5STAR EXPENSIVE COMPANY
DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
05DAMATURU/YOBE
PotiskumMamman dai abu yaci tura, kullin sai am tsince shi a kwata, ko bola....Abin nashi ma Wee wee ce yake sha kuma ta fara yi masa illa.
Kullin Inna ita ce leka kwatan layi ka, da bolan dake ta bayan unguwan, idan tayi nasara tana samun sa, wani lokacin kuma bata samun sa, haka zai kwana a waje, washe gari yunwa zata koro shi da sassafe.......rayuwar da yake yi ne yasa wata rana Mallam makwabcin Inna ya kama shi da kanshi ya kai shi offishin ƴan sanda Saboda yaron ya ɗauko hanyar lalacewa, gwara a dakatar da shi tun abin bai girma ba.
Kwanan Mamman biyu a station ya daku, an jibge sa kamar ba gobe sannan washe gari aka kai sa gida tare da kashe ɗin idan ya koma ɗabi'ar Shaye Shaye sai an kuma yi masa haka.
Inna taji daɗin abin da Mallam makwabcinta yayi, hakan yasa Mamman baya fita yana ta laulayin dukan da akayi masa, tsahon sati guda....yana cika sati ɗaya ya sa kai tun da ya sa kafa yabar gidan bai sake dawowa ba, tsahon kwana tara, Inna tana ta bada sanarwa a gidan radio garin potiskum.
Wata rana da yamma tana cintan shinkafa aka rugo da gudu ana cewa Innar Mamman kizo maza maza ga Mamman ce yau kwanan shi uku a bola kamar ya mutu fa"
Inna ta kaɓar da tiren Shin kafa, tayi hanyar karshen layi da gudu, taron mutane yasa ta karaya sosai, tana kuka ta karasa wajan da Mamman yake, wanda ashe an kwara masa ruwa ya farfaɗo yana ta tangaliliya, wani abokin sa yace,"Ba fa mutuwa yayi ba Inna, kawai dai mun haɗa babbar ce shine tayi mana yawa a jiki,".....maganar ƴan shaye shaye yake yi, Ya cigaba da cewa, " A ka'ida dama idan kasha daga kwana uku zuwa huɗu ne kake dawowa hayyacin ka"
.Babu abin da Inna take ban da kuka, ta kama Mamman ta kai shi gida, tayi ma Mamman wanka tas bakin jikin sa da Dadtin jikin nasa ya fita tas, ta sanya masa sabon kayan sa, a lokacin Ɗan ta Mamman ya fito sak ainahin Ɗan ta na da, kafin ya fara rayuwar shaye shaye....sosai tayi kuka kamar ranta zai fita.....Shin wannan ne amanar da Allah ya bata, idan Mamman ya lalace fa to dole laifin ta zata gani, amma duk da haka ita uwa ce kuma ta tsaya tsayin daga wajan ganin ta bashi ilimin boko, amma duka yace shi baya son ko ɗaya....to ya zatayi da Mamman.....ta ɗaga hannu tace Ya Allah,ka shiryar min da Ɗa na Mamman.Amin ya rabbi.
KADUNA
HAYIN RIGASAMallam ya wurga masa kayan sa waje yana kara masa kashedi, amma tuni Innar Umar ta biyo shi da ɗan yagulallan mayafin ta, tana kuka tana cewa,"Mallam kayi hakuri zai biya Kuɗin dutsen ba sai kun koran min Ɗa ba.
Kasancewar Umar matashi ne zai kai ashirin da bakwai zuwa da takwas ma, ya ce,"Inna share hawayen ki, ki koma kiyi bacci lafiya, In Sha Allah ba gudu ba ja da baya, ni da ke mutuka raba takalmin kaza, zanje wajan su Jamilu na kwana, gobe zan shigo.
Inna ta girgiza kai zata bishi waje, Mallam yace "Kina sa kafa wallahi a bakin takardar ki, dama kuma ko kwai ɗaya baki saka ba balle ki kyankyashe"
Umar ya shigo ya kwantar wa da Innar tashi hakali, ya tabbatar mata Im Sha Allah babu abin da zai same shi.....matukar tana yi masa addu'a.
Inna ta share hawayen ta ta juya ta koma ciki, ranar Maman walid ne ta shigo tana ta kwantar mata da hankali, kuma daga karshe ta turo mata Mufida ƴar ta suka kwana tare.
Mafarin lalacewar UMAR kenan.
Mafarin Kaddarar sa ta shiga rayuwar Shaye shaye......Umar ya kama hanyar sa ya tafi shagon da su Malance suke kwana, ya tura kofar, ɗakin ban da hayakin taba da warin wee-wee babu abin da yake yi, Umar ya danne kirjin sa ya ɗauke numfashin sa ya fita waje da gudu, sannan ya saki numfashi yana tari tsabar hayakin yayi yawa.....saboda haka Umar ya koma bakin layin su ya kwana a waje kan barandar wani shago, anan ya kwana, da safe kuma ya tashi ya tafi neman kuɗin sa.
YOU ARE READING
DRUG ADDICT ✔
Science FictionNAWWAS a trouble teenager finds him self in the world of taking any kind of drugs, while living a luxury life because both parents were millionaires, As he attempt doing so he became a drug addict, yet he loses everything, his money, his parent, his...