*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_©️ *OUM MUMTAZ.*
_No: 4_
_Free page_Tin daga wannan lokacin sai ya zamana yan uwan nata basa shiga sabgarta sun fita daga uzirinta, wanda hakan yake damunta ƙwarai, amma Maimuna tana kwantar mata da hankali tare da nuna mata cewa za su gama fushin su sauko don kansu kawai ta basu lokaci, wanda hakan yake rage mata damuwar ganin ba dikkansu bane suka juya mata baya, Maimuna da Amina suna tare da ita.
Sannan Babban abinda yake damunta bai wuce na ganin yanda Ammah ma take mu'amalartar ta fiye da baya ba tin sanda Baba ya hada kan yaran yayi musu fada ba, wanda ta tabbata ba laifin kowa bane sai na yayun nata da take ganin a yanzu kamar ba akan talaucin ta yasa suke mata irin abubuwan nan ba, sai dai idan da wani abin a kasa da ita bata sani ba.A ɓangare guda kuwa, mijin da za ta iya cewa dik ta silar sa komai ya cakuɗe mata tsakanin ta da mahaifiyar ta da ƴan uwanta, yana naiman zame mata hawan jini da ciwon zuciya, wanda ya kamata ace shine zai janyo ta jikinsa yasa taji kwanciyar hankali da natsuwar da ba ta samu daga kowa idan aka cire Baba, Maimuna da Amina, amma kuma shima yana ɗaya daga cikin mutanen da suke sake hargitsa duniyar ta sahun farko, da taji rayuwar gaba daya ta fitar mata a kai, wanda hakan yasa take wani mugun rama da dik wanda zai kalle ta idan yayi mata farin sani a baya zai fahimci Umaima yar gayu ta baya, da wannan Umaimar da ta fara disashewa dikda karancin shekarun ta, to tabbas akoi tazara ta bambanci mai nisan gaske.
****
"Wai ke wace irin wawuya kuma mahaukaciya ce Umaima? Banda wawanta da rashin hankali ina matsayin mijinki na aure amman ace kinyi min laifi nazo ina karanta miki maimakon ki natsu ki bani hakuri shine zaki buge da yi min rashin kunya?"
Da wani irin mamaki ƙarara da ya bayyana a Kan fuskar ta Umaima take kallon mijinta Lawal, sabida jin kalar zagi na cin mutunci da kaskancin da yayi mata a yau, lalle tabbas abin nasa gaba yake yana kara gaba, wanda wata rana tana tunanin duka ma zai iya biyo baya tinda har sun zo matakin da zai fara zaginta.
"Shashasha kawai wacce ba ta san abinda ya kamata ba." Lawal ya sake fada ganin yanda Umaima take kallon sa ba tare da ta basa hakuri ba kaman yanda yake buƙata,sannan ya sa kai ya fice daga kewayen nasu yana sake sakin zantuka.Durkushewa a wajen Umaima tayi, tana jin yanda yawun bakin ta ke kafewa ba tare da ya wuce ta makogoron ta ba sabida kaduwa, yanzu ace har lalacewar ta yakai ace wanda yake matsayin miji a wajen ta, kuma uban danta Amir ya iya bude baki ya ƙira ta da, wawuya? Mahaukaciya? Kuma Shashasha? Ita kuwa mai tayi ma Lawal haka da zafi da har ta cancanci irin wannan cin mutuncin? A iya sanin ta dashi dai auren soyayya suka yi na saurayi da budurwa, wanda soyayyar da take masa ne ma yasa ta tsallake tarin samari da ma masu aure da dama, wayanda suka fisa kyau, asali, kuɗi da komai ma na rayuwar duniya tace idan bashi ba sai rijiya, wanda a dalilin hakan mu'amalar ta da mahaifiyar da sauran yan uwan ta dik sai da ya canza ba akan yanda suke a baya ba,amman ace wai ya rasa da mai zai saka mata sai tarin bakin ciki da bacin rai?
Yanzu fisabillahi ta ina ma tayi masa laifin da har akansa zai mata irin wannan zagin? Kukan da Amir taji ya fara ne yasa ta miƙewa daga durƙushen da take tana jin yanda kirjin ta ke matuƙar yi mata nauyi zuwa in da yake kwance yana wulla kafar sa sama, daukar sa tayi suka shiga parlor, tare da zama kan kujera ta basa ruwa.
Wayanta ta dauka tana jujjuyawa, tare da tunanin waye ya kamata ta kira sabida neman shawarar ta yanda zata gyara rayuwar auren ta da yake daukar wata hanya ta daban ba a yanda tayi tsammani ba, lambar Ammah ta latso, amman sai tayi hanzarin katsewa tin kamin ya shiga sabida tunowa da gargadin Ammahn a gare ta ba sau daya ba, ba sau biyu ba._"Tinda kin dage kince lallai ke ba zaki auri zabin da nayi miki ba, sai wani can banza matsiyaci da ko kwakkwarar sana'a basa da shi da zai ke biya miki bukatunki, kije ga-ki-ga-shi bazan takura miki ba, amman ina so kisan cewa, wallahi Allah ko ba yanzu ba, idan kika kuskura ki ka sake, ki ka kawo min wani matsala da ya shafe ki tsakanin ki da shi wanda ki ka zabi kasancewa tare da shi sama da farin ciki na sai na baki mamaki KHADIJA. _
YOU ARE READING
LOKACI NE
RomanceTa zaɓe sa sama da farin cikin mahaifiyarta a dalilin shine zaɓin zuciyarta kuma farin cikin zuciyarta! Dawowarta daga gidansu da tayi tsawon kwanaki takwas a dalilin rasuwar mahaifinta kwatsam sai ta tarda mijinta ya ɗankaro mata kishiya ba tare da...