BABI NA TARA

32 3 0
                                    

BAQEER🦼
     NA
UMM ASGHAR
DA
AYUSHER MUHD

RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TARA

Dandano......

{9}

Yallaɓai yana kashe waya Bello ya daka wani irin tsalle tare da yin ƙaramin ihu, lalai ba shakka rayuwa zata fara masa da ɗi yanzu, masu mai gani-gani su shirya ganin abinda zai zama yanzu. Sako ne ya shigo wayarshi na Yallabai akan wai ya tura samples na zanen dayai ya gani dan ya sake tabbatarwa akan ba matsala.
Ajiye wayar yai ya durkusa ƙasan gado yana jawo zanukan da yai, wanda kusan kowane ya ɗaga sai yaga Baqeer ne ya tayashi ko kuma Baqeer ne ya nunamai yanda zaiyi, tsaki yai yace "Nuna min yai ai ba shiya zana min ba." Kallan initial na sunanshi da ya saba amfani dashi yake wato BB da sauri yasa pencil ya ƙara M a gaba nan danan da ɗi ya ƙara rufeshi ba shakka Allah ne ke sanshi da rahama, shafar zanen yai yanajin wata nutsuwa na sake zuwa mai, yau ina mutanen dake ganin zane ba inda zata kaishi? Wanda ciki harda mahaifinshi? Dole ya shayar dasu mamaki dan bazai sanar dasu ba sai yaje ya ciyo gasar da za'ai a Abuja nan ne fa zai nuna ma duniya shi ɗin wanene.
Haka ya ɗau hotuna kala-kala ya tura nan da nan Yallabai yamai reply akan komai yayi sai sun haɗu gobe.

******

Kallan ɗakin tai cike da jin daɗi a hankali ta ke sake takawa ciki, wani sanyi na sake ratsata, ta baya taji an dafata, ba tare da ta juyo ba ta saki murmushi tace "Senate Allah yayi autata zata dawo."
Kai ya girgiza yace "Ke dai wallahi san yaran nan ya miki yawa, ina fitowa da naga ban ganki ba dama nasan kina nan, ba last year tazo hutu ba?"
Waigowa tai tace "Hutun wata ɗaya ne fa kacal? Yanzu kuwa fa? Kaga dai wannan karan inta dawo shikenan ba komawa."
Kai ya girgiza yana kallan yanda tasa aka canza komai na ɗakin, kallanta yai yace "Nabeela ce zataje airport ɗin?"
"Eh nace taje dan kasan halinta in taga ka tura yaran nan shi kaɗai bamusan me zata aikata ba."
Yana ɗan jinjina kai yana cewa "Sam bansan meke damun yarinyar nan ba, ace wai ita ba'a isa a hadata da wani ta kulashi ba? Tunda kike da ita kin taɓa ji tace tanasan wani? Ita bata kawo ba sai taurin kan tsiya."
Hannunta ta saƙala cikin nashi tace "Calm down please my Senate, kasan Zeey abubuwa ne suke mata yawa, ita bawai auren bane bataso kawai....."
Hannu ya ɗan daga mata alamar tai shiru yace "Nidai Allah tana dawowa ki sanar da ita ko ta kula wannan ko karta kulashi a shekarar nan zan aurar da ita, sam banasan yarinya mace ta min girma haka a cikin gida, tun yaushe nake san aurar da ita amma abu yaki yiwuwa?"
Sanin halinshi yasa ta nemi janye maganar da cewa "Yau ne zakuyi meeting ɗin da kace?"
Fara tafiya yai yana fita daga ɗakin yana cewa "Yau ne, nidai ki faɗawa Nabeela taja mata kunne kindai san wannan ɗan wanene bansan shirme."
Zatai magana yace "Da zatai rabin hankalin Nabeela da ba haka ba." Daga nan bai jira tace wani abu ba ya wuce, itadai sam batasan ya zatai ta nusar dashi akan ya rage tsauwalawa Zeey ba.

***
Baqeer tunda Mama ta fita ta barshi a ɗaki yake zaune a gun, banda ƙoƙarin riƙe pencil dayake tayi babu abinda yakeyi, ganin yafi awa ɗaya yana abu ɗaya yasa ya runtse ido, yanajin wani irin kunci a zuciyarshi wanda kawai yacigaba da samun kansa da addu'ar Allah ya ɗau ranshi ya huta da wannan bakin cikin, Fatima ce ta shigo jiki a sanyaye tace "Baqeer bari na roki Bashir ya taimaka ya kaika bandaƙi kai alwala azahar tayi."
Kamar wanda aka daɓa masa wuka a zuciya haka yaji kalamanta, shikenan shi yanzu komai sai an taimaka mai yayi kenan?
Kasa magana yai har sai da ta fita ya ciji kasan leɓensa yana sake runtse idanuwansa.
"Bashir baya nan, sannan banaji sanda na haifi ɗan akwai gadan zaki sashi wahalar nakashashen ɗanki."
Kalaman da Jamila tace kenan wanda yasa Fatima hadiyar yawo a ranta tace "Inama yanada kani namiji?"
Abu ta kalla tace "Abu dan Allah naga kamar Kamalu ya shigo ko zaki mai magana?"
Baki Abu ta buɗe tace "Kamalun saninshi ne bakiyi ba? Sai kije da kanki ai kinsan ɗakin shi."
Kamalu shine mai bin Baqeer a gun mahaifinsu, sam ba jituwa tsakaninsu, tunda yaga Baban yanasan Baqeer sosai sai ya kangare ba wanda ya isa ya sashi balle ya hanashi, har zargin shaye-shaye akemai sai dai tsoronshi yasa inba Baba ba bamai masa magana. Wani tunani ne yazo mata wanda yasata juyawa ta koma ɗakin tana murmushi tace "Baqeer bama sanan amma na ƙira Salim yace dama gashi nan zuwa."
Kai kawai ya ɗaga dan yasan akwai abinda ya faru faɗane kawai batai ba, hanyar fita tai ya daure yace "Umma dan Allah aran wayarki." Cikin sauri ta miƙa mai, ya fara ƙoƙarin sa hannu dama zai amsa, da sauri ta ɗau ra mai akan cinyarsa ta fita ɗakin zuciyarta na sake karyewa, gaba ɗaya intaga Baqeer a haka sai taji hawaye, Baqeer ɗinta wanda a koda yaushe yake cikin ji da ita wai shine a wheelchair.
Wayar ya ɗauka da hannun hagu ya sa number Asiya ya ƙira, tana zaune suna cin abincin rana itada Habi, ganin ƙiran da number da bata sani ba yasa ta ɗaga, tace "Hello!"
Baqeer ya haɗiyi wani abin yace "My love!"
Dam gabanta ya faɗi dan kuwa tasan waye, cak ta kame ta kasa magana, Baqeer ya daure ya sake cewa "My love am so so......"
Kashe wayar tai da sauri tana maida hakki ta maida kallanta kan Habi wacce take cewa "Wenene? Ko Baqeer ne?"
Abincin ta cigaba da ci tace "In ma shine sai me? Kinga ni dan Allah ki kyaleni ke in hakan ta faru dake ki tabbatar baki bar mutum ba."
Habi cike da takaici ta tsame hannunta tace "Butulci dai babu kyau."
Wata muguwar harara Asiya ta zabga mata ta ɗauke kanta.

BAQEERTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang