5STAR EXPENSIVE COMPANY
DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
16NDLEA
BAUCHI STATEAisha ta kawo mun ziyara har gida....Ita taga halin da nake ciki ta tausaya min sai ta cire hijabin ta ta fara gyara sashin nawa, duk wasu kwalaben giya ta kwashe su ta gyara ɗakin da falo tas.
Ta wanke min bayan gida, ta fita ta aiki yaron gida wanda wanda yake aike aike tace ya siyo mata kayan miya.....2hours Aisha ta gama girki a sashin mahaifi na saboda a nan ne akwai karamin kitchen.....shinkafa ta dafa da stew yaji naman kaza kasancewar babu abin da babu a cikin freeza sai dai babu mai girkawan, dama Daddy ne yake kokarin yin girkin.
Ina zaune ta kawo mun abinci, ta kai wa masu gadi nasu ta sanya hijabin ta tana cewa, ita zata tafi sai gobe idan ta dawo....Janyo hannun ta nayi, abin da ban taɓa yi ba a iya bariki na ba bu ruwa na da mace.
Ban taɓa kwantawa da macce ba amma yau na tsinci kai na da kama hannun AISHA saboda ta min abin da ba zan taɓa mantawa da ita ba.....Jikinta na rawa saboda rikon da nayi mata sai taban tausayi nayi saurin sakin hannun, na taso na ɗaura hannaye na saman kafadar ta ina cewa,"Kiyi hakuri ko, dama zan miki godiya ne"
"Tayi murmushi, ta ce babu komai, Har ta juya zata tafi sai ta dawo tace Nawas ka dena shan giya don Allah babu kyau a addinin musulunci, kuma kana lalata rayuwar ka"
Har cikin jinin jikina naji wannan nasihar, na gyaɗa mata kai ta tafi.....ranar sai ban sha komai ba, amma wallahi ina tashi da safe na kwalɓe rabin kwalba saboda tabi jikina.
Ranar ma da ta zo a bige nake, na bita har kitchen ɗin sashin Daddy ina mata tinɓele, "Tana ta dariya, tace Nawas nikam ka ishe ni ka barni nayi aiki na" komawa falo nayi na kunna T.V na ina serching channel Mzone a DSTV.
A daidai gabar da ake wani american movie, suna ta iskancin rungume rungume da sumbatar juna.... rike hannu kam ai normal ne....Na natsu ina kallo sai naji karar saukar ruwan sama, haka nayi matashi da lallausan couch ɗin falon Daddy na, nazarin abin yanda ya shiga rai na ina tsananin son na gwada duk da ban taɓa tunanin hakan a zuciya ta ba amma yau ɗaya naji ina so.
Bacci ne yayi awon gaba dani, har Aisha ta gama ta aje min abinci ta tafi....na tashi dai ban ganta ba, Na cu abinci na koma sashi na.
Tsahon watannin biyu AISHA ta ɗiba tana mana bauta a cikin gidan nan, duk wata ina biyan ta amma bata son karɓa.....duk da ina yin abu kamar yaro wani lokacin kuma da hankali na....Kamar kullun Aisha tazo aiki, tun daga part ɗina na bita bayan gida ina tsokanar ta ta hanyar watsa mata ruwa, tun tana cewa bata so har ta soma biye min na jikata ita ma ta jika ni sharkab.
Ta riga ni fita daga toilet ɗin ta tafi bedroom ɗina tana matse kayan ta, na biyo ta ina cewa "Kayan ki sun jike ki cire ki shanya su a dryer mana".....ta gyaɗa min kai amma sai tace,"To idan na cire me zan saka kuma?
Ya buɗe wardrobe ɗin sa babu wani kayan mata, wani babban towel ya ɗauko wanda zai rufe mata har cen kasan kafafuwan ta, ya ce "ki ɗaura wannan to kafin su bushe"
Ta karɓa, ta shiga toilet ta sauya kaya, ta fito bayan taje ta shanya kayan, ta dawo kawai ta ji an janyo ta an manna ta da bango, cikin kwarewa ya soma matsa mata tsokar hannun ta yana sanya bakin sa cikin nata yana sha cike da natsuwa.....AISHA kam tuni ta jima da faɗawa wata duniyar da Nawas ya kai ta.....har sai da yayi nasarar raba ta da budurcin ta, don tun tana kuka tana magiya baya jin komai, har yayi nasa ya koma gefe ya kwanta yana mai da numfashi ya jima a hakan, kafin daga bisani ya tashi ya ɗauki Aisha cak ya kai ta bayan gida sai daya haɗa ruwan zafi wanda yasan zata iya zama, sai ya zaunar da ita.....Da taji wani azaba tayi yunkurin kamo sa tana kuka, haka yayi ta lallaɓa ta suka gama ya ɗauko ta ya dawo da ita bedroom ganin yadda gadon gayi kaca kaca hakan ya tabbatar masa da cewa ita ɗin budurwa ce, kuma shi ya fara mai da ita cikakkiyar mace.
Tun daga ranar na mai da AISHA tamkar mata ta, ina tsananin kula da ita, wanda ko kuda bana son ya taɓa min ita....Rayuwar mu kawai muke zubawa, ban kuma dena shan kayan maye ba....wata rana aka kira ni daga nan Bauchi akan ana son kaya...a lokacin na jima ai banyi harkar ƙwaya ba, na bar gidan banyi sallama da kowa ba har ta Aisha.
Na sake jimawa a bauchi ina harkar a ɓoye, saboda masu fita daga bauchi suje maiduguri suna fita da kayan maye daga Borno zuwa kasashen waje.....tsahon shekaru biyu nayi na ma manta da rayuwar Aisha.
2023,
Suna yen mu ya watsu a duniya, Sirrin mu ya watsu aka fara kamo wasu daga cikin mu, wanda a lokacin banyi tsammanin za a iya kama ni ba.
Ina kokarin guduwa zan koma ABUJA sai sukamin tarko, Hukumar NDLEA su suka riga kama ni kafin Civil defence....hakan yasa da sauran kwana na a gaba su ka rike ni don nema min lafiya tukunna.
Binciken likita na farko ya shaida musu kwakwalwata bata functioning well, babban damuwar da har yau nake fama da shi kenan., Zan iya cewa kwaya ta addabi rayuwa ta, shaye shaye ya zame min jigo na rugujewar rayuwa ta, silar mantawa da dukkan wani abin da ya wuce matukar ba tunani akayi ba to Mahaifi na, wanda ya taka babbar muhimmiyar rawa wajan bani wani sinadari na maye wanda yake hana bacci, tsananin buguwa sai kayi kwana biyu idanuwan ka ma basu rufu ba balle bacci ya ɗauke ka.
Nawas ya sauke ajiyar zuciya yana kama kunci kumatun sa da hannu biyu yana cewa,"Yanzu ko a wani hali Aisha take ciki sai Allah masani.
Hafsat ta jinjina kai tana tsananin tausayin Aisha a matsayin ta na ƴa macce.....bakin ta ya kasa magana ta kai karshen labarin ta rufe littafin ta sannan ta tashi tana cewa,"Gobe ba lalle ku ganni ba zanyi tafiya mai nisa...."Ina zakije Aunty? Mamman ke tambaya.
"Idan na dawo zan zo ai, zaku ganni"
Ina komawa gida, na shirya kayana tsab, har ƴan ɗakin mu suna min tsiya wai *Hafsat busy* to bana zama dana zo dana yi tafiya.
Flight nabi da sassafe....karfe takwas ina Abuja, 9:30 ina tsaye a layin su NAWAS....Da tambaya aka nuna min addereshin gidan sai da na fara ganin gidan da AISHA take wanda baya da nisa dana su NAWAS.
Nayi knocking gidan su NAWAS, Wani dattijo ya buɗe, na gaishe shi cike da girmamawa....na ce,"Baba kai ne mai gadin gidannan?
Ya ce min ,"Eh yarinya wa kike nema?
Na ce,"Ina fatan banyi kuskure ba, Nan ne Gidan *NAWAS MAKERMERH*
"Eh kwarai nan ne yarinya, amma baya nan, babu kowa a cikin gidan ma daga ni sai ɗan yaro na da nake aike"....yau tsahon shekaru biyu da rabi ban sake saka Nawas a idanuwa na ba, ban san wata duniya yake ciki ba, gashi maraya ne"
Na jijjaga kai, ina daɗa son samun wani bayani wanda ban sani ba game da Nawas,nace ,"Amma kace ba kowa a gidan Baba?
"Babu kowa yarinya, mu mu kaɗai muke rayuwar mu" Ya karashe maganar yana mai fitowa waje ya kullo kofar da kyau......"Amma meyasa baku bar gidan ba, meyasa kuke zaune a ciki duk da babu masu biyan ku kuɗin gadin ku" naji tambayar tazo min a gabar da baki na ya buɗe na tambaya.
"Saboda rikon amana, babu abin da yafi rikon amana, wata rana zai iya dawowa gidan sa, mu kuma sai mu damka masa makullan gidan sa"
Na jinjina kai ina kara kwaɗaituwa na san abin da ban sani ba game da labarin NAWAS, Tsahon shekara biyun da yayi baya gidan.
Ina kokarin taka kafa zan bar wajan sai na ga an bugo kwallo ta fito waje ta saman katanga, na ga kwallon tana bouncing, na sake baki ina kallon kwallon, ina mamaki na juya ina kallon Baba mai gadi.
©FADILA IBRAHIM
YOU ARE READING
DRUG ADDICT ✔
Science-FictionNAWWAS a trouble teenager finds him self in the world of taking any kind of drugs, while living a luxury life because both parents were millionaires, As he attempt doing so he became a drug addict, yet he loses everything, his money, his parent, his...