Page 12

33 2 0
                                    

*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_

©️ *OUM MUMTAZ.*

_No: 12_

"Abban Amir dan Allah idan akwai wani abin da na maka, wanda ban sani ba, ka yi hakuri ka yafe min, bazan iya jure wannan yanayin naka ba ka tausaya min." Umaima ta fada cike da sanyin murya, tana zube kan gwiwowinta gaban Lawal da yanzu shigowar sa gidan.
Lawal da yaji numfashin sa na ƙoƙarin ɗaukewa sabida tsananin warin da yake shaƙa da ga wajen ta yayi hanzarin ficewa daga parlon wani irin amai ta taho masa gadan-gadan, a bakin barandar parlon ya tsuguna ya dinga kela amai sabida tashin zuciya. Umaima da take nan a yanda ya bar ta, hawaye na zubo mata wani na koran wani ta taso da hanzarinta jin aman da yake, kaman zai zubo da kayan cikinsa. Lawal da yake neman fita hayyacinsa kuma jin wannan warin yana sake doso inda yake yasa wani aman sake taho masa da tsananin ƙarfi, isowar ta wurin kuwa ji yayi lumfashin sa ya dauke na wucin gadi, ya tattaro dikkan wani ƙarfin da ya rage masa ya hankaɗa ta daga ƙoƙarin dafa sa da take, wanda hakan yayi sanadiyar faɗuwarta ƙasa war-was, sabida taji yanda abin yazo mata a un-espected,wanda hakan yayi sanadiyar da goshinta ya bugu da jikin windo.
Kuka mai tsananin ƙarfi Umaima ta fashe da shi mai cike da tashin hankali, domin kuwa dai ita a iya tsawon zamanta da Lawal ba za tace ga wani taƙamai-mai laifin da ta aikata masa ba da har ta cancanci fuskantar wulaƙanci da kuma ƙasƙanci daga wajensa. Ga kuma azabar da take ji a goshinta da yasa ta rintse idanunta.
Lawal kuwa tin hankaɗa ta da yayi da gudun gaske ya fice daga gidan, ya samu kan wani dutse da yake kofar gidan karkashin wani bishiya ya zauna, yana mai da lumfashin wahala.

Umaima

Sai da taji kan ta da zuciyarta sun lafa mata daga radadin da suke mata kafin ta mike da niyyar shiga dakinta, sai kuma ta dakata sabida ganin inda Lawal yayi amai, wanda hakan yasa ta zagaya wa bayan ɗakin ta inda suke ajiye abin zuba shara ta ɗauki faka, har za ta juya haka nan taji kawai bari ta daibi ƙasar da za ta je ta rufe aman da shi, ta sunkuya kusa da bolar wajen da taga alamun ƙasar gurin zai yi daɗin ɗeba, cika fakar tayi da kasan wajen taje ta zuba amman bai rufe mata yanda take so ba, hakan yasa ta sake komawa taje ta sunkuya da yake ba ta jin ƙarfin jikinta kawai sai ta zauna a wajen, tana cika hannun ta dika biyu tana juye wa a fakar, hannun ta ne ya sauka akan wani dunkulallen tsumma da aka yi ma kyakkyawan dauri,har za ta wurga abin shara sai kuma tayi sak, da mamaki Umaima take kallon kyallen sabida sak irin na dan kwalin ta da sati daya da ya wuce taga an yankar mata, wanda take mamakin wanda zai aikata mata haka, sanin da tayi cewa a tsawon zaman ta hakan bai taɓa faruwa da ita ba, zuciyarta ce ta umarce ta da ta kunce.
Gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin laya ce cikin ƙyallen ɗan kwalin, wanda hakan yasa ta miƙe a kidime ta fara warware wa, tana gamawa kuwa wani farar takadda ta fadi ƙasa, jikinta yana karkarwa ta sunkuya ta ɗauko, ba ta damu da tsananin warin jabar da yayi ma hancin ta maraba da zuwa ba, wani mitsitsin gawan jaba ya faɗo daga cikin takaddar a lokacin da ta gaba buɗe linkakkiyar takardar, sunan ta ne ya bayyana ɓaro-ɓaro da harshen larabci 'KHADIJA USMAN BAƘO', sai kuma daga kasan sunan ta aka rubuta 'LAWAL SA'IDU MARAYA' dik da harshen larabci, sai kuma wani chakuɗaɗɗen yaren da ba ta fahimta ba, inda ta tsinto 'LAWISA' rubuce da manyan harrufa na ABCD daga can ƙasa.
Zufa taji ya jika mata rigarta sharkaf, sabida tashin hankali sai faman zare ido take, domin kuwa indai a yanda tayi hasashe da kuma tunanin ta ya bata dai-dai to tabbas warin da Lawal yayi iƙirarin tana yi akwai saka hannun Lawisa dumu-dumu, wanda idan ba ta manta ba jiya da safe sai ta tayi mata wata da magana wanda a lokacin Umaima ba ta bai ma maganar mahimmanci ba sai a yanzun da take ganin wannan abu mai kama da almara, tana tunanin mai nene Lawisa ta ɗauki duniyar da har akan ɗa namiji za ta iya yin shirka sannan kuma ta hada ta da warin jaba don kawai sun hada miji? Wanda inda ace zafin kishi ne ma ita ya kamata ta nuna sabida a irin yanayi na wulakanci, kaskanci da cin amanar da Lawal yayi mata a lokacin da zai auro ta? Ta ɗauke kai ta nuna komai ba komai ba dik don sabida a zauna lafiya amman shine ita Lawisa ta rasa da mai za ta saka mata sabida son zuciya sai warin jaɓa?
Umaima tana kuka da majina yana zuba a hancinta, ta ɗauko ashana tazo ta cinna ma shirgin layar wuta, bayan tayi dogon addu'oin neman tsari daga mutum da aljan,aman da ba ta kwashe ba kenan tayi shigewarta daki tana kukan da ta jima ba tayi irinsa ba, inda ma Allah ya taimake ta Amir yau bai ma kwana a wajen ta ba, can gidan Maimuna jiya Amina tazo ta dauke sa suka tafi.
Ba ta san tsawon lokacin da ta ɗauka tana saƙe-saƙe ba, taji muryar Lawal yana kwaɗa mata kira da yasa gabanta ya yanke ya faɗi, dik da wani sashe da yake zuciyarta na tabbatar mata da cewa wata ƙila kukanta ne yazo ƙarshe sanadiyar ƙona wannan layar da tayi, da gaggawa ta mike tsaye tana kallon Lawal da ya shigo dakinta, wanda ko da gigin wasa tin last week da ta gama jeran kayan ta bai sake shigowa ba.

LOKACI NEWhere stories live. Discover now