BABI NA GOMA

32 2 0
                                    

BAQEER🦼
     NA
UMM ASGHAR
DA
AYUSHER MUHD

DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA

Kallon inda Asiya ta fara tafiya kawai yake yi baki a sake, jikinshi na wata irin rawa da tsuma ta tsananin tashin hankalin daya tsinci kanshi a ciki yanzun nan, shi maganar yarinyar can ma bata ɗaga mishi hankali ba irin maganar da Asiya tayi. Cikin rawar murya yace "Me kike nufi kenan Asiya? Saboda Allah ya aiko mini da ƙaddara kike nema ki gujeni? Ina alƙawarin da muka yiwa juna na duk rintsi duk wuya muna tare babu abinda zai iya rabamu, shine yanzu zaki janye maganar saboda kinga Allah ya mayar dani haka?"
Yai maganar wani siririn hawaye mai ɗumi ya biyo gefen idonshi ya silalo kan kumatun shi, yana jin wani irin ciwo mai zafi na damƙa a cikin ƙirjinshi har ma fiye da yadda yaji lokacin da aka sanar mishi da ƙaddarar data same shi, dan tunda yake rayuwa bai taɓa tunanin akwai abinda zai sashi rabuwa da Asiya ba, komai na rayuwar shi da ita yake ginawa, dame akeso yaji?

Cak ta tsaya sannan ta waigo tare da sake takowa inda yake, wani wulaƙantaccen kallo ta watsa mishi tayi tsaki "Kai nan a tunaninka zan iya cigaba da yin soyayya da kai, a hakan? Kalle ka fa ka kalleni kai ma kasan ajina yafi gaban na zama matar gurgu, never wallahi har abada" Ta ƙarasa maganar tare da tofar da yawu kamar taga wani abun ƙyama. Juyawa tayi ta fara tafiya sai kuma ta juyo ta kalleshi irin kallon tsaf ɗinnan kafin tace "Ina fata zaka cireni daga cikin ranka ka manta ka taɓa sanin wata mace mai suna Asiya, ka ɗauka duk soyayyar da muka yi a cikin mafarki ta gudana ba gaske bane don ni tuni na cireka daga cikin zuciyata daga lokacin da nasan ka zama nakasashe gurgu nasa a raina ban taɓa saninka ba don haka nake haɗa ka da Allah kada ka ƙara nemana ko a waya ko kace zaka zo gidanmu don idan kazo ma bazan fito ba." Daga haka ta juya tayi tafiyarta ta barshi yana ƙwala ƙiran sunanta yana cewa "Please Asiya kada kiyi mini haka, kada ki juya mini baya don kinga larura da ta sameni, idan kika barni a cikin wannan halin dana tsinci rayuwata ban san inda zan waiwaya ba naji daɗi kuma."

Ko waiwayowa bata yi ba har ta ƙurewa ganinshi kuwa, haka ya sunkuyar da kai yana zubar da hawaye mai ciwo yana jin wai yau shi Baqeer, Asiya take faɗawa waɗannan maganganun saboda taga yadda Allah yayi dashi, har Salim ya dawo kanshi yana ƙasa ya kasa ɗagowa, sai da ya dafa kafaɗarshi sannan yasan ya dawo don dama matsawa yayi ya basu wuri. Salim gani yayi fuskar Baqeer tayi jawur gashi tayi caɓa-caɓa da hawaye.

"Lafiya kuwa Baqeer? Wani abu Asiyan tace maka naga duk ka firgice ka fita daga hayyacinka?"

Girgiza kai kawai yayi don bai ji zai iya buɗe baki yayi magana a daidai wannan lokacin ba, maganganun da Asiya ta yaɓa mishi sosai suka dakeshi duka bana wasa ba don ko kusa bai taɓa tsammanin tana daga cikin butaulallun mutane ba masu saurin manta alheri, bai ɗauka a cikin ɗan taƙaitaccen lokaci Asiya zata juyawa soyayyarshi baya ba sai kuma gashi ta ƙaryata tunaninahi ta nuna mishi rashin amana irin na mutanen wannan lokacin.

*****

A kwance Habi ta shigo ta tarar da ita akan katifarsu tana danne-danne a cikin waya. Kallon tsaf tayi mata taga babu abinda ya dameta da abunda tayi sai ma wani ɗan murmushi da take saki idanunta manne da allon wayar. Ninke hijabin ɗin data fita dashi tayi ta ajiye akan jakar kayanta kafin ta zauna daga bakin katifar wajen ƙafafun Asiya zuciyarta duk babu daɗi. "Ke kuwa Asiya me yasa zaki yi haka saboda Allah, ko ba kya son Baqeer bai kamata kiyi mishi irin wannan cin fuskar ba babu tausayin halin daya samu kanshi a ciki a haka ya taso don ya ganki yana ganin ko da ya rasa komai a rayuwa kasancewarshi tare dake zai sauƙaƙa mishi abubuwa ashe ke ɗin mayaudariya ce mai saka alkhairi da sharri, me manta girman soyayya da sanin darajar masoyi."

A harzuƙe ta tashi zaune tayi wurgi da wayar can gefe ta hau nuna Habi da yatsa tana cewa "Kinga Habi ki kiyaye ni ki fita daga idona na rufe, akan gurgun kike cewa na manta alkhairi, gurgun? To idan na aureshi bara zai yi ya ciyar dani ko kuwa ni zan turashi a keken guragun mu tafi yawon barar, wallahi nafi karfin auren nakasashe Allah ya tsareni da auren wahala, to me na sama yaci bare ya bawa na ƙasa? Idan ban rabu dashi tun yanzu ba sai yaushe? Ko kin fiso nayi ta bashi false hope ina yaudararshi alhalin ba aurenshi zan yi ba? To ni ba haka nake ba tun farko da nasan gurguncewa zai yi ma bazan fara kula shi ba bare har ki samu bakin faɗa mini baƙar magana, aikin banza kawai bayan ko kece babu yadda za ayi ki yarda ki aureshi shine ni zaki cikani da baƙin munafurci da iyayi  har da wani wai abinda nayi ban kyauta ba, mtsew" Ta ɗauki wayarta ta koma ta kwanta tana cigaba da chatting ɗin da take yi kafin shigowar Habi tayi mata ruining mood ɗin ta.

BAQEERDonde viven las historias. Descúbrelo ahora