5STAR EXPENSIVE COMPANY
DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
12*AMRAH POV*
KANO STATE
OFFISHIN HISBATaron mutanen da ke wajan su suka sanya hayaniyar wajan tayi yawa har baka jin maganar na kusa dakai....mata ne zube a kasa wasu da kananan kaya, wasu da shigar mutunci, wasu da abaya dogayen riguna, wasu da hijabs.
Masu ɗaukan rahoto ne suke magana da ƴan matan.
Takaitaccen labari game da ƴan matan...an kama su ne a hanya misalin karfe goma da wani abu, a wannan rayuwa da muke ciki ace an samu mace a waje da misalin sha ɗayan dare, ita bata koma gidan mahaifan fa ba tana yawo a waje......Kasancewar garin kano sun saka dokar kame duk wacce suka gani a wannan lokacin tana yawi bata tafi gida ba.
Ciki ƴan matan da aka kama har da Amrah...wacce take zaune gefe guda sanye cikin sea blue ɗin material na doguwar riga, ta chukurkuɗe fuskar ta ta rufe fuskar da ɗan siririn mayafin ta.
"Karamar yarinya dake, Shin me ya fito dake daga gidan iyayen ki, da karfe goman dare?? wani ɗan rahoto ke tambayar ta.
"Sunana Amrah, ina zaune da iyaye na a unguwar hotoro, Mama na ne ta aike ni na siyo maganin ciwon mara, shi ne na tsaya a joint ina yiwa wasu da na sani magana shine aka zo aka kama ni"
Ɗan rahoton ya ce,"Karamar yarinya dake, kin tsaya a joint, tsabar shaye shaye ma a bige muka ɗauko ki yanzu da safe kika wastsake, wannan wace irin rayuwa ce kika sa kanki" ya karasa maganar sa.
Amrah ta ce,"Don Allah ku kirawo Mamana zata zo don Allah kar ku kira Baba na baya nan"......Amrah ta karashe maganar sanin cewa Daddy ba zai taɓa zuwa wajan nan ba.
Yau ne gobe ne Amrah bata ga kafar wani daga cikin iyayen ta ba, gashi igayen wasu suna ta zuwa suna tafiya da ƴaƴan su amma ita shiru, ga cikin ta ya fara murɗawa alamar tana jin yunwa....Ta ɗaga waya ta kirawo Hafsat.
Hafsat na cikin offishin NDLEA, Suna tattaunawa da Nawas taji ana kiran wayar ta, Bugu ɗaya ta ɗauka ta ce,"Amrah ya ya?
Shasshekar kukan ta ne ya fara amsa kuwa a cikin kunnen Hafsat, yayin da muryar ta na rawa ta ce,"Anty Hafsat Daddy da Hajiya basu zo sun ɗauke ni ba "
Cikin rashin sanin kan maganar Hafsat tace,"Basu ɗauke ki a ina ba kuma?
"Ina office ɗin Hisba, sun kama mu jiya da daddare, Anty hafsat yunwa nake ji, kice ma Daddy yazo ya tafi da ni gida don Allah"
"Toh ai Amrah ni na koma Bauchi kwanan ki nawa ba kya gida Amrah, haka kika dawo Inna lillahi wa'inna illaihi raji'un"
Kiran da Amrah tayi wa Hafsat shi ya bata damar sanyaya zuciyar ta ko ba komai ta san ƴar uwar ta zata kira Daddyn ya sa a zo a tafi da ita gida.
Ɗaga cikin wayar Hafsat, ta tambaye ta "Me yake faruwa ne?
"Ina office ɗin Hisba, sun kama mu jiya da daddare, Anty hafsat yunwa nake ji, kice da Daddy yazo ya tafi da ni gida don Allah"
"Toh ai Amrah ni na koma Bauchi kwanan ki nawa ba kya gida Amrah, haka kika dawo Inna lillahi wa'inna illaihi raji'un"......
"Wait! wait!! wait!!!! will you please call Daddy for me, saboda maganar ki kaɗai zai ji"
"No i cannot Amrah, tun da baki san da whereabout ɗin Daddy ba sai yanzu da kike cikin matsala" Hafsat ta bata amsa sannan kuma ta kashe wayar ta"
Amrah ta jima tana kare wa wayar wani kallo ta maida hankali kamar akwai wani abu da take son hangowa cikin wayar salulan na ta jim kaɗan sai taga wayar tana walkiya kamar duk da babu kara dama a silent ta saka wayar nata.
*Hannun ka bazai ruɓe ka yar ba*
*DADDY* Ɓaro ɓaro haka sunan ya bayyana a screen ɗin wayar yayin da ita kanta tana mamakin yadda Hafsat har ta mishi magana kuma har ya kira, wannan karan kuka kawai ta fashe da shi, tana kuka mai tsuma zuciya"
"Amrah" Da da nake miki faɗa baki san zakiyi kuka ba sai yanzu Amrah?
Taji sautin muryar nashi mai magana a hankali yana tashi daga cikin speaker na wayar, kara ruɗewa tayi da taga saura su biyu ne a wajan, yamma tayi ga wani azababbiyar yunwa da take ji wanda ya ke sa cikin ta ƙugi ta manta when last ta ɗauki abinci ta ci...sai dai kawai tai ta shan tramadol tana bacci........Daddy na magana yana cewa yanzu Hajiya zata zo ta tafi da ita, ta kwantar da hankalin ta.....Wayar ya katse da kansa, Sallamar sa ita ta dawo da ita daga tunanin da ta shiga. "Salamu alaikum, Wani murya mai cike da amo da zati yayi mata magana, wanda tayi saurin juyawa tana kallon waje kasancewar tana ta ciki ne, Idanuwan ta suka kalli mai sallamar.
"Bawan Allah lafiya?Amrah ta tambaya?
"Lafiya, dama abinci na kawo miki, naga har yanzu ba a zo ɗaukan ki ba, Ko baki da iyaye ne?
Amrah ta zumɓure baki tana kunkuni, duk da ita yarinya ce mai shaye shaye amma Amrah bata da rai ni, ko faɗa bata yi da kawayen ta balle abokan harkar ta, ita ba ruwan ta da raina na gaba da ita, amma fa idan tasha yayi mata yawa tana faɗace faɗace......Har zata ce bata jin yunwa sai cikin ta ya fara kugi saboda yaga abinci Ta sanya hannu ta karɓa tana masa godiya.
Kamar Almajira haka ta soma buɗe takeaway ɗin fried rice ce har da nama, ta hau ci tana korawa da pure water, har ta gama tana daga kai tana kallon wanda ya kawo mata abincin....sai data gama tace,"Alhamdulillah" tayi gyaza ta na lashe baki alamar dai ta kashe yunwa amma bai ishe ta ba.
"Miye sunan ka? Amrah sai a lokacin take tambaya, daka ji muryar nata kasan shaye shaye take yi ba kakkautawa har ya soma bayyana a fuskar ta.
"Don Allah kiji tsoron Allah, ki koma gaban iyayen ki, ki natsu ki maida hankali, kar kibi ruɗin duniya, domin kuwa wahala zaki sha, Ki dena shan abin da zai lalata miki kwakwalwa, ki rage shan duk wani tarkacen kayan maye don gyara goben ki, saboda ke mace ce kuma wata rana zaki aure har ki haifi yara, kuma bazaki so yaran a nuna musu abin da kika aikata ba, bakuma zaki so suma yaran su aikata kwatan kwacin irin rayuwar da kikayi ba"
Sunana *Bin Umar*
Yana kaiwa nan ya juya ya bar wajan, tunawa da mahaifiyar sa wanda har kwalla ta sauko idanuwan sa ya goge ya koma cen wajan Hamzah suka tafi gidan Kawun suna zama ne a ɗakin waje kunsan yadda gidajen kano suke.
Yau kam ba sauki Umar ya faɗa soyayyar Amrah, tun da suke karatun dare bai karasa ba, saboda zuciyar shi tayi laushi tunanin halin da Amrah take ciki kawai yake yi.
AMRAH
Umar na barin wajan tabi shi da kyawawan idanuwan ta, tana jin maganganun da yayi mata har cikin jinin jikin ta....dama akwai masu tsoron Allah haka, tana ta faman leke ta ma manta a wajan da take sai da taji ana kiran sunan ta sannan ta waiga da sauri Hajiya ce tazo ɗaukar ta.
Da gudu ta rungume ta tana kuka,"Hajiya ina kika ajiye wayar ki tun jiya nake faman kiran ki amma shiru.....har na kwana anan, na yini"
Hajiya tsabar ranta ya ɓace da Amrah ta wanka mata mari, yau rana ɗaya kenan da Hajiya ta ɗaga hannu ta wanka ma Amrah mari ko me ya janyo hakan?
Ashe tana wajan bikin yarinyar kawarta, ita da manya manyan kawayen ta masu kuɗi, kasancewar duk sun saka ƴaƴan su a *Seat of Wisdom*
Taji ana hira ana cewa, "Yarinyar da tayi rashin kai a *Seat of Wisdom* video ɗin yake ta trending ɗinnan gaskiya bai kamata ba.
Sai wata ta chapke da cewa "To kuzo kuga gata a offishin hisba an kama ta jiya da daddare karfe goman dare"Wata ta sake karɓa da cewa "Karamar yarinya ce fa, abin da yake bani haushi kamar bata da iyaye masu kwaɓa mata, haba don Allah abin yayai yawa"
Salin alin Hajiya ta tashi tabar hall ɗin, ta duba wayar ta sai taga miss calls dayawa na Amrah, ta tuka mota cikin ɓacin rai ta isa offishin Hisba.....Tun ma kafin Daddy ya kirawo ta kai tsaye taje ta musu magana suka sake mata yarinyar ta.
©FADILA IBRAHIM
YOU ARE READING
DRUG ADDICT ✔
Science FictionNAWWAS a trouble teenager finds him self in the world of taking any kind of drugs, while living a luxury life because both parents were millionaires, As he attempt doing so he became a drug addict, yet he loses everything, his money, his parent, his...