BAQEER
NAUMM ASGHAR
DAAYUSHER MUHD
RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA BIYAR
KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?
INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?"
KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI - MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS - MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA - GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO - MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB - MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA - MATSI
MAGANIN NI'IMA - MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU.....Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯08142800199
070685580965
Da ƙyar likitocin nan suka samu suka lallaɓa Baba har ya haƙura da ɗauke Baqeer ya mayar dashi wani asibitin da yake son yi bayan sun yi mishi doguwar nasiha da bayani kan cewa duk inda ma suka je abu ɗaya ne za'a faɗa musu ga kuma ƙarin kashe kuɗi tunda duk waɗannan tests ɗin sai an sake yi kuma mawuyacin abu ne results ɗin su fito ba irin na nan ba. Haka nan dai ya haƙura ba don yana so ba sai don tunanin irin kuɗaɗen da ya kashe tunda Baqeer ɗin ya kwanta a asibiti gashi har ɗan abinda gwamnati ta basu na shirin tafiyar Baqeer ɗin wajen gasar ya tasarma ƙarewa buƙata bata biya ba sai ma nakashewa da yayi, wannan abu yana yi mishi ciwo idan ya tuna yadda ya sadaukar da komai nashi don ganin Baqeer ɗin ya kai matakin da shi ya kasa cimmawa a rayuwa yanzu ga abinda ya faru yana ji yana gani mafarkin shi na neman tsayawa a mafarkin kawai ba tare daya cika burin shi ba.Wannan takaicin yasa shi barin asibitin ba tare daya ƙara bi takan Baqeer ba da har wannan lokacin yake kukan baƙin cikin ƙaddarar data afko mishi don a ganinshi duk laifin Baqeer ɗin ne da baya iya zama a cikin gidansu yayi abinda zai fishe shi sai ya tafi yawon majalisa gashi nan yanzu asarar da ya janyo musu. Yana tafe a hanya yana ƴan mitocin shi kamar yana yi da wani har dai ya ƙarasa gidan, tun daga soro yake ƙwala kiran sunan Fatima hankali a tashe. A gigice ta fito daga ɗakin a tunaninta ko Allah yayi wa Baqeer ɗin rasuwa ne saboda irin wannan mahaukacin kiran da yake ƙwala mata gashi ya hanata zuwa asibitin ta zauna dashi sai dai idan lokacin ziyara yayi taje ta ganshi ta dawo shima kuma ba kullum ba.
Murya a shaƙe tace mishi "gani Mallam, ya wajen Baqeer ɗin? ina fatan dai lafiya?" Jikinta gaba ɗaya ya saki dama kuma tunda Baqeer ya gamu da tsautsayin nan ta ƙara yin sanyi fiye da da duk abinda ake yi a cikin gidan bata iya saka musu baki saboda hankalinta ba a kwance yake ba. Harara ya watsa mata kafin ya bata amsa murya a ɗage "ina fa lafiya bayan duk abinda na kashewa ɗanki duk don na inganta rayuwarshi yaje yayi sanadin da yanzu duk abinda na kashe ya tashi a banza, gashi can likitoci na maganar gurguncewa, kamar ni ace a gidana an samu nakasashe salon maƙiya su samu abun yi mini dariya akai".
Kamar a mafarki taji maganar wai Baqeer ɗinta ya zama gurgu ba zai tashi ba, rigijib ta zube a ƙasa dafe da kirji saboda wani irin tsinkewa da zuciyarta tayi. Tama kasa buɗe baki tayi magana tsabar ruɗewa da tayi sai rawa da bakinta yake yi amma ta kasa cewa komai. Haka ya rufe ido yayi ta zazzaga mata ruwan masifa ba tare da la'akari da yanayin firgicin da take ciki ba, har yayi ya gama ya shige ɗakinshi tana nan zube a ƙofar ɗakinta ta kasa motsawa.Abu ce ta kamata ta shigar da ita ɗaki ta kwantar da ita akan gado, su kansu kishiyoyin nata jikinsu yayi sanyi da jin irin ƙaddarar data afkowa Baqeer ɗin don haka aka rasa me magana a cikinsu haka kowacce ta koma ɗakinta suna juyayin wannan al'amari. Tashi tayi zaune jin da tayi ba zata iya zama ba alhalin tasan Baqeer ɗin nacan a wani hali saboda afkowar ƙaddarar nan a rayuwarshi a daidai wannan lokacin ba ƙaramin al'amari bane da dole yana buƙatar lallashi da tausayawa daga wurin makusantan shi gashi uban nashi da zai tsaya ya lallashe shi ya baro asibitin cikin fushi.