Page 9

108 4 0
                                    

*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_

©️ *OUM MUMTAZ.*

_No: 9_
_Free Page_

Umaima ta fara attending na lectures na level 4 ɓangaren computer science, wanda daman shi take karanta, sai ya zamana karatun na bata wahala sakamakon zaman shekara biyu a gida da tayi, ba tare da tayi zaman aji ba, amman kuma Alhamdulillah da yake ta nace ma karatun, kuma tana maida hankali sosai ta fara fuskanta, ga kuma project din da suka fara gadan-gadan wanda hakan yake sake sakata cikin busy sosai.
Akwai wata da take kamar ƙawa a wajen Umaima a layinsu, wanda ba tayi aure ba, sannan kuma ba ta makaranta, sabida iyayen ta masu ƙaramin ƙarfi ne a wurin ta Umaima take barin Amir idan za ta tafi makaranta, bayan ta dama masa kununsa da dik wani abinda zai buƙata kafin ta dawo daga makarantar. Sannan kuma Hassana da ta kasance kanwa a wajen Asiya(wacce take kula da Amir), Umaima ta ƙira ta a lokacin da take yankan huluna da hijabai kafin ta fara fita makaranta taga yanda akeyi, da yake daman ta iya dinki tinda sana'ar mahaifiyarsu ne, wanda hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci ta koya, sai ya zamana sun ajiye yarjejeniya da Umaima akan za tana dinka Hijaban, ita kuma idan ta sayar a makaranta ribar da suka samu sai a raba shi gida uku, Umaima ta dauki biyu ita kuma Hassana ta ɗauki ɗaya, za kuma ta tafi da keken dinkin gidansu idan ba ta da ɗinkin hijabai za ta iya karɓar ɗinkin kaya tinda ta iya take samun wasu kuɗaɗen ta, da gudu kuwa Hassana ta amince, sai godiya mamarsu take ma Umaima tana mata addu'a sabida daman rashin kuɗin sayan keken ne yasa bata bari yaranta sun maida hankali a koyar ɗinkin ba, sai kuma gashi Allah ya kawo musu sabo fil har cikin gida ta hanyar da basu taɓa tsammani ba.
Sosai kuwa ɗalibai ke rububin hijaban da huluna, wanda hakan kuwa sosai yake ma Umaima dadi, a ranta tana gode ma Allah bisa ga ni'imar da ya saukar mata a harkar kasuwancinta.
Sau ɗaya ta sake komawa gidansu, inda daga nan kuwa ba ta sake marmarin komawa ba, sabida zagi na ɗibar albarka da Aunty Halima tayi mata akan ta zauna kusa da ita lokacin da zasu ci abinci washe garin arba'in na rasuwar Baba, wai da uban dauda na tsiya, cin amana da talauci za ta rabi jikanta, wanda hakan ya mugun bakanta mata rai hadi da fusata ta, da hakan yayi sanadiyyar da ta fara maida mata martani, wanda wannan martanin da ta maida mata yasa Ammah da tinda Aunty Halima take faɗi ma Umaima maganganu ba tayi magana ba sai a lokacin ta rufe Umaima da faɗa har da guzirin mari sabida taƙi yin shiru, Ummah, Aunty Asma'u, Yaya Atika da Aunty Hamida suna sake zugata haɗi da aibata Umaima, wanda hakan ya matikar sanyaya ma Umaima jiki, har ma ta diga ma kanta alamun tambaya anya kuwa Ammah ce ta tsuguna ta haife ta? Da wannan dunƙulalliyar damuwar ta sungumi Amir da yake ta faman yanka ihu kaman yasan abinda yake faruwa suka fice daga gidan, wanda ba don Allah ya takaita ba ƙiris ya rage mota ba ta bige Umaima ba a bakin kwalta sabida nisar da tayi cikin tunanin ta ba ta san cewa har ta shiga tsakiyar hanya ba, tin daga ranar kuwa ba ta sake zuwa gidansu ba, sai dai dik ranar juma'a tana kiran Ammah su gaisa sabida sanin da tayi cewa UWA UWACE.
A ɓangaren yanayin zamantakewar ta da Lawal kuwa babu abinda za ta iya cewa sai Alhamdulillah, sau daya ta taba sanya Lawisa a idonta, ranar da shi Lawal ɗin da kansa ya kawo Lawisar domin ta gaisar da ita, wanda Umaima taji hankalinta ya sake kwanciya, domin kuwa kyawun fuska da na sura, har ma da ilmin Boko da Addini babu wani abinda Lawisa ta kamo kafarta, sai hali wanda kuma kai tsaye ba zata iya cewa ga halin Lawisa ba tinda ba taɓa zama na cikakken awa guda tayi da ita ba.
Wanda a zahirin gaskiya kuwa Lawisa sosai tafi Umaima wayo, da kuma kissa ta yanda zata karkato da hankalin mutum zuwa wajen ta idan dai za'a so ta, wanda Umaima kuma ba za ta taɓa yin wai badda kama da sunan wani ya yabe ta ko a kulata ba, sabida takance ita mutum idan yaga zai iya ya so ta a yanda take, idan kuma ma mutum bazai iya ba fine, bata da damuwa tinda ita tasan da zuciya ɗaya take zaune da kowa ma, har ita kanta Lawisar.

_Bayan shekara biyu_

*Umaima*

Da farin ciki mara adadi akan fuskarta take kallon mai ɗaukan hoto hannun ta rike da kwalin shedar kammala bautar kasar ta, tana sanye da uniform na Nysc, sai da aka mata hoto kala uku masu kyau, sannan Lawal da Amir ɗinta wanda yayi wayo da yake cikin shekarar sa ta uku suka shigo akayi musu tare, sai kuma Lawal ya fita a kayi ma Umaima da Amir, sannan Amina ta karbi Amir ɗin aka yi ma Umaima da Lawal su biyu suna manne da juna, sai kuma itama Amina ta shigo aka musu dikkan su huɗu.
Daga nan kuma Lawal ya kira mai taxi ya kwashe su, zuwa gida. Sai da Umaima ta ɗan ɗauke kwallar farin ciki na ganin wannan ranar da ta jima tana mafarki a lokacin da take zaune kan kujerar parlon ta, Amina ma tana zaune kusa da ita, Amir kuma daman yana can kofar gida wajen Babansa ya makale masa da zai fita.
"Amina ina tsananin farin ciki na ganin wannan ranar a gareni, amman kuma a ɓangare guda damuwa da baƙin ciki ne suka min kawanya a dalilin halin ko in kula da nake fuskanta daga mahaifiya ta da yan uwana, wanda da farko gani nake akan talauci na yasa suke min abinda suka san zai baƙanta min rai, sai kuma gashi har a yanzun da nake da sana'a ta ban tsira daga gare su ba,kuma ina kyautata musu daidai gwargwado, wanda ni kuma na tabbata akwai wani abu bayan talauci na da yasa suke min dik wani abinda zai sosa min zuciya,dan Allah idan kinsan mai nene ki fada min na tashi tin wuri na gyara sabida ina bukatar kulawar mahaifiyata a gareni ko da ace kowa da yake cikin duniyar nan zai juyamin baya Amina..." Umaima ta karasa maganar wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo mata, da yasa Amina dafa kafaɗun Umaima cikin sigar lallashi da son kwantar mata da hankali tace, "Aunty na hakurin nan dai da na saba faɗa maki a yau ma ita nake son jaddada miki, rayuwar duniyar nan da kike gani ɗan hakuri ne, babu wanda a kaf cikin rayuwarsa zaki ji yace komai yana zuwar masa a yanda yake so kuma ya tsara ma rayuwarsa, dan haka nake mai baki hakuri, ki yi hakuri akan dikkan nin wasu abubuwa da suke samun ki a rayuwa, ki dauka cewa wayannan sune salon naki ƙaddarar da ubangiji yake jarabtar dikkan nin wani ɗan Adam da ke cikin duniya. Ammah mahaifiyarki ce, su Aunty Halima kuwa yayunki ne babu ta yanda za'a yi ni ko kuma ke mu chanja hakan, don haka a matsayi na, na ƙanwarki ina mai shawartarki da ki miƙa dikkan lamuranki ga Allah, ki kuma ci gaba da addu'a insha Allahu wata rana sai labari."
Da murmushin samun natsuwa Umaima take kallon ƙanwarta, tace,"Nagode Allah da ya azurta ni da ƙanwa mai hankali da hangen nesa kalarki Aminau, Ubangiji Allah ya nuna mini ranar aurenki da raina da lafiya ta, kuma insha Allah zanyi amfani da shawarar da kika bani, sann...... "
Umaima ba ta ƙarasa maganar da take da niyyar yi ba ta jiyo hayaniya daga tsakar gidan, muryar Lawal cike da fusata yana cewa,"Wallahi Allah ba ka isa ba Yusuf, banda ma ka raina min wayo kuma idanunka babu kunya har kai ka isa ka tsaya a gaba na kace min wai a dole sai na baka kuɗi na aro, ba za ma ka tsaya kana bina a sannu da lallashi ba sabida kai kana jin kai uba na ne?"
"Idan ni din ba ubanka bane mainene? Ko ka manta cewa nine babba a gidannan, kuma babban wa matsayin uba yake a wajen kannensa idan da mutunci? Na faɗa dole sai ka aramin kuɗin nan akwai abinda zan yi da shi, idan kuma kace min ba zaka bani ba to wallahi sai dai a yau ɗinnan ka tattara ya naka-ya naka ka bar gidannan tinda baka da ko taku ɗaya a cikin gidan dan ubanka!" Ta jiyo muryar Yaya Yusuf shima cike da fitina, wanda dama can shine masifaffe kuma ummul'aba isin na dik wani husumar da yake tashi a gidan sai kace mace.
"Ba dai ubana ba, kuma babu gidan uban da zan tattara na tafi tinda kai ma nan din ba wai gidanka bane kai ɗaya, ko da ace bani da ko taku ɗaya a gidan amman ai akwai na sauran yan uwana." Lawal ya baima Yusuf amsa shima a salon nashi fushin da yasa Umaima fitowa a gaggauce, ai kuwa fitowarta yayi dai-dai da lokacin da Yusuf ya kwashe Lawal da wani irin mari, kafin ta dawo daga mamakin marin kuwa Lawal ya kaima bakin Yusuf wani irin naushi da nan take jini ya soma zuba, wanda hakan ya hargitsa ma sauran matan da suke gidan lissafi, gashi babu namiji ko guda ɗaya da zai shiga tsakani. Da gudu Umaima ta karaso ta hankade Lawal sabida ganin wani icen da Yaya Yusuf ya wawuro zai kwaɗa masa cike da tashin hankali.
"Da kin bar sa ya kwaɗa min wannan icen, da wallahi yau sai dai a dauki gawarka a nan wajen babban banza da wofi wanda bai san darajar kansa da y'an uwansa ba." Lawal yayi maganar numfashimsa na fita sama-sama, sabida tsananin bacin rai, Umaima kuma ganin yanayin da yake ciki kaman zai faɗi, tare da taimakon Amina suka janye sa zuwa ɓangarensu, sabida ganin Yaya Yusuf yana kokarin kwaɗa masa icen da bai samu dama ba a farko dik da yanda matarsa take bakin kokarinta wajen hanasa.
Ruwa mai rangwamen sanyi Umaima ta bai ma Lawal da suka zaunar dashi kan kujera yana ta sauƙe numfashi a wahale, kadan yasha ya ɗauke kai, ya jingina da jikin kujera ya lumshe idonsa, ganin hakan da Umaima tayi yasa tayi ma Amina inkiya da hannu suka fito dan ƙaramin tsakar gidan suka Shimfida tabarma suka zauna.
Cike da damuwa Amina tace, "Amman dai ga dikkan alamu wannan Yayan nasa shine bashi da gaskiya, ki duba kiga wani fusgar da yake sai kace wanda yake fada da sa'ansa fisabilillahi ko kunya baya ji?"
"Ai kaɗan ma kika gani daga cikin halin wannan mutumin, ni dai fatana Allah ya kawo mana dalilin da zamu bar wannan gidan, sabida bazan iya jurar wannan tashin hankalin nasu ba, abin ya fara yin yawa tinda har ta kai su ga yunƙurin illata junansu, kar kuma yazo ya zamana ni ko Amir abin ya shafe mu." Umaima ta ce a sanyaye tana jin babu daɗi cikin zuciyarta na ganin wannan rigima dikda bata san musabbabi ba.
"Insha Allah za ku tashi a gidannan da yardar Allah Aunty Umaima, kawai ki kwantar da hankalinki, sannan wallahi idan yayi yunkurin yi maki wani abin ko da wasa tinda ba shiga sabgarsa kike ba, babu abinda zai hana nasa Alhaji Abba(wanda zai aure ta) ya kulle min shi a cell sai ya bambance tsakanin aya da tsakuwa tinda naga alamar notin kansa a tsince yake, hankali bai wadace sa ba." Amina ta faɗa a sanda take gyara zaman gyalenta a kafada fuskarta ɗaure.
Shiru Umaima tayi ba tare da tace komai ba, sabida ba ta san mai za tace ba. "Ni na wuce gida sai munyi waya." Inji Amina dake ficewa.
"Ki gaida mutanen gidan."Umaima tace a hankali, tana dafe kanta, jin yanda wani irin matsanancin ciwo ke sauko mata.
Parlon ta koma bayan fitar Amina, ta samu Lawal yana nan a yanda ta barsa, amman zuwa yanzu numfashin sa normal, sannan fuskarsa na bayyana tsantsar damuwar da yake ciki, a gefen sa ta zauna tana kallon sa cikin danne ciwon kan da ya uzzira mata tace, "Abban Amir nasha baka shawara ba sau ɗaya ba kan kana kiyaye dik wani abinda kasan zai haɗo ka da Yaya Yusuf sabida ka riga da kasan halinsa amman baka ji, yanzu ka duba ka gani fisabilillahi da ace ya sauƙe maka wannan itacen mai kake tunanin zai iya samun ka!? Dan Allah ka rufa mana asiri kake baya-baya da sha'anin fitinarsa ko don ka tsira da lafiyarka." Umaima tayi maganar a sanyaye tana riko hannuwan Lawal dikka biyu.
Kallon ta Lawal yayi ya sauke wani ajiyar zuciya cike da damuwa a muryarsa yace,"Kinsan tin da muka yi haka da ke ban sake shiga sabgar wannan mutumin ba, wai fa kawai daga Yaya Masa'uda ba bani kudi na, na gidannan wanda nace a ciremin gado na sabida ina son akwai wani gidan da zan siya miki ki koma shikkenan tin shekaranjiya mutuminnan ya dinga matsamin lamba wai sai na basa aro, nace masa nima uzirin gaggawa ne dani amman ya dage har yana iƙirarin dole sai na basa kaman irin wanda ya bani ajiya, ni kuwa na riga da na rantse tinda ba tsoronsa nake ji ba wallahi ko naira biyar bazan basa ba." Lawal ya ƙarasa maganar cike da ƙunan rai na takaicin halin Yayansu da yake nuna ma duniya indai akan kuɗi ne bashi da alamun mutunci ko dai-dai da ƙwayar zarra.
Umaima ma shiru tayi ba tace komai ba sabida mamakin Yusuf, wato dik wannan tada jijiyoyin wuyar da yake yi akan kuɗin da ba nasa bane, lallai kuwa idan yace a haka salon nasa rayuwar zai tafi ba fata take masa ba yana da tare da wahala. Amir ne ya shigo da gudunsa yana ihun kiran Ammi(Umaima), wanda hakan yasa Umaima miƙewa a hanzarce ta fito tsakar gidan nasu Lawal ya rufa mata baya, sabida daga jin kukan ba na lafiya bane.
Dago sa Umaima tayi cike da damuwa, wanda kafin ma tayi magana taga yanda yatsu ke kwance akan kumatunsa alamun wani marar imanin aka samu ya maresa, wanda hakan yasa ta maida akalar tambayar ta kan waye ya dake sa.
"Ba Shani(Sani) bane maye ni ban masa komai ba, wai don na taɓa masa kekensa." Yayi maganar cikin kuka sosai, take fuskar Umaima ta rikide zuwa bacin ran da ta jima ba tayi ba, tace, "Dan kawai ka taɓa masa Keke shine zai maka irin wannan mari na sa'a sabida zalinci? To wallahi yau kam bazan yarda ba tinda ba jaki na haifar musu ba, dan bazai yu ace shine babba amman a kullum burinsa bai wuce yaga yaci zalinka ba idan yaganka a tsakar gidan tunda bakai kaɗai bane yaro a gidan." Tayi maganar cike da ɓacin rai, wanda kafin ma ta ankara Lawal da ya gama sauraron abinda Amir ya faɗa ya fice daga kewayen kamar kububuwa ta rufa masa baya ba tare da ta dakatar da shi ba, sabida yanda yau Sani(Babban yaron Yaya Yusuf, shekarar sa goma sha uku) ya mugun kai ta bango akan cin zalin Amir da yake, wanda da farko tin tana daukan abin wasa amman gani take kullum gaba yake ba baya ba.

*FITATTU BIYAR 2023 paid books:-*

1- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*
2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*
3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*
4- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*
5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*

_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_
_LITTAFI BIYU:- ₦800_
_LITTAFI UKU:- ₦900_
_LITTAFI HUDU:- ₦1000_
_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_
_VIP 2k._

Za ku biya kuɗi ta wannan account...
*6314170140*
*FIDELITY BANK*
*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*

sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(09061794195)*

katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(07083818353)*

*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(08162576936).*

_LITTAFI ƊAYA:- 350f_
_LITTAFI BIYU:- 600f_
_LITTAFI UKU:- 650f_
_LITTAFI HUƊU:- 750f_
_LITTAFI BIYAR:- 850f_

'''ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-'''

*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*
*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*
*_•TICTOK 1500_*
*_•INSTGRAM 1500_*
*_•FACEBOOK 1500_*
*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*

'''ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(09030398006.)'''

*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(07018098175).*

MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*

LOKACI NEWhere stories live. Discover now