Page 3

41 2 0
                                    

*LOKACI NE...!*
     _(Umaima)_

©️ *OUM MUMTAZ.*

   _No: 3_
_Free Page_

Allah yasa sanda ta iso babu kowa a tsakar gidan ballantana wata daga cikinsu ta fahimci yanayi na damuwa da ɓacin ran da ta shigo da shi, ga Amir da yake ta faman kuka tin sanda suka fito daga gidan Aunty Halima.
A kan kujera ta zauna ta sama Ameer nono a baki da yasa kukan nasa tsayawa, wanda ita kuma tayi amfani da wannan damar wajen sanya ɗayan hannunta tana goge hawayen da yake mata sintiri a fuska, zuciyar ta kuwa banda tafarfasa babu abinda yake mata. Wayar ta dake cikin jikanta ne ya ɗauki ringing, wanda hakan yasa ta janyo jikar ta buɗe tare da ciro wayan da har ƙiran ya yanke, zata bi bayan ƙiran kenan ganin Ammahn su ke ƙiran ta wani ƙiran ya sake shigowa, da yasa gaban ta faɗuwa sabida jikinta ya bata wannan kiran ba na lafiya bane tinda Ammah bata taba yi mata ƙira biyu a jere sai da ƙwaƙƙwaran dalili.
A kunnenta ta ɗaura wayar, kamin ma ta bude baki tayi sallama Ammah ta tari numfashin ta da faɗin,  "Wato dai Umaima wuyanki ya isa yanka har haka ko? Tsabagen rashin kunya da rashin hankali har kinsan ki ɗauki ƙafa ki wanke ki tafi gidan yayarki kije ki mata rashin kunya da fitsara sabida kema kina jin kin Kai kin isa daga ta fada miki gaskiya? To wallahi ki kiyaye ni idan ba so kike na mugun bata miki rai ba tinda kinsan Halima ba sa'arki bace, banda ma rashin hankalin ki da haukarki ai ko wani kika ji labarin yayi mata rashin kunya ke mai tsaya mata ce har sai inda karin ki ya kare matsayin ta uwa a wajenku baki daya, amma shine kece da kanki zaki je ki mata rashin kunya? To ki shiga hankalin ki dani shashasha kawai wacce bata san inda yake mata ciwo ba!" Daga haka Amma ta katse wayar ba tare da ta tsaya tabi ba'asin maganar ba.
Bin wayar Umaima tayi da kallo, tana jin hawayen dake zuba a idon ta tin dazu ya kafe kaf, sai suyar da zuciyanta yake mata sabida tsananin damuwa da ɓacin rai, wai ace a dake ka a wannan duniyar ba komai bane dik don kawai an ga cewa baka da arzikin duniya kuma a hana ka kuka? Wanda suma masu arzikin ba wai su suka bama kansu ba Allah ne ya basu, ba kuma don yafi ƙaunar su ba akan kai da baka dashi?
Ita yanzu abinda yafi ɗaga mata hankali ma shine wai ace yanzu uwar da ta tsuguna ta haife ka ma idan baka da kuɗi sai ta nuna maka bambanci ƙarara tsakanin ka da sauran ƴan uwanka da suke da abin hannun su?
Tana nan zaune tana tufka da warwara bata san yanda lokaci ya tafi ba, sai da taji hayaniyar yaran gidan nasu da hakan ya tabbatar mata da sun dawo daga makaranta. Hakan yasa ta aro jarumtar dole na babu yanda ta iya ta miƙe haɗi da kaima yaran Amir su riƙe mata shi, ita kuma ta dawo ta hura wuta.
Taliya jaloup ta dafa musu da guntun kayan miyan da ta rage jiya, wanda hakan yasa ta kammala cikin ƙanƙanin lokaci, kayan jikinta ta cire tare da saka mara nauyi bayan ta gama tattara inda tayi girkin, Khairat da ta rike mata Amir ta miƙo shi bayan ya fara rigima.
Wayar ta ya ɗauki ringing, ganin Maimuna tke kiran ta yasa ta ɗauka bakin ta ɗauke da sallama.
"Amman banji dadi da kika fito kika barni gidan Aunty Halima ba dik kiran sunan ki da nake yi Umaima, ai ko babu komai Aunty matsayin Uwa take a wajen mu bai kamata ace kina ɗaukan dik wani abinda suke maki da mahimmanci ba tinda kin riga da kinsan halin yan gidan namu babu baƙo a ciki, wanda na tabbata abubuwa dayawa da gangan suke yi don su dinga hadaki dasu Ammah, wanda na tabbata idan su Ammah suka ji labari babu makawa sai sun ƙira ki sun yi miki faɗa akan abinda basu da tabbaci akai tinda kinsan dole wajen kai ƙarar taki baza su fadi abinda ya faru daga farko har ƙarshe tsakani da Allah ba." Maimuna ta ƙare maganar a sanyaye cike da tausayin yar uwarta.
Rintse ido Umaima da take sauraran abinda Maimuna take faɗa mata tayi, cikin sanyin murya sabida yanda duniyar ta sake fice mata akai tace, "Na fahimceki sosai kuma na gode da shawara, insha Allah zanyi amfani da shawarar da kika bani sai munyi waya." Daga haka Umaima ta katse wayar ba tare da ta jira abinda Maimuna zata sake faɗa ba.
Lawal ne ya shigo da sallama, wanda dawowar sa daga kasuwa cin abinci kaman yanda ya saba, Umaima dake kwance kaman mai bacci, nan kuwa idon ta biyu ne ta tashi ta zauna haɗi da masa sannu da zuwa.
"Yawwa sannu, miko min ruwa yau nasha rana sosai dikka jikina ciwo yake min."
"Ayya Sannu, Allah ya yaye."
Ta fada a sanda ta kawo masa ruwan randar ta dake da sanyi.
Sai da ya sha ruwan sannan ta zubo masa abincin,wanda komai take yi cikin ƙarfin halin danne damuwar ta gudun kar ya fahimta ballantana ya takura mata sai ta fada masa abinda yake damun ta, wanda ita kuwa ba zata taba kaunar mijin ta yasan halin da take ciki da dangin ta ba akan auren sa da tayi sabida gudun matsala.

LOKACI NEWhere stories live. Discover now