bazaki taba aikata ba bazaki taba ba Allah yatsinewa zuri'ar mai lema Allah yasakawa talaka abisa zaluncin da wasu masu kudin suke musu hajiya fatima Allah ya wulakanta ahalinki kamar yadda kika wulakanta ahalina inshaa Allahu zuri'arki sai sun wulaƙanta, daya daga cikin ƴan sandan ne ya kifawa iyami marin da sai data tsugunna saboda masifar zafi da radaɗi. Kukan latyfah imam ne yayi karfi ganin yadda suka zage suna duƙan iyami, duk yadda sukaso iyami tayi shiru batayi ba, ganin yadda suke duƙanta yayi yawa yasaka dpo din tsayar dasu.

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now