03

23 2 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na Uku

Ummu POV

Gidin Arc. Lawal kasancewar nan ne dama gidan auran ta ya cika makil ana jana'iza.

Ɓangaren farfajiyar filin gidan da akayi ma rumfa wajan ajiye motoci maza ne layin da Baffah daban tun daga kan Baffah, Arc. Lawal, Papa da kannen Arc. Ibrahim Baffah da sauran ƴan uwa da abokanan arziki.

Daga ciki kuma tun daga farkon karamin gate ɗin flats ɗin Ummu mata ne ƴan uwa da abokan arziki, sun zo ta'aziyya yayin da Mummy tana ɓangaren ta itama tana karɓar gaisuwa. yayin da Nadiya da yaran ta ma suna ɓangaren Ummu, daga cikin ɓangaren ƴaƴan Ummu ne HADIZA da SOFIA zaune Anna na tsakiyar su duk sun kwanta a cinyar Anna suna kuka tana tapping bayan su.

Tausayin yaran ya kama zuciyar Anna yadda suke fuskantar jarabawar rayuwa Allah ne ya haɗasu dasu Hadiza kuma suma Allah ne ya haɗa su jinin su ya kuma basu damar da zasu kula dasu ɗari bisa ɗari.

Tun daga wannan lokacin Hadiza da koma America, Sofia kuma take tsoron jirgi don ko da wasa idan aka ce zataje America sai tace aa ba zata je ba ita bazata hau jirgi ba.

SOFIA  ta dawo daga tunanin da takeyi, ta ce,"Baffah wani lokacin ba zamu gudun ma kaddarar mu ba, kamar yadda Anna take yawan faɗa min cewa "Sometimes we can't escape our destiny" Baffah ina so na koyi shiga cikin ƴan uwa, duk da ana kyamata ta a makaranta amma a duk lokacin da nake tare da ku sai na tsinci kaina cikin farin cikin da ban yi tsammani ba"

Anna ta rungume ta tsam ta ce,"Allah ya kare mana ke Sofia" "Ameen ya Allah Anna"

Daga nan suka sauya wata hirar daban suna ta raha a tsakanin su haɗe da tsaida lokacin tafiyar na su idan Sofia sun samu hutun makaranta sai su tafi Kaduna daga nan kuma sai su tafi United Kingdom.

SCHOOL TIMES
7:10am
As usual 7.00am take gama shiri, tana zaune comfortable saman wheelchair ɗin ta wanda ta matso da shi kusa da dining table, tsakurar chips and egg ɗin take yi saboda dama bata cika cin abinci sosai da safe ba.

Jim kaɗan Anna ta fito da lunchbox ɗin ta tana cewa,"Muje ko""
Tura keken tayi tana yiwa Anna murmushi, har suka isa bakin motar Anna, sai ga Baffah ya fito cikin sauri Anna ta ce,"Meeting ne haka da sassafe Baffah, nayi tsammanin zaka kai time ɗin da zan kai SOFIA na dawo kafin nima na shirya"

"Nooooo plan ɗin jiya kenan kafin muyi bacci, da safen nan na samu kira daga new client ɗina sun zo daga America kuma yau ya kamata na haɗu da su"

"It's okay" Anna ta faɗa tana rungumar shi tsam, ta manna mishi peg a kumatu, sannan ya rungume Sofia yama cewa,"Sofyy me zan siyo miki ƴar Baffah?

"CHOCOLATE" Na faɗa ian kanne masa ido ɗaya, "Alright my good girl study well kinji" ya faɗa yana dafa kanta yayin da ya ɗaura ta cikin motar shima yayi hanyar tasa motar sannan suka bar compound ɗin gidan.

Filin assembly ita ta buɗe taro da addu'a kasancewar tana ɗan gefe kaɗan da layin da mates ɗin ta suke tsaye. basu wani jima ba kowa ya kama hanyar ajinsu,a hankali take tura keken nata ta sunkuyar da kai, bayan ta dawo daga staff room ta kirawo malamin da zai musu darasin farko.

Su uku ne suka sha gaban ta, tun daga kasa ta fara kallon kafafuwan nasu kama daga kayan makarantar nasu har zuwa fuskokin su wacce ko anan ma kasan SOFIA ta ɗarasu kyau,aji, ilimi, dukiya, hutu, natsuwa da komai ma kamar kullum ɗaliban da suke yawan takura mata ba adadi, tunawa da tayi dalilin takurar yasa ta dafe goshin ta tana ɗan murza shi kaɗan saboda yau kam ta kudiri aniyar sai ta ɗauke kowaccen su da mari matukar suka taɓa ta.

SOFIA ✔Where stories live. Discover now