Page 13

42 3 0
                                    

*LOKACI NE*
_Fitattu Biyar_

*©️OUM MUMTAZ*

        _No:13_
  _Last free Page_

"Sai na zama ajalinki Umaima,sai na rusa miki farin cikin rayuwarki kaman yanda ki ka rusa min farin ciki na a wayewar garin yau, bayan wannan abinda ki kayi min shine har kike da bakin da zaki iya zagi na,sannan ki zagi ubana? Kuma magana da ki ke akan wani ke ya kamata ki nuna kishi ba ni ba shi Lawal ɗin uban waye yace miki don ke kaɗai aka halicce sa? To wallahi ki rubuta ki ajiye ko ta halin yaya sai Ni Lawisa na kawo karshen zamanki tare da Lawal, sabida Lawal nawa ne ni kadai,ba ayi wata macen da zan bari tayi rayuwar aure da shi ba, tunda shi da bakin sa yasha furta min babu macen da ya taɓa yi ma ko da kwatan-kwacin kalar son da yake min, wanda bai cire ke ma daga ciki ba, da ya tabbatar min da cewa ko wajen shimfiɗa ke ɗin zero ce babu abinda ki ka iya sai dai ki tsaya masa ƙiƙam kamar dusa,shi yake kiɗan sa kuma yayi raw..."
Umaima ta katse Lawisa daga dogon zancen da take cikin tsananin fusatar da ita kanta bata san tana da shi ba ta hanyar watsa mata wani lafiyayyen mari da nan take hancin Lawisa ya ya fara zubda jini. "Ga ki ga nan Lawal ɗin ai jaka ballagazar mata,jahila da bata san abinda yake mata ciwo ba, naji takaici matiƙa da ya zamana cewa ni da ke munyi tarayya akan namiji guda Lawisa,amma ki sani idan ma abinda kike akan dai-dai ki ke za ki gani a ƙwaryar cin tuwonki." Umaima ta ƙare maganar ta da wani ɗaci cikin muryar ta na abinda Lawisa ta ke faɗa, wanda tayi iya bakin ƙoƙarin ta da ba ta bari kukan baƙin ciki ya kubce mata ba.
Lawal da ya sunkuyar da kansa ƙasa saboda tsakanin kunyar da ya kama sa akan ɓaran-ɓaramar da Lawisa tayi masa,wanda shi a lokacin da ya furta mata hakan yana kan ganiyar cin amarci da bai taɓa tunanin akwai ranar da Lawisa za ta furta hakan ga wani ba, ballantana kuma Umaima. "Dan Allah kar ki dauƙi maganar wannan jakar matar,sharri take ƙoƙarin laƙa min saboda kawai ta haɗa ni da ke wajen ganin ba muyi zaman lafiya ba,amman kinsan ke ma daga jin wannan maganar ai ko da wasa ba zan iya furtawa a gareki ba." Lawal ya ƙare maganar a ransa kuwa addu'a yake Allah yasa Umaima ta yarda da abinda ya faɗa mata domin ya kare kansa.
Kamin Umaima ta yi magana Lawisa ta daka wani uban tsalle sai gata a gaban Lawal ta cakumi kwalar rigar sa cike da zallar masifa da rashin ɗa'a tace, "Amma dai ban taɓa sanin kai ƙungurumin munafuki bane sai yau, wato tsabagen iya ƙwarewa a munafurci muyi maganar tsakanin ni da kai shine har kake da bakin ƙaryata ni, hakan kuma bai ishe ka ba sai ka haɗa da danganta ni da jakar mata? Ashe kai dan akuya ne...."
Lawal da yake jin zuciyarsa na tafarfasa akan irin ɗibar albarkar da Lawisa take masa bai san lokacin da ya kai mata wani wawan naushi a bakin ta ba,wanda hakan yayi sanadiyar da hakwaran ta guda shida na gaba suka zube nan take.
Suman wucin gadi Lawisa tayi, wanda ihu sai da ya gagare ta saboda tsabagen azaba da kuma shock,har ma ba ta san ta cika masa kwalarsa da taci ba,ta durƙusa a wajen hannun ta kan bakin ta tana jujjuya kai.
"Nayi danasanin sanin ki a rayuwa ta Lawisa, wacce babu wani abinda na tsinta a taraiya ta da ke sai zallar tarin baƙin ciki,da kuma wargaza min zaman lafiya da nake da iyalinsa,ki tashi ki fice min daga gida na sake ki saki ɗaya,biyu, uku......"
Wani irin ihu Lawisa ta fasa cike da tsananin shiga rudu da tashin hankali,har ma ta manta da zubar jinin da bakin ta yake tana faɗin, "Wallahi Lawal ba ka isa ka sake ni ba kayi kaɗan, aure na ni da kai mutu ka raba, sai dai wannan shegiyar dangin ibilisan ta tattara ta barmin gidan miji na, saboda ban shigo gidan ka na aure ka don na fita ba, sai don zama a dindindin,yau ɗinnan kuma yanzu a gaban ka zan kashe wannan halittar da take min ƙoƙari na ganin ta katangeni zuwa ga mallakar ka na har abada...." Lawisa ta ƙare maganar a haukace tana yin kan Umaima da take tsaye ta harɗe hannuwanta a ƙirji tana bin Lawal da Lawisa da ido.
Da yake itama Umaima a iya wuya take,tana naiman hanyar da za ta bambance ma Lawisa tsakanin aya da tsakuwa,dik da yanda wannan warin har zuwa lokacin yana tsakanin hawar mata kai,ta zage ta kuma dage iya ƙarfinta ta kiɓa ma Lawisa naushi a baki dai-dai inda Lawal yayi mata na farko da hakan yayi sanadiyar da Lawisa ta fadi wajen tana burburwa, Umaima ba ta tsaya iya nan ba,ta haye ruwan cikin Umaima ta fara jibgar ta babu ji babu gani,tun Lawisa na ƙoƙarin kare kanta har sai da yazo ya zamana tayi laushi, Umaima sai da ta gaji da dukan nata don karan kanta kafin ta tashi tana maida numfashi,tana faɗin,"Ko yanzu ki ka kuma yimin wani dabbancin a nan wurin sai na miki linkin ba linki na dukan da na miki,wawuya kawai jaka."
Lawisa tabi bayan Umaima da kallo da bayan gama maganar tata ta fice daga ɗakin,wanda Lawal dama tin farkon fara faɗan nasu da suka yi da yaga Lawisa ake jibga yayi ficewarsa har da jan ƙofa saboda kar ta samu hanyar guduwa. A ranta kuwa banda alwashin*MUGUN NUFI*  (Littafin *NANA HALIMA* ) babu abinda take saƙawa na tunanin hanyar da za ta bi wajen ganin ta wulaƙantar da rayuwar Umaima,tare da shi Lawal ɗin kansa da taji dikkan wani son da take masa yana kwararewa, tsananin tsanarsa na samun mahalli mafi girma a zuciyarta.
Da kyar ta samu ta miƙe saboda tsamin da jikinta yayi,tana ɗingisa ƙafarta,ta samu ta fice daga ɗakin,a parlo ta tarda Umaima da Lawal zaune kan kujerarta da suke jere cikin parlo,ba ta sake musu kallo guda ba ta sa kai ta fice daga parlon. Ta sha tafiya sosai kafin ta iso gidansu,wanda ta tarda ƙofar gidan nasu cike maƙil da jama'a,gabanta ne ya yanke ya faɗi a lokacin da ta idasa shigewa cikin gidan saboda ganin mata da tayi sunyi jugum a zaune,jimami ƙarara ya baiyana akan fuskokinsu. Bilkisu ƙanwarta ta gani da Allah ya rufa mata asiri ba ta kwaso ko ɗaya daga cikin muggan halin mahaifiyar tasu ba,tana ta faman kuka kaman za ta shiɗe,wata mata da ta kasance uwar ɗakin Bilkisu tana faman lallashinta.
"Ga ma nan Lawisar ta dawo."  Da sauri Lawisa ta kallo uwar gidan mahaifin nasu da ta tayi maganar gaban ta yana faɗuwa.
"Rayuwa fa kenan,ace wai kina matar aure kuma cikakkiyar musulma da akwai igiyoyin aure ɗai-ɗai har guda uku akan ki, bayan kuma ni'imar da Allah yayi miki na arzikin haihuwa ƴaƴa guda biyu da ba ko wacce mace bace Allah yake baima ni'imar haihuwa,da ranki da kuma lafiyar ki amman ace wai ki rasa wani irin rayuwa za ki zaɓar ma kanki sai bin malaman tsubbu da suma suka kasance bayi ne na Allah kamar ko wani ɗan Adam ki ke haɗa matsayin Allah Ubangijin subhanahu wata'ala da wayannan bayin Allah da suka kafirce masa? Hakan kuma bai ishe ki ba sai kin haɗa da shiga cikin rayuwar auren ɗiyar ki ,kin lalata sa kaman yanda ki ka lalata naki don kawai biyan buƙata ta duniya da babu wani mahalukin da zai tabbata a cikin ta? Mata wai me muke nema ne cikin wannan duniyar saboda Allah da Annabi? Yanzu waye gari ya wayarma? Me za taje tace ma Allah akan irin wannan ƙarshe da tayi dik da ma dai ni, ke ko kuma kai bamu isa mu shiga tsakanin Ƴar Madina da Ubangijinta ba?" Wata mata ta faɗa cike da jimami da yasa Lawisa ƙarasowa inda take a hargitse tace, "Maman Musa wai ban fahimci abinda yake faruwa ba,ina mahaifiya ta? Mai kuma ya samu Bilkisu take irin wannan kukan? Sannan kuma menene musabbabin da yasa naga ƙofar gidan mu ya cika da maza, sannan kuma cikin gidan ya cika da mata?"
Cike da tausaya mata Mamar Musa da ta kasance makwafciyar su ta dafa kanta. "Kin riga da kin san cewa kullu nafsin za'ikatul maut,wato dikkan mai rai sai ya ɗanɗana mutuwa ko? To ina son ki karɓi ƙaddarar ki a dik yanda tazo miki idan kina son kasancewa cikin musulman kwarai,a yau bayan fitar ki Allah yayi ma mahaifiyar ki rasuwa sakamakon buge ta da mota yayi, wanda kuma babu abinda tafi buƙata a halin yanzu daga wajen ki sama da addu'a, Allah ya jiƙanta ya gafarta mata." Sauran jama'ar da suke nan wajen suka amsa da, "Amin thumma Amin." Daga wannan maganar Lawisa ba ta sake sanin inda kanta yake ba.......

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 15, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LOKACI NEWhere stories live. Discover now