*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_©️ *OUM MUMTAZ.*
_No: 2_
Karfe goma da rabi da daren ranar Lawal ya shigo gidan bakin sa dauke da sallama, Umaima da take zaune tana kallon wani film da ake haskawa a tashar MBC2 sabida akwai nepa lokacin, ta ansa masa fuska sake tana masa sannu da zuwa, Zama yayi a gefen ta ya ansa mata sannu da ta masa yace, "Kallo kike ba kiyi bacci ba?"
"Eh wallahi, film dinnan nake son a karasar, gashi kuma na jika shiru baka shigo ba nace Allah yasa lafiya."
"Ina kofar gida tare da Yusuf shiyasa ban shigo da wuri ba,Babana yayi bacci kenan?"
Ya tambaya yana leken fuskar Amir da yake bacci cikin gidan sauron sa na yara fankar kasa tana kai masa iska."Yayi bacci amma fa sai da nasha rigima kasan halin mutumin."
"Gaskiya kam Amir rigimar sa sai ke zaki iya dashi."
Yace a sanda ya tashi ya shiga daki hannun sa rike da wata bakar leda da Umaima bata san miye a ciki ba taci gaba da kallon ta.Tsawon mintuna ya dauka kamin ya fito, wanda fitowar tasa yayi dai-dai da sanda aka dauke wuta, yayi amfani da wayar dake hannun sa ya kunna torchi yana cema Umaima ta kashe sucket din TV, shi kuma ya shiga gidan sauro yabar mata tocilar wayar tasa kunne, sai da ta kashe sannan ta fita taje tayi wanka, daki ta shiga ta shafe dik wani lungu da sakon dake jikinta da wani daddadan khumra da Maimuna ta aiko mata jiya da bata taba amfani dashi ba.
Riga da wando masu laushi da suka kasance na baccinta ta saka tare da hula mara nauyi ta fito da mahuci a hannu ta shiga gidan sauron ta danne musu.Kwanciya tsakiyar Lawal da Ameer tayi tana kallon Lawal da ya ke danna wayarsa yana game din maciji, wanda a lokacin wayar android bata gama shigowa hannun mutane ba sai kananun waya. Kamshin da Umaima yaji tana yi ne ya sa shi kallon inda take a hankali yace, "Wannan Kamshin turaren yayi min dadi sosai Umaima ta."
Yayi maganar a sanda yake janyo ta jikinsa yana shakar Kamshin sabida ba karamin dadi yayi masa ba.Cikin kunnensa itama tace, "Thank you Sweetie." A salon yadda yayi mata maganar.
Hirar suka fara na soyayya dake cike da shauki, wanda Umaima tayi amfani da wannan damar wajen shigo masa da bukatar ta.
"Auren Hamidar yaushe ne?" Ya wurga mata tambaya a sanda fuskar sa ta fara dinkewa daga fara'a zuwa akasin ta, sabida shi fa yana daya daga cikin mazan da wallahi ko da wasa basu da hannun kyautar kudi wa matan su ballantana kuma wasu yan gama gari.A hankali tace, "Saura satu uku, bayan salla da sati biyu kenan." A ranta tana addu'ar Allah da daura ta akan sa ko da bazai bata duka ba.
"To kinsan dai nima din ba wani kudi ne da ni ba, talaka ne dake fafutuka wajen ganin na samu na kaiwa bakin salati, dan haka magana ta Allah bazan iya baki naira dubu goma sha biyar kiyi kyauta dashi ba ni ina nan baki bude,amma gobe da safe idan Allah ya kaimu zan baki dubu biyar ki bayar Allah yasa mata albarka tinda dai kinsan,baki da gashin wane ba lallai ne kiyi irin kitson wane ba, suma kuma sun san baki dashi tinda ba sana'a kike ba."
Kallon sa tayi cikin duhun tana jin wani bakin ciki da takaicin maganar sa ta karshe, wai ita ba sana'a ba? Ko ya manta cewa shine ya hana ta sana'ar kan dalilin sa mara kan gado wai don kar mutane suyi tunanin ya gaza kula da iyalinsa har sai ta hada da sana'a? Sannan kuma idan shi ya manta ai ita bata manta ba, yanda ya kasa ya tsare a lokacin da ta fara sana'ar saida murhun gawayi da su kayan miya tana samun taron ta da kwabo yake bin dare yana kwashe mata su har sai da ta gaji tayi masa magana, shine ya fara borin kunya kan baza ta sake masa sana'ar kaskanci ba a gida tazo tana daura masa cewa ya daukar mata kudi, tin daga ranar yace wallahi koda bai sani ba idan ta sake ta kara yi masa wani abu da sunan sana'a cikin gidan nan a bakin auren ta, amma shine yanzu tsabagen ya raina mata wayo zai wani ce mata ita da ba sana'a take yi ba?
Danne zuciyar ta tayi wajen ganin bata fada masa bakar magana ba gudun samun sabani da wannan daren da dik al'ummar gidan suke bacci tace, "Hakan ma na gode Allah amfana."
YOU ARE READING
LOKACI NE
RomanceTa zaɓe sa sama da farin cikin mahaifiyarta a dalilin shine zaɓin zuciyarta kuma farin cikin zuciyarta! Dawowarta daga gidansu da tayi tsawon kwanaki takwas a dalilin rasuwar mahaifinta kwatsam sai ta tarda mijinta ya ɗankaro mata kishiya ba tare da...