*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR**RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA**KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯08142800199
07068558096*2*
Yau tunda ta tashi take jin jikinta babu daɗi gabaki ɗaya yayi mata nauyi ga wani irin ƙunci da ya lulluɓe kirjinta lokaci zuwa lokaci sai taji gabanta ya faɗi, komai take yi tana yin shi ne cikin rashin karsashi tunda tasan ba rashin lafiya take yi ba sai dai yanayin data samu kanta a ciki sam baya yi mata daɗi. A kasalance ta yunƙura daga inda take kwance a tsakar ɗakinta ta tashi, tsakar gidansu ta fito ta hau tattare wajen da suke yin girki don itace da girkin ranar, haka nan cikin dauriya ta samu ta haɗa wutar ta ɗora tukunya, aikin take yi salalaf-salalaf kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki don sam jikinta baya da wani ƙwari.Tana lura da abokan zamanta da suke ƴan maganganu ƙasa-ƙasa a gefe da sun ganta sai suyi shiru suna zunɗenta da baki abinda yasa ta ƙara tunanin tabbas akwai abinda ya faru da suke ɓoye mata duk kuwa da ba yau ne karon farko da suka taɓa yi mata irin hakan ba sai dai na yau ɗin yayi tsanani ga kuma yanayin data tashi dashi tun safe yasa tayi tunanin tabbas ba lafiya ba, gashi ma maigidan tunda ya fita bai dawo ba haka nan Baqeer yau yayi nisan kiwo abinda ba halin shi ba ya fice waje yayi zamanshi in har ba wani muhimmin uzuri ne ya riƙe shi ba ba tare da ya leƙo yaga a halin da take ciki ba don duk inda ya tafi hankalinshi yana kanta sanin irin zaman da take yi a cikin gidansu yasa baya son yin nesa yana barin gidan don kaɗan da aikin mutanen gidan suyi mata wani abun na cutarwa ita kuma ba iya kare kanta take yi ba.
Har ta gama girkin ta raba kamar dai yadda suka saba Baqeer bai shigo gidan ba abinda ya ƙara ɗaga hankalinta don baya taɓa kaiwa magriba a waje duk inda yaje yana ƙoƙarin dawowa gida kafin ayi sallar magriba idan kuma ya zama lallai sai ya daɗe a wajen to tabbas zai kirata a waya ya faɗa mata. Sai da ta kawar da komai ta tsaftace wurin kafin ta tashi ta koma ɗakinta, wayarta ta ƙara ɗauka ta kira number Baqeer sai dai har yanzu a kashe ake ce mata, juya akalar kiran tayi zuwa ga wayar maigidan sai dai har ta ƙari ɓurarinta ta gama bai ɗauka ba, ƙara kiran wayar tayi amma har yanzu bai ɗaga ba. Tunani tayi watakila sallah yake yi don haka ta ajiye wayar da zummar ta sake kiranshi in anjima, tashi tayi ta fita don ta ɗauro alwalar ita ma tayi sallah sai dai abinda taji a tsakar gidan yasa ta sakin butar dake hannunta ta faɗi sauran ruwan dake cikin butar ya tsiyaye akan simintin tsakar gidan nasu.
Kamar wacce aka jeho sai ganinta suka yi a gabansu tana cewa "Me ya samu Baqeer ɗin kuke ɓoye mini? Ni dama nasan shirun nan nashi bana lafiya bane tabbas akwai abinda ya faru dashi, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙare da ɗora hannayenta bibbiyu a kanta tana kuka.
"Ke dallah kada ki cikawa mutane kunne da kwakwazo a cikin gida, wani abu kika ji ance ya samu Baqeer ɗin da zaki cika mu da iface-ifacen kuka," Uwargidansu Jamila tayi maganar cikin yi mata tsawa.