18

5 1 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_18
Washe gari
7:00am
Da wuri na tashi da ɗokin Mai martaba ya ce yau za a dubo min Abhi in da hali ma na san za su taho da shi, yau ina son gwada wani abu wato girki don na jima rabon da nayi girki, ko ni da Abhi ne sai dai dafa ruwan shayi da dama kunu sai ɗumama abinci da jefa ɗan wake....so bayan ƴar aikin sashi na ta shigo tamin gyare gyare da goge goge ta biyo ni kitchen tana ta ya ni wasu ayyukan.

Tsahon awa biyu muka bata mu haɗa wancen mu sauke wannan mu ɗaura wancen haka dai har mun gama, na jera komai saman dinning table ɗin da ke tsakanin falo da kitchen babba mai ɗauke da shura na sanya takalman baki da console babba da mirror ɗin sa, da kuma chest drawer mai kyau an jera casserole da kwalaban khumra wajan ya ƙayatu na sallami badi'a da nata abincin ta tafi sashin bayi.

Da kai na na kira Fulani Mami na ce ta aiko a ɗauka musu abinci, jim kaɗan sai ga jakadiya ita da bayi mata mutum biyu suka ɗau kulolin, ni kuma na tura keke na kunna t.v don ba ni da aikin da ya wuce wannan. kamar kullum, zaman shirun ya fara min yawa sai na fara suggesting karanta littafai na turanci da na hausa.
•••••••
Ɓangaren Fulani Mami suna ta tattaunawa a falon shakatawar Mai martaba wanda ya ke sashin Fulani Mami. Mai martaba ya ce,"Gaskiya ban yi tsammanin Yarinyar nan ta iya girki haka ba"

"Nima dai ban taɓa tunani ba, Allah dai yaba ma Yarima ikon kulawa da ita,Allah yasa matar sa ce har karshen rayuwar sa domin akwai wani abu da nake ji game da yarinyar"

"Allah ko ranki shi daɗe, kin san ki da hangen nesa atimes" Fulani Mami ta yi dariya kaɗan sannan tace ya batun ciwon Yarima ne,na yi magana da asibitin Maitama Hospital amma sun faɗa min Dr.Theresa ce mai duba shi kuma ba ta ƙasar amma akwai wata wacce ta ƙware sosai akan ciwon"

"To babu damuwa wannan karan ma Abujan za ku je, da ina ta tsammanin gwara ku fita ƙasar waje ko za a da ce" Cewar Mai martaba.

Fulani Mami ta ce,"Mu jaraba wannan likitar mu gani Allah yasa a dace" "Amin" zuwa anjima za su tura mana address na hospital ɗin gobe na ke tsammanin flight ɗin mu zai ta shi"

"In Sha Allah zuwa anjima ki faɗa min da wuri sai muyi booking available flight
Sallama ta ce ta janyo hankalin su yayin da Fulani Haɗejia ta riga ni shigowa ta na wani yatsina ta samu waje daga gefen Mai martaba ta zauna ta ce,"Sarki na" kasancewar sunan da take kiran sa da shi kenan, irin Sarkin ta ita kaɗai abin ma dariya ya bani ta yi mishi magana a hankali wanda ko na kusa da su ba lallai ya ji hirar ba daga bisani ya maido da hankalin sa kai na ya ce,"Suruka guda a cikin dubu" ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi sai naji kunya ta kama ni na durkusa har ƙasa na sadda kai na ƙasa na gaishe shi cike da ladabi

"Barka da yamma Abba"
"Barka da yamma Mami"
"Barka da yamma Fulani"

Mami ce ta fara amsawa ta ce,"Barkan ki daughter kin yini lafiya"

"Lafiya lau" na amsa yayin da Abba ya ce ,"Badi'a matso da ita nana mana" Badi'a ta matso da ni ya ce ,"Kina ji na ki ɗau kanki a matsayin ƴa cikin fadar nan, ni ma tamkar mahaifi nake a wajan ki, kuma suma ki ɗauke su a matsayin iyaye, shine zaki zauna da kowa lafiya kin ji Sofia,mai sunan ƴan gayu"

"Na'am na ji Abba, kuma In Sha Allah zaku same ni mai biyayya agare ku"

"Ma Sha Allah , Allah ya yi miki albarka"

"Amin ya rabbi na amsa ina sadda kai na ƙasa", da ga nan na sallame su Badi'a ta mai da ni sashi na.

MAITAMA DISTRICT HOSPITAL
05:00pm
Anna ce ta fito daga cikin motar ta hannun ta rike da disposable labcoat, wuyanta rataye da stethoscope sauri sauri har ta karasa cikin asibitin, ta na duba agogon hanun damam ta wanda yake daɗa tunasar da ita cewa majin yacin na tsananin bukatar ta a wannan kokacin.

SOFIA ✔Where stories live. Discover now