5STAR EXPENSIVE COMPANY
DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
14KANO STATE
HOTOROHafsat ta fara shirye shiryen komawa, Hajiya ta same ta a ɗakin ta, ta rike mata hannayen ta tana kuka, "Subhanallah Hajiya kuka kuma"
Ta sanya hannu zata share mata hawaye sai Hajiya ta dakatar da ita tana cewa,"Bar ni Hafsat nayi kuka , Hausawa na cewa Idan zaka gina ramin mugunta to gina shi daidai da kai, Banyi tsammanin Allura zata tono garma ba, muzguna wa rayuwar ku, na takura muku dake da yayanki amma baku taɓa koda raina ni ba, ko kuyi min rashin kunya ba,, Ban taɓa tsammanin reshen zai juya ya dawo kai na ba.....yau gashi zan girbi abin da na shuka da hannaye na.....Wallahi tsananin kunyar ki yasa bana fitowa a gida ƴan kwana kinnan Hafsat, yau gashi Amrah zata haifa min Ɗan shege.........Hafsat tayi saurin toshe mata baki tana girgiza kai itama kamar zatayi hawayen.
Hajiya ta cigaba cewa,"Abin da yake sani kuka, likita ya faɗamun cewa, Karamar yarinya kamar Amrah mahaifarta babu kwari, kuma ta zubar da ciki sau ɗaya, yanzu ma da kamar wuya ba lalle ta iya haihuwa da kanta ba, dole sai dai idan babyn ya kai sai ayi mata Cs....a hakan ma yace rai yana wajan Allah ne amma walau a rasa uwar ko jairirin.
Hafsat ta lallashi Hajiya tana kara jaddada mata babu abin da zai samu Amrah da yardar Allah......tana faɗa mata ai yanzu Amrah tana wajan Daddy shi yake kaita Islamiyya kuma yaje ya ɗauko ta, cikin jikin ta ma ya fara girma kuma Yakumbo na kula da ita.
Hafsat ta tsagaita jin Hajiya na tari daga bisani ta soma aman jini, Bata taba ganin Hajiya cikin wannan yanayin ba sai yau,..... Ruɗanin da Hafsat ta shiga shi ya sanya ta kuka ta rasa ta ina zata fara, mai gadi ta kira yazo da gudu ya kama mata suka fitar da Hajiya suka sanyabta cikin mota, ta kai ta wani private hospital aka shiga emergency da Hajiya.
"Hello Daddy!!!!!!
"Na'am Hafsat Yaya kamar hankalinki a tashe?
"Daddy Hajiya ce muna asibiti tana aman jini" ta karashe maganar ba tareda natsuwa ba tsabar hankalin ta a tashe.
"Subhanallah, bari na ɗauko Amrah a Islamiyyah mu taho da Yakumbo"...."Ki kwantar da hankalin ki kinji babu abin da zai faru."
"To DADDY kuyi sauri don Allah".......tana kashe wayar wani kira yana shigowa wayar nata daga group ɗin su na CDS ne ake kiran ta kasancewar akwai batch ɗin da zasuyi POP to president ɗin zaiyi handing over kuma ita zai ba mawa as new president....Ta faɗa musu tana nan dawowa gobe In Sha Allah.
Bata jima da kashe wayar ba sai ga Daddy sun iso, ta hango kanwar ta Amrah sanye da uniform ɗin islamiyyah, ya mata kyau har da nikab, tazo ta rungume Hafsat tana kuka mai har da shesheka Hafsat ta ce,"Yi shiru Amrah addu'a zaki mata"
"Aunty Hafsat halin da nake yi ne ya janyo mata shiga wannan yanayin, gashi.........."Shihhhhh Amrah kuyi hakuri tukunna, ku bari muji condition ɗin da take ciki ga likitocinn nan fitowa." ya faɗa a daidai lokacin da suka tashi suna tunkarar likitocin.
Likitan ya gaisa da Daddy yana kara karrama shi saboda sun san shi, likitan na cewa dama Matar kace aka kawo?
"Eh" Daddy ya mayar masa amsa,....likita ya ɗaura da cewa "Ku kwantar da hankalin ku jinin tane ya hau sosai amma yanzu mun mata allurar da zai saukar mata da hawan jinin....don Allah ku kiyaye bacin ranta saboda zata iya rasa ran ta a ko da yaushe"
Bayan wannan lokacin sun jima zaune a reception Hafsat ta faɗa wa Daddy cewa zata koma Bauchi gobe idan Allah ya kai mu....Daddy yayi na'am da bukatar nata amma duk da haka bai so ta tafi da wuri haka ba, yaso ace ta kara jimawa tare da ƴar uwar ta ko wani abu zai canja, Daddy na tsoro kar Amrah ta koma halin data baro.
Ni da Amrah muka kwana a asibitin, washe gari bata farfaɗo ba, tafiya ta nayi kawai, Yakumbo ke kula da ita, Daddy ma yana zuwa akai akai.
NDLEA
BAUCHIWashe garin ranar dana koma naje Clearance da safe a fed sec bauchi, a hanya ta na dawowa sai na tsaya nayi take away a aroma har biyu na nufi offishin NDLEA.
Na jima ina zaune a wani dogon bench da aka tanadar mun don zama, ashe ana musu orientation ne a cikin wajan.....Kallon wajan nayi kawai banyi tsammanin zan ganshi yana taho wa ba.
Ya kara kyau sanye cikin brown trouser da long sleeve turtle neck sweater wanda ta ainahin fito masa da tsayin sa da kuma sirantar sa, tafiya yake cikin natsuwa kanshi ƙasa yana tafe yana girgiza kai alamar yana magana da kanshi, tarun gashin kansa an aske masa shi ya sake fitowa shine aka kitsa masa shi, gefen sa Mamman ne wanda yaron yayi duhu bakin sa yayi baki tsabar wiwi tayi masa yawa, suna tafe suna magana da junan su har suka iso in da nake.
Murmurshi kawai na sakar musu, na tura musu takeaway ɗin abinci kowa da nasa, suka hau ci suna min godiya....tas suka cinye a gaba na, Mamman na cewa bama cin kaza anan wallahi.....Dariya nayi sosai
Na kalli Nawas nace Bisimillah zamu ɗaura daga inda muka tsaya.....Nawas ya ce shi ya manta, na buɗe littafin na nuna masa daga inda muka tsaya, sai ya gyaɗa kai kaman mai nazari naji ya ɗaura da cewa.
************
A shekarar da gwamnatin ELRUFA'I ta kawo ziyara wato shekara ta dubu biyu da goma sha tara.....2018-2019
Sun kawo ziyara tare da manyan polisawa saboda wani gagarumin abu daya faru a wannan gida na Malam Niga.
A lokacin a wani gidan almajirai a cikin hayin rigasa an samu malaman suna lalata yara matasa ciki har da yara mata, Dalilin da yasa Gwamnatin Elrufa'i ta kawo ziyara cikin karamar hukumar igabi local government suka fara binchiken duk wani gida daya kasance gidan tsaron masu shaye shaye da kuma ko wani gidan Almajirai.
Cikin wannan yanayi na binchike aka shigo gidan Malam Niga yayin da suka tarar damu ana azabtar damu ta hanyar bada horo wai duk akan mu dai na shaye shaye, masu sata su dena duk akan mu gyara halayen mu.
Anyi hira da shi sosai wanda ya fahimtar da mutane da duk waɗanda basu gane ainahin abin da ke faruwa a gidan MALAM NIGA ba.
An fara wannan rigimar sai na samu hanya na gudu saboda banga anfanin zama na a gidan ba.....dana samu hanya na gudu, na kunce marin kafa ta na tsere kai tsaye gidan MAHAIFI NA na tafi Abuja.
Da daddare na karasa gidan kuma masu gadi suka buɗe min na shiga......Gidan mahaifi na mai kyau ne ya gina gida tsararre, wanda nayi mamakin sabon gidan da yaushe ya gina kuma akwai part ɗina daban, na shi babban flat ne mai kyau da ɗakuna birjik a ciki.
Na je da niyar kashe shi amma sai na fasa kuma na hakura, a lokacin na rage shaye shaye giya kaɗai nake sha, dama ni ba masoyin taba bane, ina taɓawa ba sosai ba.
Na koma karo na biyu kenan, idan masu karatu suna fahimta, Na koma bayan na fito daga prison, yanzu ma bayan na gudo daga gidan malam nigga na sake komawa don cika wani buri nawa.
Anan kuma na sake haɗuwa da wani ɓangare na sashin labari na wanda yayi daidai da komawa ta shaye shaye bayan na dawo daga India. idan baku manta ba na tafi india bana shan komai, na dawo bana shan komai, zuwa na Abuja kuma komai ya taɓarɓare na sake komawa halin ɗan ɓera.
©FADILA IBRAHIM
YOU ARE READING
DRUG ADDICT ✔
Science FictionNAWWAS a trouble teenager finds him self in the world of taking any kind of drugs, while living a luxury life because both parents were millionaires, As he attempt doing so he became a drug addict, yet he loses everything, his money, his parent, his...