SOFIA
NOBLE WRITERS
EP_23
*BONUS PAGE FOR FREE*
United Kingdom
Tun da suka tafi, ya shiga hali na damuwa saboda yadda Anna tayi kiran su urgent, sai yanzu yake danasanin abin da ya sa bai bi su ba.....Wata zuciyar na tunasar da shi wata kil ko wani abu aka samu ta ɓangaren iyayen su, Ya kai hannu zai kashe system ɗin sai ya ce bari ya sake kira ko zai same su, Bugu ɗaya biyu aka ɗauka Baffah ne ya ɗauka ya na zaune kujerar dake kallon ta Anna, yana mika mata Tuffa lokaci guda hankalin sa na kan ɗan sa ya ce,"Ahmad fatan kuna lafiya?"
"Lafiya lau Baffah" Ahmad ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce,"Ka dawo kenan, kuma da har munyi waya da new clients ɗin mu fa"
"Really, sun canja shawara ne kuma"
"Eh, amma kar ka damu zan tura musu event date, da time ko zuwa cen sai na yi"
"Allah ya kai mu Baffah, Ya su Anna mind ɗina yana wajan na ƙosa na tambaye ka su"
"Gata a kusa dani" Baffah ya faɗa yana karkato da laptop ɗin zuwa fuskar Anna wacce bata jima da farkawa ba ta ce,"Ahmad kana ji na"
"Yeah yeah Anna ina jinki, komai lafiya dai ko, ya na gan ku kuma a asibiti, Baffah kuma"? Ahmad ya faɗa yama kallon Baffah alamar yana bukatar amsa, yana saukowa daga matakalar benen da yake sadaka da bedroom ɗin su, hannun sa rike da laptop, Anna na cewa,"Lafiya lau Ahmad" ta amsa don babu yadda ta iya ne, ta na zaune taga call na shigowa hakan yasa ta amsa don ita ma bata jima da farkawa ba tun da aka mata allurai.....Alhamdulillah taji dama dama, Ahmad ya katse ta yana cewa,"Anna ya kaman kina hospital,miye a hannun ki kamar cannula, Anna tell me what's happening you left me behind" ya faɗa cike da damuwa karara a fuskar shi
"Calm down my son, am okay kaji, am fine as you can see, ina jikoki na, a kira min su mu gaisa"
"Are you sure? Ya tambaya yana zumbura baki ,Ta gyaɗa kai tana nuna masa muscle ɗin ta tana cewa"See am fine"
"Hahhh why are you showing me biceps, by the way women doesn't have biceps at all" Anna ta harare shi ta ce," da kana gefe na ne da na rankwashe ka" Ta faɗa daidai lokacin ta hango yaran sun taho Ahmad na dariya yana cewa"Childrens come come come!!!! "Anna wanna talk to you"
Duk suka rugo a guje har da yaran Sageer da kannen sa, yaran Kamal kuma suna cen wajan shi basu zo nan ba, Anna ta gaisa ta samu surutu wanda ya ɗan mantar da ita kaɗan daga cikin damuwar da ta shiga, daga bisani ta musu sallama sannan ta kashe system ɗin gaba ɗaya don dama ta san ba zata iya faɗa masa Khadija ta samu miscarriage ba, she cannot force her self to say that"
A wannan lokacin Baffah ya koma gida shi da escort ɗin sa don yana so ya tabbatar ko Abhi na lafiya, ya samu Nainah na zaune a ɗakin da aka kwantar da shi, tana karasa gyara ɗakin, ta kunna T.V ta dawo ta zauna, tana cewa,"Baffah kayi hakuri da maganganun da Ya Sageer ya faɗa, Baffah don Allah ku yafe masa, har yanzu ruɗin duniya na ɗiban sa gaskiya"
"Ahhhh babu komai Nainah, ai komai mai wucewa ne, I think zan shiga ciki na watsa ruwa, duk wani abin da kike bukata kiyi ma Chioma magana zata baki"
"Okay In Sha Allah, mun gode Baffah, kun zame mana katangar da ya kare mu daha faɗuwa, Allah ya saka muku da alkhairi"
"Amin ya Allah, ina tunanin za a mai da Abhi ICU saboda a bashi kulawan da ya kamata, zaman gida shikaɗai ba zai yuwu ba"
Nainah ta tsaya tana kallon Baffah, wani irin zuciyar taimako ne Allah ya dasa ma bayin Allah, hakika tun da tazo duniya bata taɓa yin katari da masu jin kan mutane ba kamar Baffah da Anna....Anan Baffah ya wuce ya bar ta zuciyar ta fal da tunani.
8:00am
Da safe ita ta tashi ta haɗa breakfast da Chioma, suka shirya ma Baffah na sa a dining table ɗin sashin, suka haɗa basket biyu Nainah ta tafi da shi hospital, Nainah ta kai ma Khadija ɗaya, sai ta kai ma Anna ta gaishe da jiki sannan ta koma wajan Khadija don ta ɗebe mata kewa.
YOU ARE READING
SOFIA ✔
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...
