*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR**ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHA HUƊU*
https://www.tiktok.com/@maims_kiddies
"Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta.
https://Wa.me//08101378616Wani irin ihu Kamalu ya saki tare da durowa daga kan gadonshi wanda hakan yasa Baqeer kallin inda yake, cike da mamaki yake yi mishi kallon zararre. Kamalu ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu gefen fuskarshi ya ƙara faɗawa kan gado a fili yace "Dole na nemoki Roshni ɗi ta ai bansan soyayyar lokaci ɗaya tana yiwuwa ba amma gaba ɗaya kin gigitani, nasan marin nan ke kanki yayi miki zafi." Yasa hannu ya finciko pillow ya ƙanƙame yana juyi, kai kawai Baqeer ya girgiza don shi abinda ke gabanshi yafi shirmen nan.
Wayar da Hadiza ta bashi ya ɗauka ya saka number Asiya kawai yana kallo, wani abu ne yaji ya taso mishi hakan yasa ya mayar da wayar ya ajiye tare da runtse idanunshi, Bello yake jira yazo ya faɗa mishi abinda Asiya tayi mishi don har yanzu ƙwaƙwalwarshi ta kasa ɗaukar abinda ke faruwa.*****
Tun daga bakin gate Zainab tana parking ta hango Nabeela, tana tsayawa da mota ta ƙaraso da sauri tace "Zeey ya muka yi dake?"
Maimakon ta tanka mata key ɗin motar kaiwa ta bata tace "Whatever! Ni raina a ɓace yake please."
Da kallo Nabeela ta bita harta shiga ciki bata iya bin bayanta ba, A ƙofar shiga taga Mummy, kusa da ita kawai taje ta rungumeta tace "Mummy ni kam me yasa mutane basu da kirki ne?"
"Ki ajiye batun mutane kin san yau me kika nemi ja mana a gidan nan kuwa? Tunda Dad ɗinki ya dawo yake faɗa, me nace miki akan in zaki fita? Ba nace ki tabbatar kin sanar mini ba?"
"Oh yeah! Na tuna amma inda naje yana da muhimmanci ba wai yawon banza naje ba Mummy kin dai sanni."
Ajiyar zuciya tayi tace "Shi yasa nace ki dinga sanar mini ɗin ai tunda kin san Babanki ba yarda zai yi ba."
Zata yi magana taji an daka mata tsawa "Uban wa ya baki izinin fita ba tare da sanina ba? Sannan tun kafin ki dawo ba na sanar dake ba ke babu fita ke kadai ba? Ko kina tunanin wasa nake yi?"
Idanunta ne suka yi raurau tace "Dad nasan nayi laifi amma......"
"Amma me? Ke wato ba'a isa a faɗa miki magana kiji ba ko? Daga dawowarki ko jira baza kiyi ma mu gama murnar zuwanki ba zaki dawo da halin naki ko?"
Hawayenta ta share don tasan inta tambaya ma ko zata mutu ba barinta zai yi taje ba shi yasa ta sulale ta fita ta ɗauka zata dawo da wuri kafin ya dawo amma babban uzuri ya hanata, cike da faɗa yace "Wuce ciki kuma wallahi kika sake gigin fita ba da izinina ba kin san sauran don shirmen da kika yi a baya a unguwar nan da maganar da kika janyo mini a yanzu bazan sake ɗaukanshi ba.”
Idanunta ne suka ciko da kwalla tayi ɗakinta da gudu kawai ta faɗa kan gado, Mummy ce tabi bayanta tana shiga itama ta shiga ɗakin, kusa da ita ta zauna tasa hannu kawai tana shafa bayanta alamar lallashi, cike da takaicin abinda ya faru ta ɗago tana hawaye tace “Mummy nasan nayi laifi amma aƙalla a tambayi ina naje ko? Sannan asan dalilin daya sa na fita, ban san me yasa Daddy yake yi mini haka ba….”
Hannu tasa a saman bakinta tace “Dalilin kenan, Zeey bakinki ba zai yi shiru ba? In mahaifinki na magana ba zaki yi shiru kice ayi hakuri ba? Kin bari ɗabi’ar turawa ta shiga kanki kin manta da wacce muka baki?”
Kallan Mu8my tayi tana share hawayenta tace “Mummy kema kin san ba haka bane tun kafin na tafi karatu muke samun saɓani da Dad sam baya yi mini uzuri.”
Ajiyar zuciya tayi tace “Taurin kanki ne baya so, in har kika saukar dashi zaku zauna lafiya, sannan bakinki, ki taimaka ki daina faɗar duk abinda ya fito daga cikinshi.”
Kallon Mummy kawai take yi tama kasa magana sai hawaye kawai da take zubarwa, share mata tayi tace “Yanzu in kinaso ku shirya gobe Najib zai zo don sunyi magana da mahaifinshi ki tabbatar kin bashi hakuri kun daidaita, Zee dan Allah kar ki ƙara jawo mana matsala.”
Tana kaiwa nan ta miƙe ta fita ta bar Zeey a zaune kawai tana hawaye.