18

2 1 0
                                    

5STAR EXPENSIVE COMPANY

DRUG ADDICT
(NAWWAS)
©Fadila Ibrahim
18

DUNIYA JUYAYI  Da sanyin la'asar, wajan wata bishiya wacce suke kira da Umbrella fruit, sallaya ne shimfiɗe,  Nawas ne da Mamman suke bitar Alkur'ani, sai wani malami da yake zaune saman kujera shi yake koya musu, wanda Hafsat tayo hayar shi saboda abubuwa sun yi mata yawa ta koma kano.

Sosai Nawas yake fitar da sauti yake kuma ba ma kowacce harafi hakkin ta yayin da yake fitar da kira'a mai daɗin sauraro kasancewar dama ya sauke Alkur'ani rashin tilawar shiya janyo masa yin baya da kowacce sura, yanzu gashi yana dawo da abin sa.

Basu jin kiran sallah a wajan saboda babu wani masallaci a kusa, sai dai suyi amfani da hatsi da kuma saukar rana bayan la'asar kenan sai suyi sallah, rana na faɗi suyi magrib, dare wata na fitowa kuma suyi isha'i,.....sosai rayuwar su ta soma canjawa, ciki har da wasu musulmai a cikin prison ɗin suna fitowa don a koya musu karatun addini.

KANO STATE

*Bayan Shuɗewar Watanni Biyu*

Hafsat ta jima da mallakan takardun degree ɗin ta, yayin da ko sallama batayi da Nawas ba ta koma kano don gina rayuwar ta, suna da number ɗin ta a rubuce, malamin kuma duk wata yana jin alert na kuɗin sa.

Tana dawowa Daddy ya cika mata alkawarin ta ta fara aiki da BBC.

Cikin kwarewa ta fara wayar dakai ga al'ummar mu matasan mu masu zaman banza, ta ɗaga kungiyar ta mai tallafa wa mata kana na da manya wanda suka rasa abin da zasu bama iyali,.....aikinta na farko a BBC shi ya ɗaga ta batayi shekara ɗaya ba aka kai ta level 5  saboda kwazon da suka gani a tare da Hafsat da son taimakon al'umma.

Kachokam ta koma Abuja da zama, bata sake bin hanyar bauchi ba, lo hanyar gidan su Nawas....sanadin ta ta shiryar da masu shaye shaye sama da ashirin a kowanni fanni tsakanin rayuwa ko mutuwa, bata da tsoron tunkarar su, Jigon ta shine ta isar da sakon da take son isar wa wato *YAKI DA FATAUCI DA MIYAGUN ƘWAYOYI*

A turance ana kiran sa da*WAR AGAINST DRUG ABUSE*

Sunan kungiyar ta kenan, wanda idan abin ya gagare ta tana haɗasu da hukumar NDLEA a kowani gari, Abuja, Kaduna, and Bauchi....Kano kam duka suke wa mutum su haɗa shi da Civil defense....Allah yasa rayuwar matasan mu ta sauya.

Tun daga bakin kofar mashigar da zai sada ka da wato ainahin falon gidan, sautin karatun da yake fita daki daki dallah dallah na muryar mutum biyu shike amsakuwwa a cikin kunnuwan masu sauraro, yayin da kowani ma'aikaci yake aikin sa a tsanake, Hajiya na cikin kuryar ɗakin dake sashin ta na shan wasu magunguna ta taso ta sauko kasa tana son taje taga ƴaƴan ta.

Ma Sha Allah, Allahu Akbar take ta nanatawa yayin da idanuwan ta suka sauka akan yaranta mata biyu sanye cikin Hijab suna tilawar alkur'ani mai girma...Ta na zama bata jima ba Daddy ya shigo, tun daga annurin fuskar shi zaka fahimci cewa yana murna da sauyin daya samu a wajan yaran sa mata guda biyu..  ashe dai ƴaƴa mata rahama ne, Allah abin godiya ya sanya musu albarka, ya haye sama Hajiya ta tashi ta bishi don tana da magana itama a bakin ta.

*********

KANO
HISBA BOARD

2years later
6:30pm

Kiran sallar magrib kasancewar lokacin azumi ne kowa yana kokari yaji an kirawo sallah, ya saka abu a bakin sa.

A daidai wannan lokacin mutanen dake wajan suka fara jiyo kakkaurar muryar da take kiran sallah ita ce abin dubawa, murya ce mai cike da amo da zati wajan fitar da sautin kiran sallah mai daɗin sauraro ga duk wanda Allah ya halicce shi da kunnuwan ji da sauraron abu.

DRUG ADDICT ✔Where stories live. Discover now