Page 6

47 2 0
                                    

*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_

©️ *OUM MUMTAZ.*

_No: 6_

*Lawal*

Akoi wata yarinya da take sayar da abinci cikin kasuwa wajen sana'ar sa, wanda a lokaci zuwa lokaci yana sayan abinci a wajen ta a ranar da bashi da ra'ayin komawa gida cin abinci, sannu a hankali shakuwa mai girma ya shiga tsakanin sa da yarinyar mai suna Lawisa, wanda cikin shekara daya wannan shakuwar tasu ta rikide zuwa soyayya mai girma tare da alkawarin aure ma junansu.
Lawal a nasa fahimtar da yayi ma Umaima kasancewar ta mace mai tsananin kishi a kansa sabida kalar son da ta ke masa, idan ya tsaya lallaba ta akan cewa zai kara aure, to tabbas ba za su wanye lafiya ba, ta dinga daga masa hankali kenan, wanda shi kuma ba ya jin ko duniya da abinda ke cikin ta zasu taru akansa zai fasa auren Lawisa, hakan yasa shi kirkiro ma Umaima wasu halayen da bata san shi da su na ganin ya cusguna mata sabida ta tsorace sa da kuma fushin sa, na yanda ko ya bijiro mata da zancen ƙarin auren sa za tayi shayin tayar masa da hankali sabida tasan ba zai raga mata ba idan tayi abinda ba shine ba,ba wai don ya daina son kayarsa ba.
A lokuta da dama idan yayi yunƙurin sanar da ita dangane da abinda ya shafi ƙarin auren sa, amman sai ya kasa sanar mata wai don gudun kar ta tayar masa hankali, wanda hakan yasa har auren yazo gadan-gadan amma ba ta da labari, gashi kuma babu wanda ya taba tinkarar ta da zancen a yan uwan Lawal din da su a nasu fahimtar Lawal ya riga da ya faɗa mata, har ma idan sun ja gefe suna gulmar ta na ganin yanda take ramewa don mijinta zai kara aure, sai kace akan ta farau kishiya, su basu san damuwar ta ya bambanta da abin da suke tunani ba. Ko da yake ba abin mamaki bane duba da cewa ba wani shiri suke da ita ba, sabida kafin ya aure ta suka so yayi auren haɗin gida da wata yar uwar sa kaman yanda suke cikin families ɗinsu, amma Lawal da yake shima rigimammen kansa ne namijin duniya yace bai san wannan ba, babu wanda zai masa tilas akan kalar matar da yake son aura, hakan yasa suke ganin kamar har da saka hannunta.
Ba tare da masaniyar Umaima ba, Lawal yaje yayi ginin gidan sa a can wani unguwa mai nisa daga cikin gari, wanda tsarin gini ne mai fasali da zai ɗauki mace guda, da farko Umaima ya so maidawa gidan sabida yanayin zaman gidan nasu sai mai haƙuri kamar Umaiman da yake tsoron halin yan gidan nasu ya sa hakurin da take yi dasu ya kare, amman kuma da zancen aurensa ya ta so gadan-gadan sai ya fasa wannan kudirin nasa yace amaryar sa zai saka a gidan, a hankali kuma idan abubuwa sun sai-saita sai itama yayi mata nata ginin. Auren sa saura kwana shida, suka yi faɗa da Umaima har ya gaggaya mata maganganu akan ta titsiye shi da tayi sai ya faɗa mata abin da tayi masa da ya tsiro mata sabbin wulakanci akan abin da bai kai ya kawo ba. Wanda hakan yasa shi rufe ido dikda yasan ita ce mai gaskiya ya ringa bal-bale ta da masifa da baƙaƙen maganganu, tare da alwashin a zuciyarsa bazai ma faɗa mata batun auren nasa ba sai bayan an ɗaura idan ya so ta haɗiye zuciya ta mutu dan baƙin ciki.
A daren ranar kuma Babanta ya ƙira sa a waya, yayi masa nasiha mai kama da wasiyya, tare da nuna masa mahimmancin kwanciyar hankali da ake buƙata a rayuwar aure, bude ma mace wuta ba shi yake sa mace ta tsoraci miji a gidan aure ba, wanda maza da dama basu fahimci hakan ba, su gani suke tsare gida da ɗaure fuska tare da wulakanta mace shi yake sa taji shakkar su ba, sai ma hakan yasa idan da fari tana shakkar su sai raini yazo ya biyo baya garin naiman gira a rasa ido baki daya. Wanda a ranar Lawal kwana yayi yana mai jin takaicin abubuwan da yayi ma Umaima, tare da alkawari ma kansa washe gari da safe zai naimi sulhu da matar sa tinda dama can ba wai baya son matar sa bane, ya kuma sanar da ita batun aurensa tare da naiman yafiyar ta akan musguna mata da yayi cikin aurensu akan laifin da ba ita tayi masa ba.
Sai kuma washe gari da safen suka riski rasuwar Baba, wanda Lawal zai iya cewa bayan mutuwar mahaifiyarsa da mahaifinsa babu mutuwar da ta girgiza duniyar sa sama da ta mahaifin Umaima.
Ranar da akayi sadakan uku aka ɗaura masa aure da Lawisa, wanda shi ya so a dage auren zuwa bayan sadakan bakwai idan Umaima ta dawo cikin hayyacinta, yayi mata bayani, sabida kar ta dauke sa a wanda yaci amanarta yayi mata kishiya a sanda take can wajen rasuwar mahaifinta. Amma sai Lawisa itama ta bude masa wuta sosai, har tana ikirarin za ta rabu dashi na har abada idan ya kuskura ya bari wannan ranar ta wuce ba tare da an daura musu aure ba, shi kuma Lawal da yake a lokacin so ya rufe masa ido, ba ya jin ko da wasa zai iya bari Lawisa ta kufce masa, sai ya bari aka ɗaura auren, a ransa yana faɗin idan Umaima ta dawo yasan za ta fahimce sa idan ya zauna ya tsara ta.
Ɗaurin auren nasu da aka yi a ranar bai bari Lawal ya samu damar ƙiran Umaima a waya ba, ballantana ya je gidan, har washe gari akayi rakiyar ango zuwa wajen amaryar sa,abin ku ga maza mutanen mu Lawal sai ma ya mance da babin wata Umaima, yake zuba angoncin sa babu kama hannun yaro, domin kuwa dai kowa na da sanin amarya ko ta buzuzu ce ana ɗaukin ta ballantana kuma mace irin Lawisa da babu abinda ta naima ta rasa a komai da ake buƙata a wajen ko wacce ɗiya mace.

LOKACI NEWhere stories live. Discover now