*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_©️ *OUM MUMTAZ.*
_No: 10_
_Free Page_"To kai Lawal yanzu sabida da Allah ina kai ina dukan Sani? Sanin nawa yake baki ɗayansa da har zaka masa irin wannan dukan,wanda nake da tabbacin idan da yazo da karar kwana mai zaka ce ma duniya?"
Yaya Masa'uda ta fada cike da fushi sosai tana kallon Lawal da yake zaune kan kujera ta three seater shi da Umaima, ita kuma tana zaune kan one seater.
"Amman Yaya ke baki ji kalar cin zalin da shi Sani yake ma Amir bane na tsawon lokaci? Sai ni yau kawai ɗaya da na nuna fushina na dauki mataki zaki ɗauki ƙarya da gaskiya ki hau kai ki zauna sabida Allah?" Lawal ya faɗa shima cike da fushi.
"Ai nasan tin da baka dauki matakin ba sai yau sabida taku ta hado ka da ubansa, sannan kuma Ƴar goal din naka ta nuna maka cewa bata yarda ba sabida ita isashshiya, ana ƙoƙarin kashe wuta idan ta kama, amman ita ƙoƙarin ta shine ta saka masa makamashi yaci gaba da tashi sabida ita makira ce da bata ƙaunar zaman lafiya tsakaninka da y'an uwanka." Tayi maganar tana watsa ma Umaima harara sabida dama can ba wai shiri suke ba.
"Ni kuma miye nawa a nan Yaya? Kowa da yake cikin gidannan ya kwana da sanin halin Sani na cin zalin na kasa dashi, wanda kuma abin nasa yafi yin ƙamari akan Amir tin bai kai haka ba, nasha yima Ummansa magana kan ta tsawatar masa, amman kuma kullum abin ƙara gaba yake ba baya ba, yanzu idan da ace shi ake ma abinda yake ma yaranmu nasan cewa wallahi an ringa tashin hankali da Babansa sabida bazai taɓa yarda ba, amman shine don yau ya kaini bango nayi magana shine zaki ce wai nice mai kunna wuta? Haba Yaya! Kema fa uwa ce, ki duba wannan lamarin mana." Umaima tayi maganar ba tare da ɗaga murya ba, dik da a saurarar farko idan kayi ma muryarta zaka fahimci tsantsar fushin da yake tattare da ita.
"I, lallai ta tabbata abinda ake faɗa ba kunya bane ya ishe ki Jummala ko wa kike da suna? Wato sabida tsabagen wuyanki ya isa yanka shine ina faɗa kina mai da min sabida baki ɗauke ni da daraja ba?" Inji Yaya Masa'uda cike da mamakin maida mata da magana da Umaima tayi, sabida tsawon zamansu tinda suke hakan bai taɓa faruwa ba, dik abinda za su mata sai dai ta kauda kai albarkacin tana auren na ƙasa da su, wanda hakan ya tabbatar mata da cewa lallai an kaita bango ne, amman da yake girman kai na ɗawainiya da ita ba za ta taɓa karɓar gaskiyar a yanda tazo ba sabida wai kar Umaima ta samu ƙofar raina ta, wanda hakan yasa ta kalli Lawal da ya dafe kansa da hannu bibiyu yana saurarsu ba tare da ya tanka musu ba tace, "Kai kuma da yake shashasha ne solobiyo da har ka buɗe ma ƙadangarun bariki damar raina maka dangi kana jin rashin kunyar da matarka take ƙoƙarin yi min shine ba zaka taka mata birki ba sabida kaine tattabara sarkin soyayya ko?"
"To sabida Allah me kike son nace ma Umaima Yaya? Tinda nasan ko ke ake musguna ma ƴaƴan ki baza ki iya haƙurin da ita Umaiman tayi ba? Kuma shine don yau ɗaya tayi magana sai ku dinga ganin bakin ta sabida bakwa son gaskiya." Inji Lawal yana kallon Yayar tasu da itama muguwar masifaffiya ce, kusan halinta ɗaya da na Yaya Yusuf, wanda shi nasa ya haɗe masa har da talauci amman ita kuwa ba ƙaramar Hajiya bace, domin kuwa mijinta mai kuɗi ne sosai, gashi kuma ita kanta babbar dillaliya ce da take dillancin ƴan mata da samari zuwa ƙasashen ƙetare domin yin aikatau, wanda kuma idan dai ta sama ma mutum hanyar da zai tafi ƙasar waje akwai percentage ɗin da take samu mai tsoka, wanda a cikin irin haka ne ma da Lawal ya sako zancen a cire masa kasonsa a gidan ta basa million ɗaya da dubu ɗari biyar bayan anyi lissafi,kasancewar anyi ma gidan nasu kudi.
"I,lallai wuyanka ya isa yanka Lawal, wato ka goyi bayan matarka sama da ni yayarka da muke uwa ɗaya uba ɗaya? To wallahi tallahi tinda naga ba farillan mutunci bane da kai yau ɗinnan ka kwashe kayanka da wannan yakunanniyar matar taka ku bar mana gida, idan kuma kace ba haka ba kuwa sai dai a yanzunnan ka maido min da kuɗi na."
"To shine me? Ga nan kudin naki sai inga ta tsiya tinda dai kinsan ba wai yanke talauci kika bani b....."
Bai karasa faɗar abinda zai ce Umaima tayi wani tsalle da diro gabansa dik da irin ciwon da kanta yake mata ta toshe masa baki tana kallon Yaya Masa'uda tace,"Wallahi tallahi mun yarda a yau dinnan za mu bar muku gidan nan." Tayi maganar a wahale, sannan ta kalli Lawal da yake binta da ido babu damar magana cikin sigar rarrashi da roko tace, "Indai don ta nice kar ka damu Abban Amir,zanyi parking na kayana a yanzun nan, kaje ka nemo mana mota mu koma can gidan ni ko 1 bedroom ka bani, yaso Lawisa ta dauki biyu ta hada da parlo bani da matsala indai hakan zai sa na bar wannan gidan sabida wallahi bazan iya ci gaba da zama a gidannan ba, hakuri na ya kusa ƙarewa, kar muzo muyi abinda za muyi dana sani daga baya dan Allah!" Ta ƙare maganar tana mai fashewa da kuka sosai, wanda hakan yasa Lawal rungume ta a jikinsa dik da yanda yake jin wani irin tsanar ta na taso masa daga can kasan zuciyarsa da bai san musabbabin tsanar ba."Ki shiga ki hada mana komai ki killace sa Umaima, karki ɓata lokaci yanzu zanje na taho mana da mota a kwashe kayan." Lawal ya fada yana bubbuga bayan ta da yasa Yaya Masa'uda buga wani uban salati irin tayi mugun ganin nan na ganin Lawal rungume da Umaima matarsa a gabanta,wanda hakan ya sa ta fice ba tare da ta gama amayar abinda yake cikinta ba.
Fita Lawal yayi, wanda hakan ya bama Umaima damar shiga ɗaki tana faman zubar da hawaye ta sauƙo da akwatinan ta na aure ta kwashe musu kayan sawansu tas da kayan shafe-shafen ta, ta fiddo su ƙaramin tsakar gidansu, sannan ta ɗauko wasu manya-manyan buhuhuna da suke shimfide ƙarƙashin gadonta tin aurenta wanda a ciki aka zubo mata kayan kitchen ɗinta ta kwashe dik wani abinda yake kitchen din kasancewar dama ba wasu masu yawa bane cikin kankanin lokaci ta kammala. Cikin abinda bai wuce awa daya ba ta hada komai da komai, wanda ta zauna kusa da Amir da tin dazun yayi baccin dole bayan ya gama kukansa tana kallonsa, zuciyarta a raunane, tare da rokon Allah kan ya raya mata shi, sannan kuma yasa ya zamto shine sanyin idaniyar ta a nan duniyar zuwa bayan ranta.
Lawal ne ya shigo, wanda Umaima tasha jinin jikinta sosai ganin yanayinsa, a ranta fadi take Allah yasa ba wani mugun abin bane kuma ya faru sabida tasan may be yaje can gidansa ya samu Lawisa da maganar komawarta.
YOU ARE READING
LOKACI NE
RomanceTa zaɓe sa sama da farin cikin mahaifiyarta a dalilin shine zaɓin zuciyarta kuma farin cikin zuciyarta! Dawowarta daga gidansu da tayi tsawon kwanaki takwas a dalilin rasuwar mahaifinta kwatsam sai ta tarda mijinta ya ɗankaro mata kishiya ba tare da...