Prologue

74 2 0
                                    

*5STAR EXPENSIVE COMPANY*

_TSOKACI_

Miyagun kwayoyi

___Ƙwaya magani ce da ake anfani da ita wajan magance cututtukan dake addaban jikin mutum.

A wani cewa kuma
Ƙwaya sinadari ce wanda da zarar ya shiga jikin ɗan adam zai canja fasalin aikin jikin mutum da tsarin gudanarwarsa.

Ma'anar Tu'amali da miyagun kwayoyi na nufin sha yin allura ko zukar hayakin sigari ko shisha da tabar wee-wee da duk wani sinadarin da babu izinin likita wajan shan sa, ko kuma anfani da wani magani ba da nufin magance cuta ba.

A lokacin da mutum ya kasance ba zai iya rayuwa ba tareda ya sha wani sinadari ba to za a ce ya kamu da cutar shan ƙwaya wato a turance *Drug Addiction*

DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
01

In the name of Allah, The Most Gracious, The Most Merciful.

*Bismillahir rahmanir rahim*

______________________________________

National Drugs Law Enforcement Agency(NDLEA)
BAUCHI STATE

Wannan shekarar sanyin da ake fama da shi ya zarce kowacce shekara a faɗin garin Bauchi, hazo mai haɗe da guguwa wanda a turance ake kiran su da *Coldy, Windy, and Dusty* Sosai iska ke ɗaukar kura tana kai wa kowani lungu da sako na cikin filin offishin NDLEA....Yayinda ko wani halittar ɗan adam yake kunshe cikin offishin sa tsabar sanyin dake shiga cikin jikin mutum.

Da misalin karfe tara na safe wani babban Hall wanda yake a killace gefe guda Corpers ne da yawa sanye cikin kayan NYSC suna CDS meeting wanda ƴan bautar ƙasa suke yi duk ranar alhamis.....A kallah minti arba'in zuwa awa ɗaya kafin suka fara fitowa suna yin hanyar Gidan yarin dake cikin NDLEA.

Inda ake tsaron masu shaye shaye da wanda miyagun kwayoyi sukayi ma illa a rayuwar su....abin dai abin tausayi, wasu suna kwance suna sambatu.

Rashin miyagun kwayoyin da suke sha hakan yasa wani yake ta kwarara amai, Yayin da wani yake ta sosa muscles ɗin sa alamar kaikayi, da sauran su.

Karshen prison ɗin ihu ne da kwarmato yake fita babu kakkautawa, Hayaniyar ƴan ƙwaya tayi yawa......haɗe da karan karkaɗawar karafunar daga cikin ɗakunan gidan yarin (NDLEA) ɗin wanda a keɓance suke ta yadda babu wanda ya isa ya buɗe ko yayi tunanin guduwa.

Karar tayi yawa, haɗe da ihu da jijjiga, a hankali na tako kafata don in gano ma idanuwa na halittar da take kurma wannan kara da kwaratsi da ihu kamar dabba mai kisa.

Siraran hannayen sa su suka sanya min kwaɗaituwa da son ganin ko waye wannan mai ihun, hannayen na sanye da zobbunan azurfa masu kyau, sheki da kuma tsada, taku biyu na kara na isa bakin karfen, ..Lord fari ne kamar ɗan igbo irin farin yellow yellow, abin da yafi bani tsoro shine gashin kansa yayi Dada sosai, rabi kitso, rabi kuma twisting an kama wani gu da ribbon na kama gashin mata, sannan wasu daga cikin gashin gaban kai sun barbazo masa sun rufe masa fuska...da alama gashin kansa ne saboda laushi da tsantsi da ya nuna a idanuwan mai kallon shi.

Ji kake ana "Ku tai maka ku bani ko wacce iri ce, ko karamar ce don Allah, sai kuma ya kurma ihu cike da kwaratsi, yana bori, yana kakkarwa da soshe soshe, hannayen sa na kakkarwa, jikin sa yayi sanyi kalau kuma yana fitar da ruwa kamar mai zazzaɓi, Lokaci guda yana soshe soshen hannayen sa tsabar bai samu abin da yake muradi ba.

Yau a kalla kimanin wata guda kenan da aka kawo sa gidan tsaron masu shaye shaye,Rehabilitation Centre karkashin hukumar NDLEA, Tu'amali da miyagun ƙwayoyi yasa ya shiga tremor. Ga ciwon kai mai tsanani wanda yake sara mishi tun daga farkon goshin sa har karshen ƙeyar sa.

DRUG ADDICT ✔Where stories live. Discover now