BABI NA UKU

25 3 2
                                    

BAQEER
     NA
UMM ASGHAR
DA
AYUSHER MUHD

PAID BOOK

ƊANƊANO DAGA TAGWAYE SHAFI NA UKU

KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?
INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

{3}

Kishingiɗe yake akan kujera fuskarshi sanye da glasses yana karanta jarida, jefi-jefi yana ɗan kallon tv ɗin dake kunne a cikin falan, shigowar da tayi cikin parlourn ne yasa ya kalleta, sanye take da wani haɗaɗɗen lace wanda yabi jikinta ya zauna ɗas, baka ce daidai misali sannan tana da tsayi wanda hakan yasa ba'a ganin kibarta sosai, mace ce mai fara'a wanda fuskarta kullum a sake, murmushi ta sakar mishi tace "Diatinguished Senate ana sallama da kai."
Rufe jaridar yayi yana dariya yace "Wai har kin bani matsayin?"
Ta zauna a gefenshi tana cewa "Me za'a fasa? Ai kujera ka hau ta ka gama, sai da kai uban  Zainab da Kabir."
Kai ya girgiza yana wani irin murmushin jin daɗi yace "Ke dai Halimah wallahi baki da dama." Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye daga kan kujerar "Bari na leƙa naga wanene?"
"Yana waje nace mai gadi yace ya shigo falon baƙi yace a'a."
Waigowa yai ya kalleta yace "To me yasa?"
Ta ɗan girgiza kai tace "Wallahi ban sani ba, ƙila kunya yake ji ko sauri yake."
Bai ce komai ba ya ke kallanta, ta sake murmushi tace "Ai sai naga wajen ma kamar yafi ko?"
Yanda ta kalleshi ne yasa ya saki fara'a yace "Wannan matar baki da dama, nafahimta kuma sosai yafi, bari na wuce."
Nan ya fito yana sake tabbatar da fitilun waje da fatan a kunne suke, sannan ya taɓa aljihunshi ya tabbatar yana da wadatacen kuɗi, gate ya buɗe ya kalli mutumin dake tsaye a waje ya ɗan juya baya.
Daga bakin gate ɗin yace "Assallamu Alaikum."
Da sauri Baba ya juya suka kalli juna ido cikin ido, wani kallo suke yiwa junansu na wasu dakiku kafin Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya dake ya kauda kai yace "A'a Alhaji Badaru? Wai kaine dama?"
Baba ya sake tamke fuska yace "Kira min yaronka kace ya gaggauta dawowa dan daga nan wurin ƴan sanda zan yi dashi."
Nan da nan fuskar Alhaji Sulaiman Ƙaraye ta canza, yayi mishi wani kallo sosai yace "Wai kai har yanzu baka girma da wannan shirmen bane? Sai yaushe zaka girma ka daina magana kamar mara tunani? Ni yanzu kaf garin nan kana tunanin akwai wanda ya isa ya kama min ɗana?"
Cike da masifa shima yace "Kai kana ganin nima kaf garin nan akwai wanda ya isa ya nemi halaka ɗana inyi shiru? Ka gaggauta sawa a ƙira shi ko kuma in tattaro dattijan unguwar nan in sanar dasu abinda yayi."
Nan da nan gaban Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya hau faɗuwa mai kuma yaron nan ya sake jawo mishi? Waya ya ɗauko ya ƙira Hajiya Halima wacce har yanzu tana nan a zaune a falon tana jiran dawowarshi, ringing biyu ta ɗauka, tana ɗagawa tace "Senate kun shigo ne?"
Yasa ƙiran a speaker sannan yace "Ina yaran nan yake?"
Cike da mamakin yadda yayi maganar yasa tace "Yana ɗaki a kwance, tun safe yake ɗan fama da zazzabi shi yasa ko abincin dare bai ci ba."
Kashe wayar yayi sannan ya kalli Baba yace "To ka dai ji yana gida, menene kake faɗa akai haka?"
"Tunda yana gida komai yayi daidai, sai ka sa ya fito ya sanar dani a wani matsayi ya ɗauki ɗan adam da har zai buge ɗana a mota sannan dan rashin imani yaja motarshi ya tafi? Wallahi kai kafi kowa sani akan Baqeer ba abinda bazan iya aikatawa ba sannan duk wani abinda ya sameshi wallahi bazan yarda ba, hukunci kuma dole ne ya fuskanceshi daga hukuma."
Da sauri Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya ɗaga mishi hannu yace "Ya isheni haka nan Malam! Kai banda ma saukin kaina har ka isa kazo ƙofar gidana kace zaka yi mini zancen banza? Sannan yaron nan ance maka yana gida tun ɗazu ko kana nufin karya muka yi maka? In zaka je ka nemi wanda ya buge maka ɗan ka kaje ka nema amma ba Kabir ba." Bai jira Baba yace komai ba ya sake cewa "Sannan kana tunanin hukumar ta isa ta kama yaran da bai da laifi ne tace zata hukuntashi?" Ya kalli mai gadi yace "Kabiru ya fita yau?"
Da sauri yace "Ni rabona dashi tun jiya daya shiga yau ko masallacin daya saba zuwa bai fito ba" yayi maganar kanshi a ƙasa don kuwa yasan ƙarya ce ya shirga shi Kabir ɗin da kanshi ne ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura yace yau ya ganshi bare har aje ga batun fita.
Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya kalli Baba ya ƙira wayar Kabiru itama yasa a speaker yace "Kana ina?"
Cikin sanyin murya yace "Dad ina ɗaki inzo ne?"
"A'a naji ance ka fita ne ɗazu."
Ɗan nishi yayi yace "Ina zan je ni kam bayan tun dare nake kwance ina fama da zazzaɓi?"
Kashe wayar yayi ya kalli Baba da duk jikinshi yayi sanyi, ba dai yaran nan basu ma gama tabbatar da wanda yai hatsarin ba?
Hannu Alhaji Sulaiman Ƙaraye yasa a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mai yace "Tunda akan su kazo yiwa yarona sharri gashi ni mai iya baka ne kyauta abinda ya faru a tsakanin mu da ya riga ya wuce." Ganin Baba ya kasa ko motsi yasa ya saka mishi a aljihu ya juya ya koma ciki.
Baba Badaru shiru yayi ya dafa kanshi yana da na sanin zuwa ƙofar gidan mutumin da tun asali basa ga maciji dashi, ganin zai shige cikin gidanshi ne yasa shi hanzarin bin bayanshi ya watsa mishi kuɗin daya saka mishi a aljihu yace "Kai dai kasan har abada ba zaka taɓa yin kuɗin da zan zo wurinka maula ba, me jiya ma tayi bare yau?" yayi wani matsiyacin tsaki ya juya ya bar wurin ya ƙarasa motarshi ranshi yana wani irin ƙuna da ɓacin rai, kanshi ya kwantar a kan sityarin motar yana sake tuno hannun Baqeer dake mane da bandage, fuskarshi ya shafa cikin tsananin tashin hankali, ya zai yi in har wani abu ya samu Baqeer? Kenan duk burin daya daɗe yana shiryawa zai tashi a banza? Kenan duk yadda ya sadaukar da komai akan Baqeer ɗin komai zai zo ya wargaje? Nan da nan ya shiga wani irin yanayin da yaji gaba ɗaya komai yayi mishi zafi, wayarshi ce tayi ƙara wanda yasa shi ɗauka.
"Alhaji kana ina ne? Meya samu Fatima ne ta shiga ɗaki sai kuka take yi." Abu tai maganar cike da damuwa ita a dole bata san meya samu Baqeer ba.
Tsaki yaja yace "Bana son shirmen banza, ita yarinyace da in tana kuka za'a nemeni a waya? Ko kuwa salon raini ne wannan?" Cike da dana sani na makirci tace "Kayi haƙuri Alhaji nayi kuskure." Kashe wayar yayi ya sakata a gefen mota tare da duba agoggon hannunshi ƙarfe sha ɗaya da rabi (11:30) na dare, asibiti ya koma zuciyarshi na sake ɗaukar zafi.
Kai tsaye reception yaje ya cire kuɗi daga cikin wanda gomnati ta bashi dan shirye-shiryen gasar da Baqeer zai tafi ya biya kuɗaɗen da ake bukata sannan ya nufi ɗakin da aka kwantar da Baqeer, mamaki ne ya kamashi ganin Bashir baya ɗakin kenan da yace ya zauna yawonshi ya tafi? Alwala yayi tare da yin sallar isha'i a ɗakin sannan ya samun kanshi da dagewa da yiwa Baqeer addu'a akan Allah ya tashi kafaɗunshi a yau ɗin nan dan su cigaba da shirye-shiryensu tunda tafiyar nan dai matsowa take yi, ya daɗe yana addu'a kafin ya dawo inda Baqeer ɗin yake, shiru yayi yana tunanin yadda rana ɗaya rayuwa take neman juya musu baya, yadda komai yake neman rugujewa bayan ya daɗe ya kuma ɗauki shekaru masu yawa yana faman shirya ma zuwan wannan lokacin, yatsun hannunshi ne yaji alamun sun motsa, a zabure ya saki hannun ya kalli Baqeer dake kwance fuskarnan tayi fayau yace "Baqeer? Ka farka? Ni dama nasan bazaka bani kunya ba, na sani kai kaɗai ne wanda baka wasa da farin ciki na, Baqeer buɗe idonka ka ganni kaji ɗan albarka."

BAQEERWhere stories live. Discover now