17

2 1 0
                                    

5STAR EXPENSIVE COMPANY

DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
17

ABUJA

"Babu kowa yarinya, mu mu kaɗai muke rayuwar mu" Ya karashe maganar yana mai fitowa waje ya kullo kofar da kyau......"Amma meyasa baku bar gidan ba, meyasa kuke zaune a ciki duk da babu masu biyan ku kuɗin gadin ku" naji tambayar tazo min a gabar da baki na ya buɗe na tambaya.

"Saboda rikon amana, babu abin da yafi rikon amana, wata rana zai iya dawowa gidan sa, mu kuma sai mu damka masa makullan gidan sa"

Na jinjina kai ina kara kwaɗaituwa na san abin da ban sani ba game da labarin NAWAS, Tsahon shekara biyun da yayi baya gidan.

Ina kokarin taka kafa zan bar wajan sai na ga an bugo kwallo ta fito waje ta saman katanga, na ga kwallon tana bouncing, na sake baki ina kallon kwallon, ina mamaki na juya ina kallon Baba mai gadi.

Shima dai ya rasa mai zai ce min, kafin ya buɗe baki yayi magana aka buɗe kofar wani kyakkyawan yaro ya fito ba zai wuce shekaru biyu ba wanda ko magana baya iya yi sosai ya na cewa Baba "Ball ɗina ne"

Yayi magana irin ta yara kanana wanda baza su wuce shekaru biyu ba, Kamannin sa sak ubansa.....Na ce,"Zo ka karɓa" na faɗa ina masa dariya yayin da na ɗauko kwallon ina buga shi sama da kasa....Ya rugo da gudun sa yana dariya, na tsugunna na shafa kansa nace,"What is your name?

*Abdul*

In short ya amsa min yana ɗaukan ball ɗin ya bar wajan yana niyan komawa ciki ne wata kyakkyawar macce fara tas kamar balarabiya tsabar kyau, ta fito sanye da english wears dark blue jeans da milk color top mai kyau ta ɗaura black kimono shara shara a sama, saman kanta kuma dark blue turban ne tayi kyau sosai har sai da na rai na kai na, dana gan ta....wani kishi naji duk dama na rasa daga in da kishin ya fito....Ko dai son NAWAS ɗinne ya mamaye zuciya ta.

Nayi watsi da kishin dake kokarin fitowa ya mamaye zuciya ta, na danne zuciya ta na kirawo sunan ta.

*AISHA*

Da mamaki ta juya tana kallo na, Baiwar Allah wacece ke, ki ka kira sunana haka?

Murmushi nayi na soma takowa zuwa in da take na ce,"Bakuwa ce kikayi daga Bauchi "

Bakuwa kuma, a iya sanina ban taɓa ketare Abuja na tafi wani gari ba, balle ma har na samu bakuwa daga Bauchi, ina dai jin sunan garin amma ban san a ina yake ba" ta bani amsa kai tsaye kuma a tsanake.

Na nuna musu ID card ɗina, ni ƴar jarida ce, kuma nazo bincike ne tare da neman izinin *NAWAS ABDULRAHMAN MAKERMERH*

Sun yi mamakin jin sunan ya fito daga baki na raɗau, ba azziki suka shigar dani gidan suna mai karrama ni, nayi mamaki kwarai ace har yanzu akwai mutane irin Baba mai gadi da Aisha.....suna zaune a gidan ba tareda ha'inci ba, ko taɓa ma Nawas dukiya, kasuwancin ta take yi wato sai da awara da shi take anfani wajan kula da kanta da yaran ta, da kuma su Baba mai gadi.

A lokacin da take shaida min halin da ta shiga a rashin Nawas.....tare da sanar dani kanwar mamanta ta rasu watanni biyu da suka wuce,Dama kuma anan gidan take zaune tun bayan tafiyar Nawas.

Na jima ban ga macce mai hakuri da sanin ya kamata irin AISHA ba, na yi ƴan rubuce rubuce na, sannan na musu sallama, bayan munyi snapping ɗin su ita da Abdul, Na kuma sanar da su NAWAS yana nan garau a gidan tsaron hukumar NDLEA, tare da fatan In Sha Allah sakon su zai isa gare shi.

Ko kara kwana ban yi ba, da yamma nayi booking flight na koma Bauchi, a daren naje na siya abinci Chips and egg na siya da naman kaza sai peak yoghurt, Ina kira waya kafin aka zo aka buɗe min gate na shiga ɗakin mu, kasancewar babban ɗaki ne mai ɗauke da gadaje, wasu sunyi bacci wasu kuma ba suyi bacci ba, ba sosai nake hulɗa dasu ba shiyasa na cire kaya na watsa ruwa nayi sallolin da ake bina, sannan na zauna na ci abinci at the same time ina kara viewing budurwar NAWAS tun da dama ba aure sukayi ba.....Na rasa dalilin wannan tuhumar da zuciya ta takeyi, na rasa ya akayi na fara son mai shan ƙwaya, ni na san halin zuciya ta tun da nake ban taɓa soyayya ba amma meyasa zuciya ta take son ta fara yanzu..... ina wannan nazarin bacci mai nauyi ya ɗauke ni kasancewar bana samun bacci enough.

DRUG ADDICT ✔Where stories live. Discover now