24

36 4 2
                                    

24

LATYFAH IMAM

Nana Diso

Bin ƙofar data fita nayi da ƙallo kamin kuma in ɗan gaggauta gurin shafa mai,  nasaka wani yadi da iyami taje kasuwa ta siyomin aka dinƙamin idan nasakashi inajin daɗin jiƙina sosai, motsin da cikina yakeyi yasani ɗan dakatawa ina mai faɗin mashaa Allah ina shafa ƙan ciƙin nawa da yayi girma sosai, jin cikin naƙeyi har cikin raina yanzu, kaunar abunda zai fito daga ciki nakeji tun kamin yafito, a duk lokacin  da na tuna nakusa zama uwa sai naji daɗi araina, awani bangaren kuma baƙin cikin wanda yazama sanadiyar cikin nakeyi. Tunawa danayi kirana fa akeyi yasakani zumbula hijjabina nafita, ada leɓena koda yaushe abushe yake amma yanzu mama dayake ƴar gayuce lipgloss take sawa ina shafawa. Ahankali na tura hannuna kofar da zata sadani da palour salama nayi aka amsamini samun gefen iyami nayi nazauna ina nazartq wanda suke falon malam yakubu ne da Barrister salisu sai wani mutum da ban sanshiba mama ma na gefen mijinta , cikin ladabi da girmamawa nagaishesu suka amsa, malam ne yace ƴata yajikin naki babu inda yake miki ciwo ko?. Batare da na'iya amsa masa ba naji hawaye yanabin fuskata, tunani na zan koma can gidan yari ne duba da takardun da suke hannun Barrister salisu. Dafani da iyami tayi yasani saurin dago ƙaina ina kuka nace masu ɗan Allah kubarni in haihu cikin dake jiƙina bashida laifi danAllah nafaɗa ina mai fashe musu da kuka mai taɓa zuciya, hakan yasa jiƙin duk wanda yaƙe daƙin yayi sanyi kowannen su yana ƙallona, malam ne yace " Latyfah babu inda zaki koma domin ankashe case dinnan tun kwanaki." Da hanzari duƙanmu muka dago muka kalleshi banda mama da tanuna alamun tasani. Barrister tani yace bayin Allahn da suka daukeni nayi muku shari'a sun kashe case dinki gaba daya ba komawa gidan yari ba ko record baki dashi na tuhuma yanzu sannan yashigar da kara akan bata miki suna da akayi, bayan nan kuma ya tabbatar da bakiyi kisa ba." Da hanzari na ƙallesa ina cikin tsananin mamaki.Cikin Farinciki yacigaba da bayani yana miƙomin wasu taƙardu da yaƙarba ahannun wannan mutumin dake kusa dashi yace " Wannan yautace ta har abada daga hannun alhaji auwal dogo shine wanda yayi kokarin ganin an kashe wannan case din naki tare da dauƙarmiki fansa, mamaki bai cikani ba sai danaji su mama da malam suna godiya iyami itama ta fashe da kuka tare da godiya, kallonsa nayi idona na hawaye nace banaso nagode wannan shine abunda yafaru da farko har akazo har gida aka tozarta iyayena bansan abunda yake nufi dani ba shima tunda shi talaka ba komai baniba agurin mai kudi. Haba latyfah imam baikamata kifaɗi haka ba itafa kaddara bata zarce ƙan kowa. Kallon mutumin da yayi magana nayi nace masa " Aminiyatace Nana bata..." bankarasa ba malam yace duk wata kaddara ta bawa zartacciyace nana ko waninta bai isa ya fiddaki daga halin da kike ciki ba sai sarkin da ya halicceki idan duniya da mutanen cikinta zasu taru don su fiddake sai da yardar Allah banaso ki dorawa kowa komai akan wannan jarabawar taki ki kuma godewa duk wanda Allah yabashi iƙon taimaka miki dan baisa ya taimaka miki ba sai da iko na Allah. Sosai Na shiga rera kuka duk falon shiru sukayi sai da Barrister salisu yace min inaso kibani haɗin kai gurin yin bincikena na gaba inaso in tambayeki ko akwai wata camera agidan da kuka zauna, kowa yasan gidan Alhaji Alhaji mai lema akwai security shine nakeso na tambayeki shima gidan naku akwai? Shiru nayi na wani lok'acin kamin naji natsani maganar dan ko sunan abdul ko mahaifinsa bana ƙaunar inji, nace musu bai bani damar kusantarsa insan komai akansa kuma idan ma akwai ai bana tunanin kusamu dan azzaluman bazasu bar shaidar komai ba nan fa iyami ta rufeni da faɗa shine na sassauta ina masa bayani kasa kasa yadda zasu fahimta, to madallah idan Alhajin yadawo tunda kusa dashi kuke sai kishiga kiyi masa godiya.  Galala nayi dan ni naƙafe bazan karba ba, Nan Barrister dasu mama suka shiga bani haƙuri Nakuwq turje akan banaso shidai baice komai ba suka fita duna godiya ga junansu aka miƙomin taƙardu a hannuna akabani, nabi iyami daƙinta ciƙin bakƙonta nasaka tana faɗin gobe goben nan zamu tashi ai mutanen sunyi mana dama tafara bincika mana gidan haya haƙan yasa na dawo hanƙali sosai. Bance kuma komai ba nayi shiru sai nayi hanyar bamgaren malam dam inaso yayimun izini zanje asubuti dan yadda naƙeji ina buƙatar likita, kuma banida kudi a hannuna nikuma ban dauka iyami tanada ko sisi dole dai sai naje gurinsa zan samu banƙarasa ba naji sautin muryar mama tana faɗin haba " malam wayazugaka kaketa faɗa duk abunda zakayiwa iyalan imam ai bazaka biyasa ba tundaga ƙauye ya dakko ka sannan yabaka ilimi yakuma maka aure dan ka hidimtawa yaransa ai naga baƙomai baniba ko? " " bazanyi ba wayasani ko gaskiyar ita tayi kisan ki duba fa kiga ciki suma ahalinsa sun ƙaryata ina kuma gamu? Wayasani ko cikin nawanine agidan yari? Wayasani? Kiduba daga yimusu hanya wai har alhaji yabata gida sai na shiga na fita yaƙarbe gidan nan." Sai najiyo mama tanata sallallami saboda sabon abu taƙeji adaɓi'ar mijin nata ai ban rufe baƙi ba naji sallamar umma haƙan yasani saurin juyawa na nufi daƙin iyami ganina yasata tambayar lafiya nace mata maza haɗamana kaya muje mu zauna akyautar da Allah yayi mana nafaɗa ina goge hawayena itama tayi mamaki amma ta lura sosai da rashin murnar malam din wanda bata taɓa tunanin haƙa ba to amma tunda idi yayi haƙan shima batayi mamaki ba ta haɗa ƴan ko matsan mu gaba daya basufi bakko biyu ba na dauki daya ta ɗauki daya muna fita muka tarar da malam a palour a zaune shi da umma mama da tadago tace mana lafiya taganmu da bakko har kasa na durƙusa ina mata godiya nakarasa kusa da malam shima nayi masa godiya da addu'oi masu sanyaya rai can najiyo umma tana faɗin " To saboda Allah inakai ina karuwa ƴar ta'adda agidanka malam da mutunci da ƙirkinka agari da darajarka kaje ka dakkowa ƙanka masifa." Daga ni har iyami bamuce komai ba sai da mukayi hanyar fita sannan malam yace " Allah yaraba lafiya." Nayi masa godiya sosai sannan nashige umma nata kwashe min albarka bance mata ci ƙanka ba haka iyami na hanata magana baƙaramin ciwo abun yayiwa mama ba har ta biyomu tana bamu haƙuri takuma ce gobe zata zo unguwar zata kira iyami. "Ko da muƙa fito Titi samun guri muƙayi muka tsaya iyami tace bari taƙira Barrister awayarta ciƙin ikon Allah kuwa yadaga yace mata mubashi minti 20 zai ƙaraso inda muƙa tsaya, yunwa naƙeji sosai haƙan yasa nazari dubu daya aƙudin da mama ta turamin aciƙin leda na nufi can gangare inda naga shago, nayi sa'a kuwa ɗan inazuwa na tarar da egg roll da lemo nasiya nadawo mun ɗan jima agurin kamin Barrister yaƙaraso yana bamu haƙuri sosai akan sabanin lokacin dayayi ashe shima yafahimci malam baiyi murna da al'amarin ba harma wai bayan fitarsa yakirasa awaya yakeci masa tunda yarinyar ta nuna bataso me zai hana ahakura kawai kokuma su siyar shida Barrister su raba kuɗin shikuma Barrister yace Allah yakiyaye. " Wallahi lauya mutane har sun daina bani tsoro." " Nima nayi mamakinsa iyami bantaba tunanin zaiyi haƙa ba amma damam mutane ai hassadarsu tana fitowa ƙarara ne. Nidai ina sauraronsu bance musu komai ba duba da yadda naƙejin jiƙina babu dadi babbar unguwa muƙa karasa manyan gidaje ne sosai alayin can gefen titi nagano wani kirarren gida mai girman gaske a waje ma ya haɗu ina ga ciki, sai da muka huceshi kadan sannan na hango wani babban shima dai bai ƙai wannan girma ba gaskiya, motar tamuce ta tsaya agefen wani ɗan matsaƙaicin gida yayi kyau sosai ni da fari ma ban dauka shi aka bamu ba sai da naga yafito daga motar ya buɗe da muƙulli sannan muƙa shiga kowannen mu da addu'a acikin baƙinsa, hawayene yashiga bin fuskata yanzu da Allah bai dubemu ba yaya zamuyi dani da iyami filin gidan bashida girma amma tsarin ginin gidan na zamani ne sosai dan mota guda daya zata iya shiga, ko da yabude falon kujerace mai dan kyau guda hudu babu TV babu fridge sai cikin daki da muka samu gado irin dai na ɗan talaka ashe Barrister ne yayi mana da kudinsa nan iyami tashiga yimasa godiya nima naƙarba haɗe dayi masa addu'oi.  " iyami idan Allah ya kaimu wani satin Wancan gidan dakike gani shine gidan da alhaji auwal dogo zai dawo sai kuje kuyi masa godiya yanzu ma zan baku numbarsa kukirashi ko bai daga ba kukara kiransa kuyi masa godiya dan nima nayi mamakin wannan kyauta dayayi kinsan irin kyautar nan sai ƴan uwanka najiki." " Tabbas hakane lauya, Zamu kirasa inshaa Allahu." " ke kuma latyfah kiyi hakuri komai na rayuwa yanada farko da karshe kada dan wannan abun yasameki kiyi tunanin babu wanda zaki kara hulda dashi kokuma kidinga yiwa kowa jam'u Allah shiya kaddara komai kuma yafitar dake ayi hakuri, ni zanyi tafiya ne kuma zan kwana biyu ga wannan babu yawa yamiko dubu 20 yabawa iyami, dafari ƙin karba tayi sai da yace ko ta raina ne. Yayi mana sallama yatafi. Tashi mukayi muka zaga gidan muna murna kowanne da abunda yaƙe sakawa kasancewa kitchen din babu komai sai tukunya a kwali da flask da plate, babu abun girki hakan yasa iyami dakko kudin da yabayar tace zataje tasiyo wasu abubuwan ita tamafi son kurfoti sai musiya gawaye " To ai iyami mama tabani kudi ta miko mata ledar bayan na zauna akasa itama kusa dani ta zauna ta buɗe ledar tana lissafa kuɗin harda taƙarda aciki mamaki ne yakamamu ' _WANNAN KUDIN DA KUKE GANI GASHINAN DUBU DARI DA SABA'IN NE MALAM YACINYE DUBA TALATIN SAI KI YAFEMASA LATYFAH DANALLAH ALMAJIRAN MAHAIFINKI NE SUKA HAƊA MIKI NA HAIHUWA NIKUMA SAI NA BOYE MIKI KWAYI ANFANI DASHI KO DA MALAM YA ƘOREKU_ Duk sai mukaja ajiyar zuciya muna mamaki. " To yanzu iyami sana'a zamu fara." " Daman nayi tunanin haka ko mufara siyar da awara." " Eh to tunda ƙin iya sai dai mu zamanan tar da'ita musiyo takeaway mudinga yi harda sauces kinga unguwace ta manyan mutane sai kiga muna ciniki can kasa nagano shago na awo da wani store bari naje nasiyo." " A'a tashi muje dai tare tunda naga ke so kikeyi ki motsa jiƙi ko? " murmushi nayi nasaka silifas dina muka kulle gidan muka fita muna tafe muna hira har muka gangara nan fa iyami tasiyo waƙen suya kwano 5 tasiyo mai maggi gishiri muma ta auno mana shinkafa kwano 2 tasiyo mana tsaƙin masara kwano biyu, sannan muka siya taliya ta awo da macaroni a lalace dai sai da muka kashe kusan dubu 30 kamin iyami taɗan mika taje tasiyo mana kurfoti da gawaye buhu daya shima muka samu Napep aka loda masa nikuma nashiga cikin store din nasiyo takeaway da cokali harma da ledar thank you itama nasiya nasiya mana vasiline mai arhan nan babba sannan nasiya mana brush da macline nasiyo mana sabulun wanki dana wanka can nagano wani cream duk da naga ansaka fair ajiƙinsa amma sai naga ƙamar wanda mama tasiya ne naƙe shafawa ina dauƙa naga ansaka dubu biyar da sauri na ajiye sai ma aikacin yace hajiya idan yanada kyau ajikinki ki daure kisiya hakan yasani dauka dai amma gaskiya banso ba da dubu biyar dinnan ai zan kara wasu siyayyar amma yadda naga macce yanzu sai da yagyara. Haka muka siya komai muka hau napep yamiƙamu har ciƙin layin mu, wata babbar mota ta masu ƙudi ce tazo ta hucemu amma sai naga ƙamar an dan tsaya dana ƙalli motar sai naga baƙin abun mota alamun su suna ganin mu mu bama ganinsu. " Alhaji hameed wannan kamar matar abdulkarim, jiyowa yayi yana kallona sai kuma sukaja motar suka tafi. Mai napep kuwa harma yataimaka mana da shiga da wasu kayan ciki ashe har kayan miya Iyami tasiyo dana shiga store din, nan muka zage sosai muka shiga gyara wajen muka jira komai iyami ta wanke kayan da ta tsinto mana a gwanjo nikuma nahaɗa gawaye Na dora mana farar shinkafa na yanka salad kafin tagama na daƙa yaji sannan na sauke shinkafa nadora ruwan wanka nashiga bandaƙi nayi wanka, nan muka zube muna cin abinci anayin magariba kuma mukayi sallah muka jira isha'i muka kwanta.

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now